MADADI 1-END

MADADI Page 41 to 50

Sosa kanta tayi cikin wayancewa tace”To ai gani nayi auran naku ko wata d’aya ba’ayi ba ya za’ayi ace har kayiwa yarinyar ciki? anya kuwa ba ‘karya bane ? idan ma da gaske ne to wallahi mybe dashi tazo.” Wani irin mari! ya kifa mata cikin fusata! yace.”Ashe baki da hankali Halisa jinina kike ‘kokarin shegantawa! Wannan wane irin rashin mutuncin ne.”? Halisa tuni ta shiga hankalinta ta dawo hayyacinta ashe zancan zuccin da takeyi a fili ta fad’e shi..Hakuri ta shiga bashi da fadin” Wallahi bata san ta fadi maganar ba kuma dai abin ne ya bata mamaki shiyasa take kwokwanto.”

Tsaki yaja mai karfin gaske ya mike daga kusa da ita tare da fad’in “Shashasha mara hankali kawai.” Kallo tabi shi dashi lokacin da yake kokarin shiga dakin da hajiyarsa take ciki…Halisa zukud’um! tayi ta ‘kurawa guri guda ido gabad’aya kanta ya kulle ta marasa wane irin tunani za tayi…Naja’atu nada ciki shin yaya akayi haka ta faru? me yasa naja’atu tayi ciki da sauri haka? Ita da Halimatu sai da sukayi shekaru masu tsayi a gidan basu dauki ciki ba me yasa ita Naja’atu ko wata daya ba tayi ba ta dauki ciki? shin wai ina Aljana *’Yar Zabira* take da har ta bari wannan al’amarin ya faru???? Wasu zafafan hawaye ne suka shigo gangarowa daga idanunta.

Hajiya Abu tayi farin cikin samun labarin cikin da ‘Yar dakinta Naja’atu take dauke dashi, kafin ta bar abun sallarta sai da ta daga hannunta sama ta roki Allah ya sauketa lafiya.

Aunty maryam tsabar haushin abinda naja’atu takeyi yasa ta fita daga sabgarta ta cigaba da shige da ficenta tsakanin kicin da dakinta, haushin hakan yasa ta mike tare da daukar ledojin magunanta ko sallama ba tayi mata ba ta bar gidan…Aunty maryam ta fito daga kicin bata ganta ba sai kawai ta girgiza kanta, tana nema mata sauki gurin Allah hakika tana jiyewa yarinyar ranar da zata zo tana nadamar abinda ta aikata.

Baba larai ta ganta ta shigo fuskarta a daure ido jajawur! hankali a tashe tace”Naja’atu lafiya ina Hajiya maryam din tun dazu ina nan a zaune ina jiran dawowarku….Zama tayi kan kujera tana goge hawayen daya tawo mata tace”Aunty maryam tana gidanta.” Baba larai jikinta a sanyaye tace”To Allah yasa dai lafiya? Fashewa tayi da kuka tace”Wai ciki ne dani.”? Baba larai tace”Alhamdullhi to shine kuma abin kuka da tashin hankali.” Naja’atu sakin bakinta tayi tana kallon matar…Baba larai ta cigaba da cewa ai abin farin ciki ne ya sameki da duk wani masoyinki menene abin tashin hankali addua zakiyi Allah ya rabaku lafiya.”

Girgixa kanta ta shiga yi hawaye wani na bin wani tace”Baba har abada ba zaku gane abinda nake ji a cikin zuciyata ba, amma babu komai duk abinda ya faru da rayuwata kune sila.” Baba larai tayi shuru tana kallonta dan ita bata fahimci inda maganarta ta dosa ba…Mi’kewa tayi ta dauki ledar magungunanta da wayarta ta nufi daki…Larai ta bita da kallo cike daso ta fahimci menene yake a ‘kasa wanda ita bata san dashi ba

Ruwa ta dauko ta zauna gefan bed tana kuka tana had’iyar maganin kamar yanda Dr ta umarci tayi, kwanciya tayi bayan tasha maganin ta tsirawa rufin dakin ido, wallahi sai ta zubar da cikin nan….Da sauri ta mike zaune ta dauki wayarta tana kokarin neman numbar Munira….Kiran wayarsa ya shigo, da sauri ta datse kiran nasa tana jan tsaki ta cigaba da laluben numbar munira..Allah sarki Abbah Abbas sake kiran wayar yayi! da sauri ta sake datsewa! sai kawai ya shiga bin wayar tasa da kallo, a duniya ya tsani ya kira waya a kashe masa, zuciyarsa ya bawa hakuri ya sake kiran wayar a karo na uku…Sai suka ce masa busy alamar ana amfani da wayar….Ajiyar zuciya yayi ya ajiye wayar a kusa dashi yana tunanin da wanda take waya

“Lallai Naja’atu ciki fa kikace kina dashi har yaushe akayi auran da har zaki samu ciki kuma ma garin yaya kika bari haka ta faru.”? Munira ce take fadin wannan maganar.

Cikin dusashshiyar murya tace” Munira ni dai dan Allah duk mubar maganar yanda akayi hakan ta faru ni yanzu burina naga babu cikin nan a jikina shine zan samu kwanciyar hankalin da nake bukata, Wallahi Munira ban shirya haihuwa yanxu ba ke ko na Shirya haihuwa to ba da wannan tsohon ba.

Munira tace”wallahi kina da gaskiya kawata ai yanzu an daina wannan ace kana zuwa ka wani haihu baka mori kuruciyarka ba yara suzo su dameka duk ka zama tsoho shiyasa nida Muktar muka tsara rayuwarmu kafin auramu ba zamu haihu da wuri ba sai munyi kamar shekara biyar ko sama da haka lokacin mun mori kanmu.

Naja’atu tace”Wallahi Munira banga laifinki ba….Nima bani da ra’ayin haihuwa da yawa a duniya sabida gudun wulakancin namiji….wannan cikin da ace ina son ubansa zan iya bari na haife shi to gabadaya na tsani wanda yayi sanadiyarsa shiyasa kawai na yanke shawarar zuwa garinku inaso ki bani cikakken address insha Allahu gobe ko jibi zaki ganni a gidanku idan yaso idan nazo sai muyi sha’awar yanda za’ayi kinga cikin ma baiyi wani kwari ba ba zamu sha wahala ba…Munira tace”Eh gaskiya kinyi dubara kada ki damu zan baki cikakken addrees din gidanmu idan kinzo zamuje Chamis akwai tablet din da zasu baki ki sha d’aya kisa d’aya a ‘kasan harshenki sannan kisa d’aya a gabanki! insha Allah cikin sai yabi rariya.”

Ajiyar zuciya ta sauke tace”Nagode sosai k’awata! ina jiran address din ta whasap.” Munira tace”To ki kunna data zan turo miki.” Da sauri tace to tare da kashe wayar……Abbah Abbas kuwa al’amarin ne ya daure masa kai sosai dan ya sake kiran wayar ya kai sau hudu sai suce masa line is busy mamaki yake to wace irin waya yarinyar take mai tsayi haka kuma da waye take wayar.? da yaga bashi da mai bashi amsa sai ya dauki wayar ya sake neman line! sanyi yaji a zuciyarsa jin wayar tana shiga sai dai har ta katse bata dauka ba! Takaici kamar ya kasheshi shin wai me yarinyar nan take nufi! mikewa yayi ya fita daga dakin Harabar gidan ya fita ya zauna kan wasu kujeru kasa hakuri yayi ya sake kiran wayar a karo mara adadi! Naja’atu ta bawa banza ajiyarsa dan kin dauka tayi ta kyale wayar nata ringing! wannan al’amarin yayi masifar dugunzuma masa zuciya sai yaji gabadaya zaman garin ya isheshi hankalinsa yayi gida wannan iskancin da yarinyar takeyi ba na lafiya bane! ya kira waya sama da sau goma saboda tsabar raini da wulakanci ta’ki dauka…Halisa ita kanta sai da ta fahimci baya cikin hayyacinsa to da yake itama ba’a cikin hayyacinta take ba sai aka rasa wanda zai rarrashi wani a tsakaninsu.

Washe gari da sassafe Aunty maryam tazo ta dubata, Naja’at gaisuwar arziki ba tayi mata ba, aunty maryam cikin zuciyarta take fad’in “Albasa ba tayi halin ruwa ba..Aunt maryam na tafiya da kamar mintina ashirin saiga Alhaji Sama’ila da Hajiya Rabi Abbah Alhassan ya kawo su su dubata….Daurewa tayi ta fito ta zauna tana sinne kanta kamar mutuniyar arziki suka gaisa da juna! suna tambayar yanayin jinta tace musu da sauki! Ta lura kowa da kowa na farin ciki da samuwar cikin jikinta ita kadai ce take cikin bakin ciki saboda son zuciya kowa ya kasa gane halin da take ciki……….Bayan tafiyarsu Alhaji Aunty Rakiya ce tazo matar Abbah Alhassan kenan itama wai tazo dubata! Naja’atu cikin zuciyarta tace duk zaku gama gulmarku ku daina…….. Tashi tayi ta bar musu palon aunty Rakiya ta zauna tare da Larai suna hira gefe guda kuma tana mamakin wulakacin da yarinyar tayi mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button