MADADI Page 71 to 80

Girgiza kanta ta shiga yi tace”Kin san Allah Mmn Sajida ba zaki ruguza sana’arki kaina ba! Ban amince ki siyar da shinkafar ki ba.” Mmn Sajida tace”To ya kike so ayi? Kin san dai babu wanda zanje gurinsa da bukatar ya bani aron kudi ya bani kai tsaye mutane yanzu kwata kwata basa bada bashin kudin.
Naja’atu shuru tayi tana tunanin yanda za tayi gaskiya ba zata bari Mmn Sajida ta rusa sana’arta a kanta ba tunani ta shiga yi ko ta kira Abbah Magaji a waya ta fad’a masa halin da take ciki! Girgiza kanta tayi, gaskiya ba zata iya kiransa a waya ta fad’a masa cewa ya taimaka mata da kudin magani ba saboda tasan halin masifarsa, kuma bata manta cin fuskar da tayi masa ba tana jin kunya sosai…..’Daya bangare na zuciyarta yace mata kawai ki kira wayar Abbah Abbas zai taimaka miki tunda dama shi mai tausayi ne zai iya turo da kudi a biya asibiti kudinsu…Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin kamar wannan shawarar data yanke itace shawarar data dace dan gaskiya ba zata amince da shawarar Mmn Sajida ba…..Suna tsaka da tunanin mafita likita ya sake shigowa ya kalli Mmn Sajida da fad’in “Hajiya ku muke saurara dan tuni mun sallameku ku biya asibiti hakkinsa.
Murya na rawa Mmn Sajida tace” Dr kayi hakuri yanzu zan je gida insha Allahu kafin goma na dare zan kawo maka kudin.”
Dr yace”Ni tara tana yi na tashi daga aiki wani ne zai maye gurbina kuma kuka kwana to kud’inku ya qaru zaku biya dubu ashirin da bakwai da dari biyar.” Mmn Ladi ta zare ido tana kallonsa! Ita kuwa Mmn Sajida mi’kewa tayi da sauri tana fad’in “Insha Allahu yanzu zan dawo.” Dr ya kalli agogon hannunsa da fad’in “Okey idan kika wuce tara baki dawo ba to ba zaki sameni ba.” Yana gama maganarsa ya juya da niyyar fita.
“Dr.” Muryarta ta katse musu hanzari daga shi har Mmn Sajidan da take kokarin bin yansa domun tafiya…..Duk suka juyo suna kallonta, tace”Idan babu damuwa ina bukatar ka bani aron wayarka zan kira mahaifina da ita insha Allah za’a tura maka kudinka.”
Dr yayi kasaqe! yana kallonta kafin ya d’an d’age kafad’arsa ya dauko wayarsa dake gaban aljihun rigarsa ta likitoci ya karasa har bakin gadon da take zaune ya miqa mata….Ta kar’ba a sanyaye, tana dubawa dama kafin ya bata wayar sai da ya cire mata sucurity da yake kai…..Tana tararrabi da fargaba ta sanya numbar Abbah Abbas din a wayar ta shiga gurin kira gabanta na wani irin fad’uwa ta shiga kiran wayar…..Daf da zata katse aka d’aga! ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya tana jiran taji muryarsa sai kawai taji murya mace mai tafe da iyayi da feleqe! tana fad’in “Waye yake magana.”? Gabanta ya dinga dukan uku uku! wacece wannan? Take tambayar kanta, tasan muryar Halisa kuma tasan muryar Saddiqa Mussadiq Mufida! muryar wannan me maganar ce bata tantance ba, Zuciyarta tayi saurin fad’a mata cewar amaryarsa ce! ji tayi idanunta na neman rufewa! tsabar fargaba! Tayi gum! da bakinta takasa magantuwa tana jin muryar Zainab sai magana takeyi amma uffan ta kasa cewa….Zainab tace” To ikon Allah waye wannan anata magana yana ji yayi shuru tsaki taja ta kashe wayar……Naja’atu ta shiga rarraba idonta a dakin gumi! na tsatstsafo mata! Dr yace.”Ke nake saurare naji kamar an d’aga wayar ana magana kuma baki ce komai ba.
Da sauri ta dawo hankalinta tace”Yi hakuri Dr bari na sake kiran wayar bana ji sosai shiyasa na kasa magana.” Okey kawai yace ya zuba mata ido yana kallonta tamkar zai lasheta…….Zainab hannunta r’ike da wayar ta kama hanyar fita palo inda Abbah Abbas din ke zaune yana hutawa.. tana daf da karasawa inda yake wani kiran ya sake shigowa, a maimakon ta kai masa wayar sai kawai ta d’aga tare da kara wayar a kunnanta da fad’in “Waye yake magana.” Naja’atu ta daure da kyar tace.”Nice.”? Zainab jin miryar mace yasa gabanta faduwa tace”Kece wa.”? Abbah Abbas yayi saurin juyowa yana kallonta jin yanda tayi maganar cikin izzah! da gadara!
‘Bangaran Naja’atu kuwa ji tayi tamkar yarinyar ta soka mata wuqa a kirjinta jin yanda take wani daka mata tsawa kamar uwarta! har ta hasala! sai kuma ta sassauta zuciyarta tace.”Naja’atu.” Zainab tayi shuru tana mamaki! Naja’atu Naja’atu? tasan sunan rad’au! a bakin yaran gidan kuma ta samu cikakken bayani a bakinsu da sauran jama’ar gari tunda dama hausawa nacewa ko haqa rami kayi ka bunne abu to wata rana sai ya fito an ganshi, duk labarin Naja’atu tasan shi daga farko har’karshe sai dai duk yanda take zungurar maigidan kan maganar koda wasa bai ta’ba bata wani labarin da ya dangace shi dashi da Naja’atun ba……..”Oh! nagane to wa kike nema.”?
Naja’atu murmushin takaici tayi Kai tsaye tace”Ina neman mijinki ne idan yana kusa ki basa wayar zanyi magana dashi.” Zainab tace”Okey kada ki damu.” Sai kitt! ta kashe wayar ta nufi inda yake tana wata karairaya ga wani tsadaddan murmushi a fuskarta, zama tayi a kusa dashi tasa hannu a fuskarsa tana shafa gemunsa tare da wasa da karan hancinsa tace”Masoyinta sannu da hutawa.” Kafad’arta ya r’ike hankinsa na kan wayarsa dake hannunta ya kar’ba yana fad’in “Waye ya kira ne.”? Tace” Wata ce aka samu akasi ta kira number ka.” Abbah Abbas bai gamsu da maganarta ba ya ‘kurawa number ido, wayarsa babba ce sosai shiyasa daga ko wane gari ko wace qasa aka kirashi sai ta nuna masa, ganin number daga garin jos ne yasa ya d’an shiga mamaki! Sai kawai ya tsinci kansa da kiran wayar…Lokacin Dr har ya kar’bi wayarsa zai fita kiran ya shigo, da sauri ya dawo da baya ya miqa mata wayar…..Rai a ‘bace! ta daga wayar ta kara a kunnanta tace”Ke! dallah malama! ki bawa mai wayar abarsa mana wai ke amarya sai hauka kikewa mutane mtssw! ki bawa mai waya wayarsa zanyi magana dashi.”
Muryarta ta dinga dukan kunnansa yayi shuru yana sauraranta har sai da ta gama hayaniyar sannan yayi gyaran murya a nutse ya kira sunanta. *”Naja’atu!!!*
Wani irin yarrr! taji tun daga saman kanta har i zuwa tafin ‘kafarta a sanyaye tace”Na’am Abbah Ina wuni.”? Ajiyar zuciya ya sauke da fad’in “Lafiya lau ya kike ya maigidanki.” ? Ya nuna kamar bai san abinda ke faruwa ba.
Kuka tasa masa tace”Abbah bani da lafiya gani a kwance a gadon asibiti likita na bukatar kudi bani dashi bani da wanda zai biya min shine na kira ka ko zaka taimaka min kamar yanda Allah yake taimaka maka.” Jin maganar rashin lafiya yasa ya mayar da abin serious yace.”Baki da lafiya Baki da wanda zai biya miki kudin magani ina mijinki yake.”? Tana kuka tace”Ya sake ni ai.”? Shuru yayi dama abinda yake so kenan yaji daga gareta…Yace.”Yanzu kina ina.”? Cikin shashshekar kuka tace”Ina tare da wata mata mai kirki tana taimakona.” Girgiza kansa yayi yace”To Allah ya sawwaqe! Bani Likitan zamuyi magana dashi.” Tayi saurin miqawa Dr din wayar……..Tana jinsu suna magana da Dr din yana tambayarsa abinda ke damunta Dr yayi masa cikakken bayani sannan ya fad’a masa kudin da ake buqata….Yace Yanzu ya tura masa account number nasa zai sa masa kudin…Sallama sukayi da juna Dr ya kallesu a nutse yace.”To alhmdullhi zaku iya tafiya yanzu.” Mmn Sajida da Mmn Ladi sukace “To mungode.” Da sauri Dr ya fita daga dakin su kuma suka shiga shirye shiryen tafiya gida……