MADADI Page 41 to 50

Halisa gabanta ya dinga dukan uku uku shikkenan asirinta ya kusa tonowa Allah yasa aljanunta su rufa mata asiri kada su tona mata asiri a idon duniya, adduar da takeyi kenan a cikin zuciyarta tana kuka.
Naja’atu kuwa tana can suna fafatawa da Abbah Magaji dan cewa tayi ba zata dawo gidan ba, Abbah magaji tun yana mata masifa har ya dawo rarrashi dan sabida yasan halinta da taurin kan tsiya da kyar ta hakura zata koma gidan, Abbah magaji yasa Aunty maryam ta rakota.
Halisa da kyar ta iya amsawa aunty maryam gaisuwarta dama sun saba ‘yar d’auke d’auken kai a tsakaninsu, aunty maryam kasa had’a ido tayi da Abbah Abbas duk kuwa da cewar suna dan wasa a tsakaninsu, abinda yasa ta kasa hada ido dashi kuwa maigidanta ya fad’a mata cewar lokacin da ta kira wayarsa tana fada masa a binda ke faruwa Abbah Abbas din na kusa dashi kuma yaji komai, wannan dalilin yasa ta kasa zama a gidan tayi musu sallama da ta tafi…Naja’atu kuwa dama ko zama ba tayi a palon ba ta shige dakinsu mussadiq tayi kwanciyarta.
********
A tsakanin kwanaki biyu zamantakewar gidan duk ta dawo wani iri Halisa tayi sanyi sosai tunda taji maganar rukiya ta shiga nutsuwarta ta daina rawar kai sai ta yini a dakinta ma bata fito ba Naja’atu da Baba Larai ne kawai suke sha’aninsu…..Yau ya kasance girkin Naja’atu ne, tana ta murna dare yayi su ke’be da maigidan dan gaskiya kwana biyu tayi missing din soyayyarsa ta shirya cikin ‘kananun kaya wanda sukayi mata kyau sosai ta zauna a palo cikin yaran suna ta wasa da dariya, taji dadi sosai da taga halisa ta daina power a gidan…..Koda ya shigo gidan ya gansu a palon sai yaji farin ciki ya lullubeshi, amma rashin ganin Halisa a cikinsu ya sosa masa rai! salo salo din da Halisa takeyi bayayi masa dadi ko kadan, dan haka bayan ya amsa gaisuwarsu kai tsaye dakin Halisa ya nufa….Naja’atu tabishi da kallo tana jan tsaki. ta tsani taga yana mu’amular arziki da Halisa( Ikon Allah wai Naja’atu meke damunki ne kullum kina cewa bakya son mutum amma kina kishi a kansa da alama kema kina bukatar ayi miki rukiyar)……Samunta yayi a kwance tayi shuru, ya tsaya a kanta da fad’in “Halisa wai me akayi miki ne kika takura kanki kwana biyu bana jin dadin abinda kikeyi a gidan nan dan Allah ki saki jikinki kamar da ki cigaba da mu’amular ki da kowa.
Kuka tasa tace” Ba dole na ke’be kaina ba tunda ni mai laifi ce a gidan nan yarinyar ‘karama na zagina na bangazata nayi min dariya ai dole na takura idan kuma na dauki mataki a kanta a dauki laifi a dora min ai ni kam walwalata da farin cikina ya kare a gidan nan.”
Yace.”Kiyi hakuri insha Allahu ta kusa ta bar miki gidanki ni nagaji da wannan tashin hankalin naku me yasa lokacin Halimatu kuke zauna lafiya da juna.” ? Tace”Halimatu daban take a cikin mata Naja’atu kuwa annoba ce a cikin mutane wallahi watarana yarinyar nan sai ta wargaza maka gidanka idan ba kayi da gaske ba.
Yace.”Magana dai ta wuce insha Allahu komai ya kusa zuwa karshe ki taso ki bani abinci.” Yafada yana me juyawa da niyar fita..Halisa dama irin wannan damar take nema tunda tasan ba girkinta bane to tunda ya nema da kansa bari taje kodan ta cuzgunawa yarinyar
Naja’atu na ganin sun fito daga daki a tare tayi saurin dauke kanta zuciyarta ta sosu amma dai ta share bata nuna komai ba gabadayansu suka zauna gurin cin abincin…..Tana kallon abubuwan da Halisan keyi masa yayi shuru baice komai ba ga yara a zaune sai haushi ya isheta kawai ta mike tana kallon yaran tace”Kowa ya dauko plate dinsa muje palo muci a can.” Da sauri suka mike kowa ya dauki nasa, dama can haka suke daga tace musu ga yanda za suyi basa yi mata musu…Halisan dashi kansa suka bisu da kallo domin kuwa sun rasa abin cewa….
To sai bayan goma na dare suka kashe tv kamar dai koda yaushe suka nufi daki domin shirin kwanciya…Naja’atu wanka akaje a kayi tayi bursh ta shirya cikin kayan bacci harda sa turare ta zauna tana jiran shigowar maigidan tasan dole idan ya shigo sai ya nemi data bishi dakinsa aikam zata bishi dan yini tayi cikin sha’awa da tashin tsigar jiki idan ta tuno soyayyarsa har wani lumshe idonta take……Har karfe goma sha daya da rabi idonta biyu tana jiran shigowarsa shuru bai shigo ba, ranta ya baci sosai, a sanyaye ta shiga gyara shimfidarta dake kasan kafet taji ya turo kofar ya shigo da sallama ajiyar zuciya mai sanyi ta sauke ta amsa masa ya karaso cikin dakin sosai kai tsaye taga ya fara zagaya gadon yaransa yana musu addua kamar yanda ya saba! shuru tayi tana binsa da kallo har ya gama musu ya juya zai fita ba tare da ya tanka mata ba
Takaici kamar ya kasheta kamar wata shashasha tabi bayansa da kallo tana ji kamar taje ta rungumeshi…Kwanciya tayi tana kuka tare da takure jikinta tana jin danshi danshi a pant dinta tsabar sha’awar data yini dashi yasa ta zubar da ruwa sai kace kankana.
Shi kuwa Abbah Abbas bacin ran da yake cike ne yasa yaji gabadaya ma baya sha’awar komai baban burinsa ya kwanta ya huta sannan kuma yayi tunanin yanda zai kawo zaman lafiya a gidansa dan ya lura ba k’aramin gagarimin aiki bane a cikin zaman Halisa da Naja’atu a gidansa.
Washe gari gidan haka kowa ya tashi da rashin walwala dalili ruhikan gidan (Abbah Abbas da Naja’atu) basa cikin walwala sai ya kasance suma yaran basu da walwala Halisa kuwa a cikin yaran babu wanda yake ta tata.
Tsaf ya fito da shirin fita, Halisa da Baba Larai ne a zaune a palo suna hira…Ya duba yaga babu naja’atu a gurin kai tsaye sai ya nufi dakin yaran, nan ya sameta a kwance tashi tayi zaune tana kallonsa…Sai da ya kalli agogon dake daure a hannunsa sannan ya kalleta babu cikakkiyar walwala a tare dashi yace.”Ki shirya anjima kadan Salim zai zo ya kai ki kasuwa kamar yanda nayi miki al’kawari.” A dan sanyaye tace”To nagode.” Fita yayi ba tare da ya sake cewa komai ba.
Shuru tayi bayan fitarsa tana tunanin sauyarsa kodai haushinta yake ji kan abunda ya faru jiya oho koma dai menene ai ba ‘karya tayiwa matarsa ba ta tabbata idan da Halisa ta samu dama a kanta mugun rauni za tayi mata, tasa hannunta a gefan fuskarta ta shafa inda ciwon yake cike da takaici tace”Allah yasa macuciya kawai.”
Salim yazo ya d’auketa kamar yanda ya fada mata…Kai tsaye sahad store dake zoorod suka nufa…Naja’atu ta dinga kallon Salim a fakaice tana mamakin sauyawarsa Salim ya goge sosai yayi ki’ba ga wani uban haske da yayi idanunsa sun kara bud’ewa! sai taji duk jikinta yayi sanyi ganin kamar Salim din kamar yafi karfinta….Salim murmushi yayi ya kalleta yana kanne mata ido yace”Anty Naja’atu ya gida ina fatan kina nan lfy.”
Ta ‘bata rai murya na rawa tace”Salim bana son sunan nan da kake kirana dashi ni wallahi sai nake ganin kamar ka daina sona yanzu.” Salim ya shafa sajensa yana wani munafikin murmushi yace.”Ai naja’atu ina kyautata zaton da soyayyarki zan mutu hausawa na cewa fad’an da yafi karfinka sai ka mayar dashi wasa, naga Kawu Abbas ya rike wuta a kanki shiyasa na cire rai da samunki.”
Tace”Salim wallahi ina nan ina kokari kan al’amarin nan dan Allah ka daina wannan maganar indai zaka aureni ni kuma nayi maka al’kawari insha Allahu zanyi duk yanda zanyi naga bukatarmu ta biya.