MADADI Page 41 to 50

Abbah Magaji ya dinga kallon abokin nasa ya rasa ma abunda zai cewa da matarsa dan duk ta daureshi da jijiyoyin jikinsa…Tace”Abban Ilham kana jina kuwa.” Yace.”Duk naji abinda kika fada idan na dawo gida zamuyi maganar insha Allahu kuma kada ki bari yarinyar taje ko ina sai na dawo.”
Tace”To insha Allahu dama babu inda zan bari taje.
Kashe wayarsa yayi ya cigaba da kallon abokin nasa dan yasan yaji komai kawai yana bukatar karin bayani daga bakinsa
Abbah Abbas ya cire hular dake saman kansa yasa hankici ya goge zufar goshinsa ya kalli abokin nasa cikin wani irin yanayi na tsantsar damuwa da tashin hankali yace.”Duk abunda Naja’atu taje ta fa’dawa Maryam hakane! Yau da safe kafin na fito al’amarin ya kasance tabbas Halisa ta dauki kwalbar turare da niyyar ta illatar dani kamar yanda tafad’a da bata samu nasara a kaina ba sai ta huce kan Naja’atu akan wani dalili nata na daban, amma Halisa bata dauki kwalbar turare da niyyar ta cakawa Naja’atu ta kasheta ba kamar yanda naji Maryam na fad’a maka yanzu..Sannan kuma inaso kasan da cewar abinda Halisan tayi bawai tayi shi bane a cikin hayyacinta ba ina kyautata zaton Halisa na tare da mugwayen aljanu wanda suke tunzura mata zuciyarta ta dinga kokarin aikata mummunan abu a kwanakin baya idan baka mance ba na fad’a maka cewar a ranar da Halisa ta samu labarin aurena da Naja’atu kwanana ne kawai a gaba dan wuka ta dauko zata kashe ni da ita da gaske caka min za tayi daba don nayi gaggawar murdeta na kwace wukar ba to da zata iya illatani kuma a ranar na tabbatar da cewar tana da aljanu dan a gurin suka bugeta.”
Abbah Magaji ya jima kansa a kasa yana ta nazarin maganganun abokin nasa, to a gaskiya idan hakane zaman Halisa da Naja’atu a guri daya bai taso ba dole daya ta matsa ta bawa daya guri ma’ana ya zamana ko wacce na gidanta tare da sharadin ‘kin ziyartar juna domin a samu daidaito da zaman lafiya, dan mutukar d’aya na zuwa gidan d’aya to kuwa matsala zata cigaba da afkuwa….Abbah Magaji ya dago kansa a nutse yana kallon abokin nasa ya shiga fad’a masa shawarar da ya yanke a zuciyarsa wacce yake ganin kamar itace mafita a garesu
Abbah Abbas yace.”Tun farko haka naso ya kasance to a tsakaninsu Halisan da Naja’atu babu wacce na isa nace ga yanda za’ayi tace to! Halisa ganin ido Naja’atu taurin kai! amma tunda al’amarin nan ya kasance da haka insha Allahu bayan munje umara mun dawo zan dauke Naja’atu daga gidan gabad’aya zan sanja mata gida idan ma bata so ta zauna a tsohon gidana dake d’anbare zan dai samar mata gurin zama wanda ya dace! Sannan ina k’ara baku hakuri a bisa abinda ya faru a yau insha Allah zan nemi malamai domin su zauna kan Halisa a sama mata lafiyarta.”
Abbah Magaji ganin yanda hankalin abokin nashi ya tashi yasa ya sassauta zuciyarsa yace.”Haba Alhaji Abbas meye abin bada hakuri ai ba wata matsala bace wannan insha Allahu Allah zai daidaita maka zamantakewar gidanka da iyalinka sannan kuma naji dadin kar’bar shawarata da kayi ina rokon Allah ya kawo zaman lafiya da daidato a tsakanin iyalinka.” Abbah Abbas ya mika masa hannu da fad’in Ameen ya Allah nagode sosai abokina.”
To ‘bangaran Halisa kuwa sai kusan uku da rabi na rana ta farka da jan gindi ta shiga dakinta ta zabga tagumi tana kallon guri guda, tunda taji kanta yayi mata nauyi da kuma kasala da ciwon jiki yasa ta gane cewar aljanunta ne suka tashi, hawaye ta dinga sharewa tana jin wani irin daci a bakinta, shin wai ita a haka zata kare rayuwarta ne a duniya bukatarta ba zata biya bane.? Sai da taci kukanta ta koshi sannan ta lalla’ba ta shiga wanka ta fito da wata iriyar masifaffiyar yunwa da kyar ta shirya jikinta ta zauna a zaune a kan dadduma tayi sallah saboda tsabar rashin tsoron Allah haka ta hada sallahr azuhur da la’asar a zaune ba tare da tayi addua ba ta cire hijabin ta fita palo
Larai tana zaune ita kadai tana kallon tv tana so hudu da rabi tayi ta shiga kicin…Tana ganin Halisa ta fito tace”Hajiya sannu da jiki kin fito kenan.”
Da kyar ta amsa tana kokarin zama kan kujera tace”Ki kawo min abinci yunwa nakeji.” Larai ta mike da sauri ta nufi kicin domin kawo mata abincin.
Larai na ajiye mata abincin tace.”Ina Naja’atu take.”? Larai tace”Eh to tun dai da suka fita da maigidan bata dawo gidan ba.” Halisa tayi shuru tana tsakurar abincin mamaki take sosai akan ya akayi yarinyar ta iya samun galaba a kanta har ta iya janye hankalin mijinta ya rufe kofa da ita a cikin kwananta a gaskiya al’amarin yayi masifar girgizata wai yau ita yarinyar k’ankanuwa tayi wa satar kwana humm!! Da kyar take cusa abincin tana tunanin irin mugun abun da za tayi wa yarinyar ta huce bakin cikinta.
*Halisa in banda abinki meye abin damuwa bayan kinsan ko ya kulle kofa da yarinyar ba iya tsinana komai zaiyi ba to meye abin d’aga hankali kuma*
Naja’atu na can tare da aunty maryam tana ta fad’a mata karya da gaskiya aunty maryam kuwa ta hau kai ta zauna dan saboda ta riga tasan halin halisa babu irin abinda ba zata iya aikatawa ba shiyasa taji gabadaya ba tayiwa yarinyar sha’awar zaman aure a gidan domin Halisa duk macen da zata zauna da ita sai ta shirya.
Sai bayan magariba suka dawo gidan shida Abbah Magaji sukayi sallama kowa ya nufi gidanshi, yayi mamaki da baiga Naja’atu a gidan ba…Tabbas yarinyar naso ta d’ora masa ciwo mai tsanani duk da cewar yana da tabbacin tana gidan abokinsa hakan bai masa dadi ba saboda shi a rayuwarsa ya tsani ya dawo gida ya tarar da babu daya daga cikin iyalinsa….Halisa ta daure ta kula dashi gurin cin abinci ya tambaye jikinta a sanyaye tace da sauki Yace.”Kin san abinda yake damunki kuwa.” Kamar wata shashasha tace”Ban sani ba wallahi.” Yace.”Kina tare da ba’ka’ken aljanu wanda ni tunda nake tsayin shekarun da nayi dake ban ta’ba sanin kina dasu ba sai da kikaji labarin aurena da yarinyar nan sannan kika fara tayar dasu shin kodai ke kika janyowa kanki su dan saboda ni nasan lafiya lau na aureki baki da wata matsala.”
Murya na rawa tace”Kawai sai na janyowa kaina aljanu a ina zan gansu na janyosu dan Allah ka daina wannan maganar kada ka ‘bata min rai. Shin kai baka tunanin iyayen matar taka zasu iya had’ani dasu ai wannan tsohon mai zama akan buzu kullum babu abinda ba zai iya ba, kullum yana nunawa duniya shi na Allah ne nan kuwa zuciyarsa tafi ta fir’auna.”
Abbah Abbas ‘bata rai yayi yace.”Bana son rashin kunya da zargi Baba malam bazai cutar dake ba malami ne shi ba boka ba kuma yana d’aya daga cikin malaman da zan kawo domin suzo suyi miki ru’kiya.”
Jin maganar ru’kiya yasa ta fashe da kuka tace”Ashe har an kai wannan matakin da zaka dauko malamai su rufu a kaina suyi min ru’kiya ni kuwa wace iriyar iska ce dani da za kayi min haka.”
Cike da mamaki yake kallonta yace”Okey wannan yana nuna min cewar kinfi so a rabu dake kiyi abinda kike so ko kuma suyi abinda suke so a kaina da iyalina kina dauko wuka da makami domin cutar dani da wanda ya shafe ni to idan kina sane kikeyi zanyi maganinki idan kuma su aljanun ne suke saki ki fad’a musu nafi karfinsu.” Halisa ta dinga kuka tana fad’in “A ina zan gansu na fad’a musu sa’konka dan Allah ka bar maganar rukiyar nan.” Yace.”Baki da gaskiya tunda kike maganar a bar maganar rukiya hakan na nufin abubuwa da dama ana so a rabaki da wahala kina cewa a bari to bazan bari ba sai anyi idan kece kika siye su da kudinki zasu fad’a kowa yaji