MADADI 1-END

MADADI Page 41 to 50

Halisa ko kallonta ba tayi ba ta cigaba da kallon dramar da akeyi a tashar mbc1 din.

Naja’atu ta mi’ka hannu zata dauki romot din ta wani fizge hannunta ta dauke romat din ta rike a hannunta.

Naja’atu tace”To ikon Allah! kina Iko da abinda ba naki ba? Kayan kallon nan fa ba daga gidanku kika zo dashi ba maigidan ne ya siya ya ajiye domun ‘ya’yansa kawai kuma sai ki dinga ‘kuntatawa yara kina son zuciyarki.” Halisa ba tare data kalleta ba tace”Ki cigaba da zagina kina min rashin kunya zaki gane baki da wayo wallahi.”

Naja’atu tace”Babu wani zan gane bani da wayo ai gaskiya na fada miki dama ni tuntuni abinda yake had’ani dake son kai aikin banza kawai.” A fusace! Halisa ta juyo ta wanke mata fuskarta da mari ta mike tsaye tana wani irin huci! tace”Ke na gaji da rashin mutuncin da kike miki wai dan uwarki ni sa’arki ce.”! Naja’atu ta dafe fuskarta tana kallonta ta’b!!! Mikewa tsaye tayi a zafafe! kawai suka ji sallamarsa a palon…Naja’atu ta fashe da kuka tana sake rike fuskarta ta da fadin “Kawai daga na fad’a miki gaskiya shine zaki mareni har da zagin uwata.”

Ya k’araso gurin yana tambayar abinda ke faruwa, Halisa dai jikinta ne yayi sanyi dan ta kasa magana data san zai dawo da wuri to da bata aikata abinda ta aikata ba shi kuwa ya dawo da wuri ne domin kawai yaga shin naja’atu ta dawo gidan ko kuma tana waje.

Tana kuka ta kama hanya zata bar gurin. Hannunta ya rike ya dawo da ita yana tambayarta abunda ke faruwa…Tana kuka tace”Kawai daga na aiki Mufida nace ta kira Mai musu wanki yazo ya dauka shine tace yarinyar ba zataje ba wai naje da kaina ko kuma na aiki wanda nake da iko dashi, sai kawai Saddiqa ta tafi ta kirawo shi yazo ya dauki wankin, to kuma yanzu yara suna kallon film dinsu kawai daga zuwanta tazo ta sanja musu tasha shine dan nace ta mayar musu su karasa gani sai kawai ta hau d’ura min ashar harda zagina.” Cikin gawurtaccen kuka ta ‘karashe maganar…..Halisa jikinta yayi sanyi lallai yarinyar nan ta gawurta gurin iya sharri yanzu dame zata kare kanta ji tayi giwarta tayi sanyi…..Babu walwala a fuskarsa ya kalli Halisa da fad’in “Wai me yasa kema da girmanki kike mayar da kanki yarinya? Akwai Tv a dakinki me zai sanya ba zakije can kiyi kallonki ba sai kinzo ki takurawa yara kuma idan nayi magana kice ina fifita yara a kanki ke abinda kikeyi ya dace kenan.”?

A sanyaye tace” To ni dai bani da abinda zance anan gurin shuru shi yafi min alkairi amma duk abinda yarinyar nan ta fada maka to karya take yi Tunda ta dawo daga yawonta take zagina dama kuma na fada maka tun kafin ta fita ta fara to ina tunanin inda taje an zugata! shiyasa ta shigo da neman fitina kuma ni ban zauna dan na takurawa yaranka ba kayi hakuri.”

Tana kare maganarta ta bar gurin, tana mamakin yanda al’amarin ya juye kanta tana so ya dawo gidan taga irin cin mutuncin da zaiyi wa yarinyar sai gashi al’amarin na nema ya dawo kanta aikuwa dole ta lalla’ba kada ya kunyata a gaban yara shiyasa tayi gaggawar barin gurun.

Halisa na barin gurin Ya shiga bin jikin Naja’atu da kallo drassing din da tayi yayi masa kyau! komai na jikinta ya futo kuma yau bata sanye da hijabi! Ganin yana kallonta ga yara a zazzaune sai tayi saurin zama kan kujera tana dauke kanta…Shima da sauri ya bar gurin gudun kada yaran su fahimci wani abun.

Mufida ce ta dauki romot din tayi saurin mayar musu da Mbc2 tashar da suke kallo, suka cigaba da kallon film dinsu.

 Halisa da kyar ta iya binsa dakinsa ta taimaka masa yayi wanka ya shirya jikinsa suka zauna suna mayar da maganar abinda ya faru ita dole sai ta wanke kanta ta d’ora laifin abinda ya faru a kan Naja’atu shi kuma ya kasa fahimtar ta shifa ba zai fahimci komai ba mutukar magana ta kasance a kan yaransa to yakan iya daukar mataki mai tsauri a kan koma waye (Lallai Abbah Abbas kana da son ‘ya’ya da yawa) Halisa da taga ya kasa fahintarta sai ta kawai ta bar maganar ta shiga fada masa zuwan mai’aikin da hajiya ta turo…Yace.”To alhmdullhi naji dadin zuwanta kowa sai ya huta dama dake da Naja’atun dukkaninku kuna ganin kyashin kulawa da yaran wannan kuwa kudi zan biya ta nasan zata kula min dasu.

Halisa ta rike bakinta tana kallonsa da mamaki a tare da ita tace”To me kuma yayi zafi da fadin wannan maganar.” ? Yace.”Duk maganar dana fada a kanku ai ba karya nayi ba, ke ‘yar da kika haifa ma baki nuna kulawarki a kanta to akan wa zaki nuna.” Halisa ganin yana nema ya mayar da abin rigima sai ta shiga bashi hakuri wai ya bar maganar kada tayi tsayi ita dai tasan tana iyakacin bakin kokarinta a kan yaran, kuma tasan Allah yasan zuciyarta…..Jinta kawai yake saboda halinta sai da ya fadawa wani 

Idanunta ne ya sauka kan ledojin kayan lefen Naja’atu da suke ajiye a gefe guda, tace”Wai wannan yarinyar ba zata dauki kayanta ta kai d’inki ba.”

Yace.”Tace bata so ki kwashe ki bawa wanda ya dace! kafin mu tafi umara zamuje da ita ta duba duk abinda take so..Halisa zugum! tayi tana kallonsa cike da mamaki tace”Yanzu meye laifin kayan nan da zate ce bata so kai kuma zaka biye mata wallahi ka dinga amfani da kudinka a inda suka dace.” Cike da kishi ta fadi maganar

Yace.”Duk da ban san kayan mata ba na duba naga kayan na gane basu da kyau da quality saboda haka tunda tace ba suyi mata dole a sanja mata wasu tunda hakkinta wannan kuma ni nace ki bayawa mabukata ko a cikin danginki ne.”

Halisa sai taji maganar tasa kamar da akwai cin fuska a cikinta Ikon Allah! Lallai yau ya shigo gidan da son yaci zarafinta dan haka sawunta a likkafa ta fita tabar masa dakin.

*( To dama waye ya fad’a miki kullum ake kwana a gado Halin namiji ai yafi dubu yau zuma gobe mad’aci! haka suke Komai asirinki idan wani namijin ya burkice miki sai kin rasa yanda za kiyi gwara ma ki daina asirin shi zai fi miki alkairi*)

Daure da alwala ya fito ya samesu a zaune a palon Naja’atu ta sake sai dariya take ita da yaran ya kallesu yana jin dadi a ransa a duniya yana so ya gansu suna walwala yace.”Ku tashi kuje kuyi sallah! Da sauri suka kashe tv din shi kuma ya kama hanya ya fita da niyyar shiga massalaci

Sai da ya sallaci isha’i ya shigo, kai tsaye gurin cin abincin ya nufa, Naja’atu da yaran suka bi bayansa, sukayi zaune suna jiran Halisa tana daki ta’ki fitowa sai haushi take ji…Ya kalli Mufida da fadin taje ta kira ta.

Yarinyar ta fito ta zauna tana kallonsa tace”Wai gata nan zuwa.” Suka cigaba da zaman jiran fitowarta bata fito ba, Ya kalli Naja’atu da fad’in “Zubawa kowa abincinsa.” Ta kuwa mike da sauri ta shiga had’awa kowa nasa, dadi take ji itama yau ta samu galaba kan Halisa…….Tun kafin ya fara cin towon ya bashi sha’awa kuma gabadaya girkin baiyi kama dana Halisa ba yace”Da alama wannan abincin na bakuwar da mukayi ne.” ? Tace”Eh nima bayan na dawo daga gidan aunty maryam na tarar da matar tace sunanta Larai daga gidan Hajiya.” Ba tare da yace komai ba yayi bisimillah a nutse ya fara cin abincin gaskiya yaji dadin abincin matar sosai ashe Halisa ba ta iya komai ba hakuri kawai yake amma yanzu tunda ya samu mai aiki dattijuwa wacce ta iya girke-girken zamani dana gargajiya to yasan matsalarsa ta kare….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button