MADADI 1-END

MADADI Page 41 to 50

Abbah Abbas koda dare yayi bai sake yunkurin kiranta a waya ba, sai kawai ya kira wayar abokinsa ya tambaye shi yanayin jikin nata, Abbah magaji yace masa jiki yayi sauki sosai dan maryam ma bata jima da fitowa daga gidan ba.

Hankalinsa ne ya kwanta sukayi sallama da juna yana d’an jin sassauci a cikin ransa, amma idan ya tuno wulakancin da yarinyar tayi masa yana ji tamkar yayi tsuntsuwa yaje yaci mata mutunci ko ya huce.

Washe garin ranar Naja’atu da niyar guduwa ta tashi sai kuma su Baba malam suka dira a gidan! Ganinsu yasa duk jikinta ya mutu ta dinga share hawaye a fakaice tana nadamar abinda zata a kaita musu na bacin rai….Nasihohin da malam yayi mata sunyi masifar kassara mata jiki taji kamar ta hakura kawai ta cigaba da zama a gidan tunda haka Allah ya tsara mata rayuwarta, sai dai suna tafiya ko gida basu je shed’aniyar ‘kawarta Munira ta kirata a waya tana sake zugata kan abinda suka kudurta.

Washe gari ta kuma tashi da yunkurin guduwa garin Jos garinsu Munira sai kuma Allah ya saukar mata da ciwon ciki. ta yini a kwance tana murkususu! duk da tasha maganin ciwon bai lafa mata ba sai dare lokaci guda ta rame saboda tsananin axabar da taci

A daran ta sake kwanciya da kudurin garin Allah na waye wa zakara zai bata sa’a! aikuwa hakane ya kasance yara na tafiya makaranta lokacin Larai na kicin tana aike aike ita kuma ta fito, cikin rashin kwarin jiki da karfin hali taja k’aramar akwatin kayanta ta fita daga cikin gidan…

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button