WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 5

 

????WATA TAFIYAR????       Story & Written

                By

         Jiddarh Umar

????????????????????????????????

*????✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????✨*

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

 *“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“????`* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~????????~~~~~~~

PAID BOOK

                  Free Page    

               05

Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank, 

Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.

Ko Katin Waya.

 Su na isa gidan da sauri Habu ya zo ya buɗe mai ƙofar mota,cikin isa da gadara haɗe da farin ciki irin na wanda ya hango nasaran shi ko cikar burin shi,kai tsaye cikin gidan ya shiga, da matar Uncle Ahmad din ya fara haɗuwa wacce ke zaune a falo su na kallo ita da yarta,gaida ita ya yi,cikin sakin fuska ta amsa”yaushe ka dawo garin Haris”

“Yau kwana huɗu kenan Anty”

ƴar budurwar ce cikin yanga ta ce “Yaya Haris ina wuni”

“Lafiya,Sumaiya”

Ganin kamar zasu bata ma shi lokaci ne yasa ya katse su da sauri ta hanyar tambayar su”ina Uncle? 

“Yana ɗakin shi”

“Ok Sumaiya yi mai magana ina jiran shi a falo”ya juya ya shiga ta wani ƙofa,

Bai ɗauki  lokaci ba sai gashi ya shigo da ɗan fara’ar shi” da fatan ban saka magajin gobe jira ba? 

Ɗan murmushi ya yi, na jin daɗin sunan da ya kira shi da shi “A’a Uncle,sai dai na zo maka da kyakkyawar labari,wanda dai-dai ya ke da canza rayuwar ka gaba  ɗaya,bama kai kadai ba har da mu gaba ɗaya”

Dan zaro ya yi bakin shi har wani rawa ya ke “wani irin labari ne wannan? 

Ganin yanda ya ruɗe  yasa har saida ya ɗan dara” Uncle na samu matar Aure,kuma irin wacce kake so kuma kake fata”

Hamdala ya shiga yi yana dariyar farin ciki “kai gaskiya naji daɗi sosai Haris,Allah ya maka Albarka,to yanzun faɗa min yarinyar ƴar ina ce,wa ye Baban ta”

“Ni bansan Baban ta ba,na sai san yayan shi ne direban daya kawo ni gidan nan”

“Kana nufin ƴar talaka ce”

“Umm, ko akwai matsala ne? 

” A’a hakan ma ya yi, to yanzun yaushe kake son komai ya kasance? 

“Uncle ni bani da matsala,duk sanda kuka shirya”

Dariya ya yi “wani irin shiri,ai ba batun wani jira yanzun,zuwa gobe zamu tattauna da saura Uncles din,dan Insha Allah bama son abun ya wuce nan da wata ɗaya in ma ansa da nisa”

“Uncle har wata daya! Bai yi yawa ba kuwa? 

Dariya ya yi” Haba Haris wani irin yauwa kuma ”

Yamutse fuska ya yi “wallahi uncle na matsu ne”

Murmushi ya yi “Haris kenan ai duk matsuwar ka baka kai ni ba”

“Uncle ke nan, a dai bar kaza cikin gashin ta” daganan suka ci gaba da tattaunawa.

Ko da ta isa gida, yawancin mutanen gidan duk suna tsakar gida, yayin da Nanne ke zaune saman kujera sai kuka take rusawa,akan ita dai a je a nemo mata Asma’u in ba haka ba zata da kanta ta nemi ta,ganin yanda ta tashi hankulan su ne,yasa Baba Mudansir ya fara kiran yaran gidan samari masu aiki wadanda suka fita aiki yana faɗa masu duk abin da suke su bar shi su tafi niman Asma’u,har zuwa lokacin da Habu babban ɗan Baba Mudansir din ya kira akan ga Asma’u nan dawowa dan ya riga ya sauke ta a juction,nan ya faɗa ma Nanne amma bata yarda ba dan gani take kamar wani abin ne ya kara faruwa da Asma’u amma suke ɓoye mata,ganin shiguwar ta ne yasa suka bata hanya har gaban Nanne ta tsuguna sannan ta kira sunan ta a hankali “Nanne na dawo”

Jin maryan ta yasa da sauri ta juyo tana rike hannu ta”Fettel ina kika shiga,gaba ɗaya kin ta da mana hankali”shiru ta yi ba tace komai ba, tana mai matukar tausayin Kakar su,wannan wani irin so ne haka Nenne ke nuna mata,a yanda ta samu labarin irin son da Nanne ke ma mahaifiyarta wacce tsayin wannan shekaron ba a san inda take ba shi ya dawo kanta,domin ta dauki wani irin so ne ta Daura shi akan Asma’u wanda hakan ne ya kara jawo mata bakin jini wurin matan kawonnan ta,sai mace daya Inna Saude,wacce ta ke ƙawa ce a wurin mahaifiyarta kuma uwa ce a wurin ta,maganar Baba Ɗan Nanne ne ya katse mata tunani”ke Asma’u taimaka mata ta koma shiyanta tunda Allah yayi kin dawo”

“To Baba” ɗaga Nanne ta yi ta taimaka mata har shiyanta,zaunar da ita ta yi saman kushi yayin da ita kuma ta zauna a ƙasa tana rike da hannun ta”ki yi haƙuri Nanne,na sa  ki a damuwa,dan Allah ki yafe min”

“Ba komai Fettel,kawai dai na damu ne saboda nasan yanayin da kike ciki,amma dan Allah karki ƙara yin haka”

“Zan kiyaye Nanne” dan shiru suka yi dukkan su,sai zuwa can kuma tace”Nanne in tambaya ki”

“Ina jinki Fettel”

Dukar da kai ta yi,alamun tana tattauna abin da zata faɗa”Nanne da gaske Mamana bata so na,kuma da gaske guduwa ta yi ta barni anan? 

Shuru tsohuwa Nanne ta yi tana kallon ta,dan bata yi tsammanin wannan tambayar daga bakin ta ba. 

Dan matse hannunta ta yi kaɗan “dan Allah Nanne ki faɗa min,a kowani lokaci  gani nake kamar zata dawo,kowace safiya ta shi nake da yakinin zan ganta wata rana harma ta rungume ni kamar dai yanda ko wace uwa ke ma yarta,a duk lokacin da na kalle ki da niyar tambayar ki game da ita sai in ji na kasa saboda tausayin ki,a matsayin ki na uwa kin rasa ƴa tsayin waɗannan shekarun, yayin da ni kuma na rasa uwa,ban sani ba ko muna da zabon haɗuwa da ita wata rana, ko kuma a labari ta ne kawai zansan wacece ita, kila wannan ciyon nawa shi ne zai yi silar rayuwa ta,mutane da yawa suna min kallon wacce aka gudu aka bari,dan Allah Nanne ki sanar da ni gaskiyar lamari,gaba ɗaya dangin Baba na su biyu ne a garin nan,sai Iyalansu da suka tara,shin ina shima Baba na ya tafi,ina sauran dangin shi, ko dai tare suka gudu da Mama na?ta ƙarasa fada tana mai zubar da hawaye masu zafi,wanda ke fita tun daga ƙasan zuciyar ta.

Hawayen idonta ta share”ba zaki mutu ba Fettel,insha Allah ba abin da zai faru dake,kuma ina mai fatan wata rana ki haɗu da iyayanki,a lokacin ko ina raye ko bana raye,ki faɗa  ma Mahaifiyar ki cewa,ni Nanne ina Alfahari da ita, kuma ita din abin Alfahari na ce har izuwa numfashi na na ƙarshe kuma na yafe mata duniya da lahira,idan kuma Allah ya yi zamu haɗu to a lokacin zan rungume ta ne a kafaɗana na faɗa mata haka da baƙi na,”dan shiru ta yi tana haɗiye wani abu mai ƙauri da ɗaci da ya tsaya mata a makogwaro,tare da share hawayen ta,ci gaba ta yi da magana”Fettel!! Mahaifiyar ki mutuniyar kirki ce,ƴa ce ta gari wacce ko wani mahaifi zai yi alfahari da ita,kamar dai mu,ita kadai ce mace a wurin mu,sai sauran yara na maza guda huɗu,wani gagarimin matsala aka tsamu a wurin aikin mahaifin ki,wanda shi ne sanadiyar komai da ya faru a waccen ranar da ba zan taba mancewa da ita ba a rayuwa ta,domin ta yi tsilar faruwar abubuwa da yawa,kamar dai rasa rayukan mutane da kuma dukiyar su,innalillahi wa innailaihi rajiun,Fettel bana son tuna abin da ya faru,amma dai abin da zan faɗa ma ki shi ne  kawai,a ranar ina zaune a daki na ina ninke kaya na,sai kawai gana fadowar mutum daki na wanda sai da naji tsoro, kasancewar bayan sallar Magariba ne, yawancin mutane basu dawo daga masallaci ba,ina dubawa naga mahaifiyar ki ci,da sauri na tare ta jikina,ganin yanda jikinta ke rawa wanda daga dukkan alamu ba lafiya ba,a lokacin duk baki wuce kwana biyar da haihuwa ba,dan ko suna ba a maki ba, anan take shaida min duk abin da ke faruwa tana kuka sosai,yayin da ta mika min ke a cikin sabon zani,tana mai cewa”Nanne ga ƴa ta nan,ban san ko zan rayuba balle in yi fatan ganin ta,amma ina da yakinin duk rintsi idan Allah yayi muna da sauran rayuwa wata rana zan dawo gare ku,amma idan ban dawo ba ina niman gafaran ki Nanne,ki kula da ita kamar dai yanda kika kula da ni”daga haka ne ta rungume ne muna kuka,jin kamar hayaniyar mutane na ƙoƙarin shigowa ne yasa muka ƙara rudewa ni da ita,ta ƙofar baya na bude mata ta wuce yayinda tana gudu tana juyowa tana waigenmu ni da ke,,har izuwa lokacin da tayi juyawa na karshe wanda bata ƙara yuwowa ba har ila yau!! a lokacin ban san ko tare da Baban ki suka tafi ba,dan bayan kwana biyu aka samar da ɓacewar mahaifin ki,wanda aka ni ma sama da ƙasa aka rasa, iya abin da na sani kenan, wannan dalilin ne yasa,bayan zagayowar wani satin na sa aka maida maki sunan mahaifiyarki wato ASMA’U,wannan dalilin ne yasa na ke  kiran ki da FETTEL,wato Asma’u ƙarama”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button