MADADI 1-END

MADADI Page 41 to 50

Tace”A’a baba nifa wannan maganar ba zan barta ba wallahi idan ya dawo sai na fada masa ga abinda tace a kaina.”

Baba larai tace”Ikon Allah ke yarinyar nan baki da wayo waye ya fada miki komai ake fadawa miji yawan kai ‘kara ga miji yana sanyawa daga ya ganki gabansa ya fad’i! duk ranar da kuka samu sa’bani da kishiyarki ki daina gaggawar fad’awa miji idan kika saba da kai masa ‘kara kullum zai dinga ganin kamar kece mai laifi.

Tace”To ai maganar ce gabad’aya ba tayi min ba wai sai bukatarta ta tabiya a kaina to me za tayi min? burinta na bar mata gidanta bata san nama fita so na fita daga gidan ba.

Larai tace”Magana dai ta wuce naja’atu dan Allah ku zauna lafiya kuma ki daina yi mata rashin kunya da habaici abinda yake tunxura mata zuciya kenan.” Dariya tayi tace”Ni wallahi baba bada ita nake ba kawai dan ina wa’ka sai ta tsargi kanta dan rashin gaskiya.

To koda maigidan ya dawo ta nuna masa kayan nata da ya duba shima sun bashi sha’awa sun burgeshi sosai yace ta dauki wanda take so sai suje da Halisa gurin da ake mata dinki dan yana sha’awar ire iren dinkunan da Halisa take masa ado dashi a gida shiyasa yake so ayi wa naja’atu irinsu.

Tace”Bata da ra’ayin haka tafi so a kaiwa telan da yake musu din’ki tsarin d’inkunansa yafi burgeta…Yace tunda haka take so shikkenan sai ta shirya Gobe Salim zai zo ya kaita ta kai masa.

Yau ma kamar jiya da ya shigo dakin gadajen yaransa yabi yayi musu addua ya fita daga dakin ba tare daya kulata ba, hakika taji ciwo da takaicin abin ace kwana biyun girkinta sun tashi a banxa babu wani dan romance da sauransu…Dan haka koda ya shigo da safe da kyar ta gaishe ta juya masa baya tana jinsa yana magana da yaransa bata tanka musu ba har ya fita daga dakin

Sosai tasa ido taga abinda zai wakana a tsakaninsa da Halisa tunda yau ya kama girkinta ne…Halisa yau ingilish wear tasa ko kunya ba taji ga yara a gida koda yake Halisa ita abu takeyi kai tsaye a gidan sam bata jin kunyar yara

Naja’atu dariya kawai take dannewa dan ganin yanda halisa aka ci gayu cikin wata iriyar riga mai gidan nono rigar bata da hannu gajere ne sai madaurai guda biyu a bayanta wani matsatstsan siket tasa halisa bata da gashi amma gwanar kitson ‘karin gashi ce duk tsantseni da kula da addini irin na maigidan sai da ya saurara mata dan idan babu wannan kitson a kanta tana komawa tamkar namiji tunda gashin kanta bashi da yawa hakuri kawai yayi ya kyaleta take sa attecment a kanta amma kullum idan ya tashi fad’ansa zai ce mata ta san da sani sallahr da takeyi ta banza ce kuma idan danshi takesa gashin doki to ba burgeshi take ba…Halisa tayi kunnan uwar shegu dashi, dole tasa ya hakura ya kyaleta ya sa mata ido.

Kasancewarsa mai so yaga irin wannan dressing din a gidansa yasa da ya dawo yaga Halisa cikinsu hankalinsa ya tashi fitinarsa ta kwana biyu ta motsa, dama tubarkallah ga Halisa da lafiyayyan jiki mai kyau sai yaji ya sake kwadaituwa da ita da irin salonta…Naja’atu duk tana hankalce dashi a gurin cin abinci ma da kyar yaci ya basu guri..a maimakon ya zauna a palo ya duba loptop kamar yanda ya saba sai taga kawai ya nufi dakinsa….Har kusan tara da wani abun na dare bai fito ba yana cikin dakin…Duk sai taji rashin dadi mussaman da taga Halisan tabi shi dakin..Cikin mutuwar jiki da jin wani irin zazzafan kishi ta bar palon…

a daran sai da taci kukanta ta koshi sannan bacci ya dauketa..

Koda ya shigo da safe barcin karya ta tsira har ya gama abinda yake ya fita daga dakin bata ido idonta ba.

Haka zaman gidan ya cigaba da gudana duk ranar girkin Naja’atu sai yaji tamkar an dauke masa sha’awarta ranar girkin Halisa kuma kamar kara masa karfi da kuzari akeyi a jikinsa idan sun raba dare suna abu daya to da safe ma kafin suyi break fast sai sun maimaita wani( Ikon Allah Aljana *’Yar Zabira* ta sanja suddabaru kenan wato ranar girkin Naja’atu tana kashe masa jiki ranar girkin Halisa tana saka masa kuzari ashe ba rabu da bukar ba wai an haifi habu Allah ka karemu daga sharrin aljani ko wane iri ne)

Naja’atu daina walwala tayi gidan dan saboda abubuwan da ake mata sun fara isarta kawai dai tana kokarin gaishe shi ne amma kwakkwarar magana bata yarda ta hadata dashi dan saboda mugun haushin sa da take ji.

Yau ya kasance ranar girkinta kuma saura kwana biyu su tafi umara kamar yanda taji suna fada dan duk wani shirye shiryensu sun gama har dakin yaran ya shiga ya sameta da daddare hannunsa rike da kwalin sabuwar waya iPhone! Gasheshi tayi ya amsa cike da kulawa bai zauna ba dan ji yayi tamkar ana axalzala zuciyarsa ya fita daga dakin…Ya mike mata wayar da fad’in “Kar’bi kisa a charge sabuwar waya ce na siyo miki.”

Kallon kwalin wayar tayi kafin ta mika hannu ta karba tace nagode.” Yasa hannu ya gaban rigarsa ya ciro dan karamin cover ya mika mata da fadin ga sim card din.” Karba tayi ba tare da tace komai ba..Kamar zaiyi magana sai kuma yaja bakinsa yayi shuru ya juya ya fita.

Wayar ta bude tana dubawa murmushi tayi na farin ciki dan saboda wayar ta burgeta sosai kuma ko babu komai tasan zata d’ebe mata kewa cajar wayar ta warware ta bude wayar tasa sim card din sannan tasa a chaji ta koma ta kwanta tana cigaba da tunanin yanayin rayuwar data tsinci kanta, yanzu ta samu waya bata da matsalar gurin neman kawarta Munira tana jira su tafi saudia ita kuma ta gudu garinsu Munira su nemata su rasa tunda dai kowa ya kasa fahimtar abinda ke damunta.

Ranar da zasu tafi gabadayansu kofar na’isa suka nufa saboda harda Hajiya za’ayi tafiyar, Hajiya Abu ganin Naja’atu kamar tana da damuwa yasa ta dinga rarrashinta da fad’in ta kwantar da hankalinta wata shida kamar yau ne insha Allahu ita aikin hajji za taje idan Allah ya nufa…To ganin yanda Hajiyar ta damu da ita yasa ta saki jikinta ta nuna ai babu komai ita bata kishi dan sunje umara da Halisa itama idan Allah ya nufa za taje…Hajiyan taji dadin hakan ta cigaba da kwantar mata da hankali ita kuma tana nuna komai ba komai bane.

Gabad’ayansu ita da yaran da Yaya Ramlatu Alhaji da baba malam Abbah Magaji suka rakasu airport tare da fatan alkairi Abbah Abbas yabi yaransa daya bayan daya rungumesu yana musu addua. itama yanda yayi musu yayi mata tamkar yar cikinsa ba matarsa ba sam yanzu babu wata kyakykyawar mu’amula a tsakaninsu..Halisa kam sai wani Jiji da kai take tana hura haci ita gata matar da akeso…Ita kuwa Naja’atu mugun alwashi taci a kansa tana ganin ita ba ‘yar wahala bace da zata zauna tana yi masa gadin yara ya tafi da matar so wallahi sai ta bar gidan koma me zai faru sai dai ya faru….

Satin su daya da tafiya Baba Larai ta rasa gane kan Naja’atu yau da lafiya gobe babu ga wani shegen zazzabi me naci da takeyi kullum da daddare haka zai zo ya rufeta tayi ta makyarkyata, da safe kuwa da wani d’an iskan amai mai mugun da’ci take farawa ta dinga kakari kenan a toilet tana rike cikinta.

Baba larai dai ba yarinya bace dan kallon farko da tayi wa yarinyar yasa ta gane cewar da akwai juna biyu a jikinta, to dan saboda ta tabbatar yasa da Anty maryam da ta shigo dubasu ta sheda mata halin da ake ciki…Anty maryam tace”Nima sai da na zargi haka tunda Allah yasa gobe litinin sai muje asibiti a dubata. larai tace”Hakan shine ya dace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button