MADADI Page 41 to 50

Murmushin takaici tayi tace”Ya shiga tashin hankali da farko amma yanzu gani nayi kamar ma ya daina sona tunda har yake iya kirana da auntynsa.” Munira tace”Lallai Salim gaskiya baiyi hallaci ba amma babu komai koda bai aureki ba ai idan kin futo ba zaki rasa saurayi mai jini a jika ya aureki ba, alhamdullhi kina da kyau da duk suffofin da ake so a jikin mace, wallahi akwai wani abokin Muktar wanda zan aura kenan dan gayu ne sosai sunansa khamis yana da hankali da nutsuwa ga kuma kudi da duk abunda mace take bukuta, insha Allah zan hadaki dashi nasan ya ganki zai soki tunda kin cika mace.”
Naja’atu tace”Ni yanzu babban burina na rabu da auran wannan tsohon saboda na tabbatar da cewar ba zanyi wani nauyi ba zan samu daidai dani na aura.” Munira tace”To shikkenan ina sauraranki idan kin yanke shawarar sai ki kirani ki fada min ni kuma zan taimaka miki saboda darajar k’awancen mu.” Tace”To nagode kawata sai kinji ni.” Sallama sukayi da juna, ta kashe wayar tare da ‘kurawa kasan kafet din dakin ido tana tunanin shawarar da zata yankewa kanta…
Aunty Maryam ce ta shigo dakin ta ganta ta zabga tagumi dan gabad’aya ma bata san ta shigo dakin ba, aunty Maryam Jikinta ne yayi sanyi ta tsira mata ido cikin zuciyarta tace”Kodai yarinyar nan da gaske takeyi da maganar da tazo mata dashi to idan ba haka ba me zai sanya ta shiga damuwa irin haka, gaskiya to idan ya kasance gaskiya ne yarinyar zata shiga damuwa tunda ta lura bata da hakuri ta wannan bangaran kuma tana da karfin sha’awa tabbas kuwa tunda har ta iya zuwa tafad’a mata maganar abin na damunta saboda haka zata yi dubarar fad’awa maigidanta taji abinda zaice.
Zama tayi a kusa da ita ta dafa kafadarta a sanyaye ta kira sunanta, ta juyo tana kallonta idonta na kokarin kawo ruwa.
Anty maryam tace”Ki daina kuka kinji ko! jikina kuma yayi sanyi yanzu dana ganki cikin damuwa, tabbas hakan tana iya kasancewa gaskiya ne insha Allah idan Abbah Magaji ya dawo zan fad’a masa abinda yake faruwa sai muji abinda zai ce a kan matsalar abokin nasa ke kuma dan Allah ki daina wannan kukan da kikeyi ita mace da kawaici da hakuri a kasanta.
Dan ta ‘kara tunzura Anty maryam din tace”Ni wallahi anty bazan iya hakuri na jure ba ni bani da hakuri ta wannan bangaran kawai a san yanda za’ayi.”
Aunty Maryam tace”Ni abinda yake bani mamaki anan kince bakya sonsa to ya akayi kike sakin jikinki dashi har wata mu’amula take shiga tsakaninku kike jin dadi wanda har kike ganin kamar yana cutarki.”
Tace”Aunty shine kullum sai yazo yayi wasu abubuwa wanda suke sawa hankali na ya tashi ni wallahi da baya ta’ba min jikina bazan damu ba amma kullum sai yayi ta damuna ni kuma na kasa hakuri.”
Aunty Maryam tace”Tom magana dai ta wuce kija bakinki kiyi shuru kada ki fadawa kowa kuma kada ki sake Halisa ta sani dan za tayi farin cikin hakan ki cigaba da bashi kulawa insha Allah idan bashi da lafiya to zai samu sauki ai kowace cuta nada maganinta.”
Shuru tayi kawai Aunty maryam ta cigaba dayi mata nasiha gami da koya mata dabarun zama da miji da kishiya Naja’atu jinta kawai takeyi domin ita ta riga ta gama yankewa kanta hukunci.
Sai bayan la’asar ta koma gidan, nan tarar da wata dattijuwa a zaune a palo ita dasu Saddiqa, ta zauna kan kujera tana fuskantar matar suka gaisa a nutse, matar tace”Sunana Larai daga gidan Hajiya nake tasa aka kawo ni nan gidan domin na dinga taimakawa matan gidan da aikace-akaice.”
Sai da matar tayi mata bayani sannan ta gane cewar mai’aiki aka kawo musu, tace”To sannu da zuwa Allah ya bamu hakurin zama da juna.” Matar tace”Ameen ya Allah.
Tace”Ina kayanki suke.” Larai tace”Suna can wani daki a harabar gidan Hajiya tasa an kai mun can tace can ne masaukina.”
Tace”To hakan yayi Allah ya taimaka.”
Larai tace”Ameen” Halisa ce ta fito daga dakinta ganin Naja’atu da larai suna hira sai ranta ya ‘baci! Ta kalli Larai fuska a ‘bace! dama can halisa akwai girman kai tace”Yana da kyau ki shiga kicin ki fara aikin ko.”
Larai ta mike da sauri tana fadin “To Hajiya a nuna min kicin din.” Tace”Muje na nuna miki yanda ake amfani da komai.” Larai tace”To.” kicin din suka nufa Naja’atu ta bisu da kallo tana girgiza kanta, Halisa ba ‘yar gidan uban kowa ba amma dan kawai tana auran mai kudi sai shegen girman kan tsiya, tsaki taja ta kalli Mussadiq dake mata magana
Tace”Ba gidan Alhaji naje ba gidan Aunty Maryam naje.” Yaron yace”Da kin sani kinje dani Yaya Naja’atu. Tace”Wani weakend din sai ku tambayi Abbanku kuje ku yini a can.”
Mufida tace”Aikuwa zamu tambaye shi.” Ta kalli Saddiqa da fadin”Saddiqa ya hannunki.” Yarinyar tace”Hannu ya warke kinga yanzu ina iya amfani dashi ba tare dana ji zafi ba.” Tana kokarin mikewa tace”Allah ya kara sauki.” dakin yaran ta nufa, ta shiga wanka ta fito daure da zanin atamfar jikinta jakar kayanta ta bude taga babu duk ta sanye su sai ‘kananu irin na kanti sai dogwayen riguna ita kam ba zata sa doguwar riga ana zafi ba riga da sket ta dauka tasa a jikinta ta gyara gashinta tasa masa ribborn ta gaji da rashin kitso tana ganin dole ta tambaye shi zuwa kitso kanta kusan satin sa biyu a tsefe! gashi tubarkalla tana da gashi babu laifi….Dankwali abaya ta daura a kanta ta zauna tana hada kayanta dana yaran wanda da sukayi daud’a! ta fito palon tana kallon Mufida tace”Kije bakin gate kiga idan me muku wanki nan kice yazo ya dauka.”
Yarinyar tace”To” Da sauri ta mike zata fita..Halisa ta fito daga kicin tace”Ke ina zakije.”? Tace”Yaya Naja’atu tace naje na kira Yunusa mai wanki.”
Cikin tsawa tace”Koma ki zauna idan ita ba zata je ba to ta aiki wanda take da iko dasu.
Yarinyar ta kalli Naja’atu dake tsaye tana kallonsu…Jikinta a sanyaye taje ta zauna saboda tana masifar jin tsoron mommyn nata tana kuma tsoron irin dukan da take mata….Saddiqa ta mike ta nufi dakinsu ta sako hijabinta ta nufi kofar fita.
Naja’atu kuwa murmushi tayi ta zauna kan kujera da fad’in “Allah yasa nima na haifa kafin ki haifa ballantana kiyi min gori ina da masu share min hawaye ehe.”!! Halisa na jinta tayi mata banza so take kawai maigidan ya dawo taga irin hukuncin da zaiyi wa yarinyar na fita ba tare da saninsa ba kuma tasan ya tsani yawo komai shirin da kuke dashi kukan iya ‘batawa dashi idan yaji maganar zuwa unguwa shiyasa itama bata fiye zuwa sabgogin danginta ba saboda kullen da yake musu.
Larai tuwo tayi musu na farar shinkafa yayi kyau sosai ga lafiyayyar miyar bushashshiyar kubewa da taji nama da daddawa da kayan kamshi, cikin nutsuwa ta shirya musu gurin cin abincin tayi musu sallama ta nufi masaukinta.
Halisa kuwa zuwa akayi ka cancad’o ado da wani uban material mai tsadar gaske sai dai anyi masa banzan dinki riga da siket ne duk an tsaga shi hannun riga mai tsayi da gajere tasa turare mai kamshin gaske, palon ta fito tana shan k’amshi
Naja’atu da yaran suka bita da kallo, Naja’atu Kallo guda tayi mata ta dauke kanta tana kunshe dariya! Halisa ta lura da ita sai ta shareta ta zauna kan kujera hade da daukar romot tana dannawa! Yaran kuwa motsin kirki sun kasa yi wanda da kafin fitowar Halisa hayaniya suke akan film din da suke kallo amma zamanta a gurin duk yasa sun shiga taitayinsu……Haka suna ji suna gani ta sanja musu tashar da suke kallo ta mayar dashi Mbc1 tashar larabawa, gabadaya yaran basu ji dadi ba dan yanayin su sai da ya nuna….Naja’atu ta kalleta a da’kire! tace”Kallo fa suke zaki dauke musu dan Allah ki mayar musu su ‘karasa.