MADADI Page 41 to 50

Tana kokarin shiga sukayi karo da Naja’atu zata fita. Tace”A’a naja’atu ina zakije kuma.”? Ko kallonta ba tayi ba ta kama hanyar fita…Halisa tace”Naja’atu kina ji ina miki magana kin share ni.
Hannu ta daga mata a fusace! tace”Kinga Anty Halisa bana son gulma da munafurci dan Allah bake kike aurena ba ballantana ki dameni da tuhumar ina zani aikin banza aikin hofi kawai wallahi kada ki dauka duk abinda kike bana ganewa ina sane, kuma ke kika damu da wannan tsohon har kike satar kwana ki rubuta ki ajiye na kusa fita na bar miki gidanki dan banga gurin zama a cikinsa ba.”
Halisa ta bude bakinta tana kallonta cike da mamaki! Naja’atu buge zaninta tayi ta bar gurin….Halisa ta juya tana wani irin murmushi ta nufi cikin gidan ranta wasai bukatarta ta kusa biya.
Dakinta ta shiga ta dauki wayarta ta kira maigidan nasu.
Yace”Allah yasa dai lafiya. cikin alhini da yanayi na a tausaya mata tace”Yanzu yanzu na Naja’atu ta gama zagina saboda kawai na tambayeta ina zata je shikkenan take zagina harda kiran ka tsoho da fadin cewar na fad’a maka wai a kurkusa zata bar maka gidanka domun kuwa ba taga gurin zama ba.
Cike da mamaki yace.”Naja’atu tace fada miki hakan.” Salim dake driving yasa kunne sosai jin an kira sunan Naja’atu.
Halisa tace”Kwarai kuwa wallahi ni kaina banji dadi ba me yayi zafi! ni banga abin’ki a tattare da kai ba.” Jikinsa a sanyaye yace.”Koda ta dawo gidan kada ki sake shiga sabgarta ballantana ta sake zagin ki ki rabu da ita dani take zancen zan dawo na sameta. Halisa farin ciki ya wanke mata zuciya tace”To shikkenan Yallabai Allah ya dawo mana da kai lafiya.” Ya amsa da amin tare da kashe wayarsa.
Naja’atu kam tana zama a gidan anty maryam kuka tasa……Anty maryam ta zauna kawai tana kallonta dan babu yanda ba tayi da ita ba akan tayi shuru tayi mata bayanin abinda ke faruwa amma taki tayi shuru sai da taga dama tukkuna ta share hawayenta tana kallon aunty maryam din tace”Anty wallahi bashi da lafiya.” Anty maryam ta zuba mata ido tana kallonta da fadin”Waye bashi da lafiya.” ? Kai tsaye tace”Abbah Abbas mana Allah aunty yana da matsala babba ni bazan iya zama ba dan cutata kawai yake….Anty maryam duk shekarunta kasa gane inda maganar ta dosa tayi.
Tace”Kinga ni kiyi min bayani yanda zan fuskanta wace irin rashin lafiya yake.”? Hanci taja tace”Baya iya biya mun bukatata kullum sai dai ya tayar min da hankali ya barni cikin sha’awa saboda haka tun kafin tafiyar nan tayi nisa ku san yanda zakuyi ku warware shi.”
Anty maryam tayi ‘kasa da kanta kunya kamar ta sa ta nutse a gurin, ashe naja’atu bata da kunya haka har ta iya zuwa tazo tana yi mata wannan maganar gaba da gaba lallai ‘yan matan zamani halinsu sai su!
Sai da ta aro jarumta tukkuna ta dago kanta tana kallon Naja’atun ta ‘bata fuska sosai tace”Ke Naja’atu bana son sharri wallahi! Ni tunda nake da Halimatu da Halisa babu wacce na ta’ba jin tayi wannan maganar! Sharri ne kawai irin naki! sannan har yaushe akayi auran naku da zaki tantance yanda al’amarin yake har kike cewa baya biya miki bukatarki wallahi kiji tsoran Allah.
Itama shan kunu tayi tace”Aunty Maryam ya zaki fad’i wannan maganar ? nifa macace kuma ina da sha’awa sai kuma kice wani abu ni wallahi gaskiya na fad’a banyi masa sharri ba ki fadawa mijinki a san yanda za’ayi.
Anty Maryam ta rike bakinta tana kallonta cike da mamaki tace”Wai ke baki da hankali ne? wai kike tunanin zan fadawa wannan maganar? Humm! ba dani ba ke idan kina ganin kina cutuwa sai ki tsaya yayan naki ya dawo ki fada masa amma ni babu ruwana….Cikin takaici tace”To shikkenan ai kuwa wallahi in tura ta kai bango sai na fad’a! ai sune suka cuce ni yama za’ayi su auran min tsoho mara kuzari ni kam ba zan iya wannan takaicin ba.
Anty maryam shuru kawai tayi tana kallonta mamakin ta kawai take lallai *Zamani* Indai akace maka *Zamani* to magana ta ‘kare ita kam tana jin koda mijinta baya iya gamsar da ita zata hakura ta zauna sabida tana jin kunyar taje gida ta fad’a to taya ma zata farayi wa iyayenta bayani
*(Wannan ba dabara bace Aunty Maryam akwai ‘kwaruwa ace namiji baya biya wa matarsa bukatarta sai dai ya biya tashi, akwai matsala babba! matsalar da kan iya janyowa mace fad’awa ga halaka! mata da yawa suna nan sun fad’a harkar madigo duk sabida irin wannan matsalar akwai wanda kuma suke bin mazan waje da auransu da komai amma kuma mazajen nasu sun zama hoto a gurinsu….’Yar uwa idan kina fuskantar irin wannan matsalar kada ki zauna kiyi ta cutar kanki ko kuma ki jefa kanki ga sa’bon Allah! Akan ki sa’bi Allah gwara kin kashe auran kije kiyi wani shine yafi miki alkairi…ko kuto kika kai al’kali ba zai ce miki don me ba sabida shima yasan matsalar gagarima ce…Allah kasa mu dace)*
Aunty Maryam ta mike da sanyayyan jiki ta kalli Naja’atun tace”Ni dai duk wannan surutun da kikeyi babu wanda na dauka a ciki dan sabida nasan karya kikewa bawan Allah nan wallahi ki sanja halinki Naja’atu.”
*(Eh gaskiya kam Naja’atu karya tayi wa Abbah Abbas lafiyarsa lau kawai Halisa ce tayi musu farraqu)*
Ganin anty maryam din na kokarin shiga kicin yasa tace”Dan Allah dan bani aron wayarki zan kira kawata.” Anty Maryam tace”Tana dakina ki shiga ki dauka.
Da sauri ta mike ta nufi dakin nata…Kan mirror taga wayar ta dauka tare da zama bakin bed dinta…Numbar Munira tasa bugu daya tayi ta daga wayar.
Munira najin muryar Naja’atu tace”Kamar *Na’ja’atu Abbas qofa* Naja’atu tace”Eh nice kinyi mamaki ko.” Munira tace”Eh lallai nayi mamaki Naja’atu yau kin tuna dani kenan ai wallahi baki da kirki Naja’atu.”
Murmushi tayi tace”Nasan dole dama ki fadi haka amma dan Allah kiyi hakuri kinji ko wayata ce ta lalace shiyasa kika ga na kiraki da wannan numbar wayar aunty na ce.”
Munira tace”Babu komai ‘ k’awata ya kwana biyu! wallahi baki yanda nake ji ba a duk sanda na tuno rayuwarmu ta makaranta.
Naja tayi murmushi tace”Wallahi nima haka munira ina kewarki sosai cikinmu duk ke kad’ai ce mai zumunci kinyi kokarin ziyartar inda nake nima a lokaci da nake shirye shiryen kawo miki ziyara wata kaddara ta gifta min.”
Munira tace”Innalilihi Naja’atu me ya faru da rayuwarki……Naja’atu ta goge hawayen dake zubo mata ta shiga bata labarin abinda ya faru bayan rabuwarsu…..Munira tace”Yanzu dama Mamma Halimatu ba itace ta haifeki ba.”? Tace”Wallahi munira nima ban sani ba sai bayan mutuwarta…Munira tace”Ubangiji Allah ya jikanta halinta na gari ya bita, ammafa ‘kawata Abbah Abbas yayi masifar bani mamaki lallai shi ko kunya baiji ba yazo ya wani aureki sabida son kai ai wallahi idan nice ba zan yarda ba gaskiya an cutar dake.”
Naja’atu zuciyarta ta sake karyewa tana zirarar da hawaye tace”Munira na rasa wane mataki zan dauka wallahi mutumin nan ya nace min dik wani wulakanci da iskanci nayi masa kamar maye yaki yayi zuciya ya sakeni.”
Munira tace”Kici kwalarsa kawai in ta kama ma ki zazzage shi!! nasan zai sake ki idan kikayi masa haka.” Naja’atu shuru tayi tana nazarin maganar! Anya kuwa zata iya cin kwalar Abbah Abbas! Tace”Munira ba zan iya yi masa hakaba yana da babban matsayi a zuciyata bazan tozarta shi irin wannan ba. Munira tace”To shikkenan wace shawara kika yanke ni dai idan zaki dauki shawara ta kiyi masa haka.” Tace”Idan na yanke shawara zanyi miki waya.” Tace”To shikkenan ni kuwa ina Salim kuma yaya yayi da yaji faruwar wannan al’amarin.”?