MADADI Page 41 to 50

*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
Mddbhrmbn39
A mutukar tsorace Naja’atu ta matsa gefe tana zare idonta tayi masifar tsorata da ganin abinda Halisa takeyi sai wasu surutai take wanda gabad’ayansu basa gane abinda take cewa……To shima Abbah Abbas din a nasa b’angaran ya dan tsorata da abinda Halisan takeyi sai dai da yake namijin gaske ne bai nuna ba tunda dama ba wannan ne karo na farko da halisan ta ta’ba tada iska a gabansa ba.
Baba Larai mai’akinsu ce ta fito daga kicin taga abinda ke faruwa hankali a tashe ta ‘karaso gurin tana tambayar Naja’atu…A tsorace tace”Wallahi nima ban sani ba kawai naga ta fad’i a gurin ne…..
Baba Larai ta kalleshi jikinta a sanyaye tace”Alhaji anya Hajiya ba iskokai takeyi ba wannan birgimar da takeyi bata hankali bace.”
Cikin alhini da damuwa yace.”Abinda ke damunta kenan insha Allahu kuma zanyi maganinsu. Ya kalli Naja’atu da fadin ta dauko masa ruwa…Kasa motsi tayi a gurin, Baba larai ita ta wuce da sauri taje ta dauko masa ruwa karamar roba ta kawo masa.
Ya bude murfin ya tsuguna gaban Halisan ya shiga tofa addua a cikin ruwan kamar yanda yayi a kwanakin baya ya shiga yayyafa mata ruwan adduar a jikinta…..Sai da duk ya Jike mata fuskarta da ruwan adduar sannan abinda takeyi ya lafa…Ya ajiye robar ruwan ya cigaba da tofa mata adduoi a fuskarta…..Kamar anyi ruwa an dauke Halisa ta daina burgimar da takeyi jikinta ya shika bacci mai nauyi ya dauketa..Mikewa yayi cikin yanayi na damuwa ya kallesu da fad’in “Kada wanda ya tashe zata tashi da kanta.” Baba larai tace” Insha Allah babu wanda zai tunkari inda take Allah ya bata lafiya.
Ya amsa da ameen tare da kallon Naja’atu a nutse yace” Kiyi hakuri da abinda tayi miki bata cikin hayyancinta….Naja’atu tsabar tsoro yasa ta manta da ciwon da Halisa taji mata a gefan fuskarta, tasa hannu a gurin tana ta’bawa kawai sai taji danshi tana dubawa taga jini a hannunta amma ba sosai ba. Hawaye ne suka zubo mata yanzu da badan yana gidan ba Halisa zata iya yi mata mummunan rauni kuma karshe babu wani mataki da zai dauka sai dai ace tayi hakuri…..Yace.”Ki sanjo hijab tunda wannan ya ‘baci da jini sai muje asibiti a duba miki gurin, a sanyaye taje ta sake hijabi ta fito, Tarar dashi da Baba larai suna maganar Halisa inda yake cewa zai kira malaman rukiya suyi mata dan ya fahimci iskokin dake damunta masu cutarwa ne, Baba larai tace”To Allah yasa ayi cikin nasara.” Naja’atu ta d’aya gefan ta wuce tana waiwayen inda Halisan ke kwance gabadaya yanzu masifar tsoranta take ji……..To Da yake tayi saurin kaucewa yasa Halisa bata samu nasarar illata mata fuskarta ba d’an gurin daya tsage aka wanke sannan aka bata magunguna masu kyau wanda zasu taimaka gurin dusashewar ciwon……Bakin gate ya ajiye ta yace ta shiga gida zai wuce kasuwa, kuka tasa wai ita ba zata shiga gidan ba tsoron Halisa takeji sai dai ta shiga gidan aunty Maryam idan ya dawo da yamma ta dawo gidan.A take ya nuna mata rashin amincewarsa yace lallai sai ta shiga gidan Halisa bata isa tayi mata wani abun cutarwa ba, Tasa gaddama hade da fad’in “Gashinan ta tsaga mata fuska da makami ai idan ta farfado ta ganta a gidan zata sake d’aukar makami a kanta! Suka dinga tababa ita dashi a motar Abbah bai ta’ba tsammanin yarinyar nada taurin kai irin hakaba, ita kuwa Naja’atu da biyu take masa haka dan kawai ta d’aga masa hankali ne ya za’bi zama da Halisa ita ya rabu da ita
Ganin tana ‘bata masa lokaci ne yasa yace”Ta fitar masa a mota tunda ita bata jin magana, aikuwa ta bude motar ta fita tana kuka kamar wacce aka aikowa da mutuwar iyayenta, yasa mata ido kawai yana kallon inda ta nufa, sai yaga ta dauki hanya tana tafiya tama wuce gidan aunty Maryam din da alama kofar na’isa zata nufa…Da sauri ya tari gabanta da mota taja ta tsaya tana kallonsa da idanunta da sukayi jawur! duk tana sane take wannan kukan iskancin…Gilashin motar ya sauke babu fara’a a tare dashi yace.” Ki shiga gidan aunty Maryam din amma kada ki sake kije kofar na’isa ki fada musu wata magana akan al’amarin nan daya faru.
Ba tare da tace masa komai ba ta juya da niyyar zuwa gidan anty maryam, bai ja motar ba sai da ya tabbatar da cewar ta shiga cikin gidan sannan yaja motar…Yana dab da fita daga layin Salim ya shigo da mota da niyar daukarsa bayan ya ajiye yara a skull Ganin kamar Kawun nasa na cikin damuwa yasa baiyi magana ba yayi saurin bin bayan motarsa data fice daga layin gidan.
Aunty Maryam na ganin Naja’atu wujiga wujiga ga gefan fuskarta manne da plasta sai gabanta ya fadi tana rawar baki take tambayarta abinda ya sameta.
Cike da neman fitina gami da ‘kara rura wutar al’amarin da ya faru tace”Halisa ce haka kawai ta dauki kwalabar turare tace sai ta burma mata ta kashe to da bata samu damar caka mata ba sai ta yanke ta a fuskarta, tana kuka ta cigaba da cewa kuma Abbah Abbas din bai dauki mataki ba karshe ma cewa yayi wai tayi hakuri Halisan bata cikin hayyacinta.
Anty Maryam ranta ya ‘baci mutuka tace”To a gaskiya wannan al’amarin ba zai yuwu ba tunda har Halisa takai ga matakin daukar makami a kanki to kuwa dole a dauki mataki a kan al’amarin! dan dama Abbah Abbas din ya saba goyawa Halisa baya ko lokacin da Halimatu take raye sau nawa Halisa za tayi mata abu baya daukar mataki sai dai kawai ya bata hakuri, dan kawai ya samu mace mai hakuri suka hadu suka dinga cutar da ita bakin cikinsu ya kasheta to gaskiya a wannan karon dole manya su shigo cikin maganar.
Naja’atu tace”Shiyasa tun farko nake fada muku cewar wannan al’amarin da kuka k’ulla akwai cutarwa a cikinsa ina zan iya zama da Halisa muguwar macace babu irin sharrin da ba tayi min a gidan kuma ya goyi da bayanta gashi yanzu ta kai har ta dauki abu zata kasheni wallahi idan baku raba auran nan ba to zan gudu na bar muku garin kowa ya huta.” Cikin kuka na fitar hankali ta kare maganar
Anty maryam jin maganar guduwa yasa hankalinta ya tashi tace”Daina kuka nima ban goyi da bayan ki cigaba da zama a gidan ba, bayan gagarimar matsalar da kike fuskanta ta rashin biyan bukata kuma a dinga barazana da rayuwarki, gwara tun kafin tafiya tayi nisa a san yanda za’ayi.
Dakinta ta shiga ta dauko wayarta ta dawo ta zauna kusa da Naja’atun.
Numbar mijinta ta shiga kira, wanda a lokacin ma suna tare da Abbah Abbas din a kasuwa suna sake tattauna maganar jiya da naja’atu taje ta fadawa maryam din ta rashin gamsuwa…Abbah Magaji ya daga wayar da sallama a bakinsa, to da yake handsfree yasa babu abinda Abbah Abbas din baya ji….Anty maryam muryarta na rawa tace”Abban Ilham abubuwa fa suna nema su lalace! ga Naja’atu nan muna tare da ita ta shigo min hankalinta a tashe tana kuka ga wani irin rauni a fuskarta wai Halisa ce ta dauki makami zata caka mata da bata samu damar caka mata ba sai ta yanke ta a fuskarta wallahi baka ga abun ba babu kyawun gani, a gaskiya yarinyar nan na cikin tashin hankali mai girma, Aure kwana takwas duk ta lalace kullum babu nutsuwa a tare da ita ga wannan babbar matsalar da na fad’a maka jiya a gaskiya yana da kyau ku zauna gabadayanku ku duba al’amarin nan kada garin son zuciyarku ku cutar da yarinyar nan Dan gaskiya xaman gidan Abokinka sai wanda ya shirya Halisa ba a zaune take ba.” Aunty maryam ta karashe maganar ta tana sauke numfashi.