MADADI Page 71 to 80

*_Allah yasa cikin ya zube Aunty Binta ci kuma!!! ????????♀️ dan Allah kada ta haihu da Bash Aunty Binta wannan pege d’in ya bani haushi????……Wato kuna so rabo ya kashe ni ko? ???? To Yanda Allah ya saukar da ikonsa a kan Naja’atu nima ‘yar kallo da addua ce……..Alhamdullhi saqona na cikin littafin nan ya soma isa, ha’kika wani baya ta’ba haihuwar d’an wani Allah ya qaddarta akwai rabo mai zafi a tsakanin Bash da Naja’atu shiyasa suka rabu da Abbah Abbas cikin ‘kan’kani lokaci ta auri Bash shima suka rabu cin ‘kan’kanin lokaci bayan ya saukar da ikonsa a kansu, babu wani wanda yasan gaibu sai Allah????????*
*Littafin na kudi ne….!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake Vip group #600 normal group #300 account….0542382124….Binta umar gtbank…..Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
****61 Abbah Abbas shuru yayi da wayar a hannunsa yana tunanin maganar da dr ya fad’a masa, Naja’atu na dauke da cikin wannan lalataccen yaron! hakika wannan al’amarin ya tsaya masa a rai mutuka, ba wai yana kishi ne da faruwar hakan ba yasan Allah ba yanda baya tsara al’amarinsa, yarinyar kawai yake tausayawa had’uwar jininsu da yaron da duniya tasan mutumin banza ne, koda yake Ubangiji kan saukar da shiriya akan bayinsa a lokacin da yaso, wannan dalilin ya sanya yaji zuciyarsa tayi sanyi sai kawai yayi addua a kam Allah ya shiryi Bash din ita kuma Naja’atun Allah ya sauketa lafiya ya sanya rabuwar auranta da Bash din shine alkairi……Zainab kuwa kunya ce ta isheta tana jin tsoron kada ya tuhumeta a kan me yasa tayi masa karya bayan ta gane Naja’atu ce ta kira wayarsa, sai taga gabad’aya ma hankalinsa da tunaninsa bayan kanta yana can wani tunani na daban.
Sai goma shaura na dare suka isa gida, Mmn Ladi kai tsaye gidanta ta wuce saboda tasan mijinta ya dawo kuma bata fad’a masa zata fita ba tunda bata da waya, yanzu babu laifi sun shirya sun daina fada sosai duk a sakamakon nasihar da Naja’atu tayi mata……Mmn Sajida ganin mutane sun cika rumfar kwanon siyar da abincinta yasa ta sallamesu da fadin yau babu abinci sai gobe idan Allah ya nufa……Dantalle ya nufo inda suke ya sha shaddarsa ‘yar rini hannunsa rike da mukkulin lifan d’insa, yana washe baki yace.”Mmn Sajida dama wannan qanwar taki tana nan.”? Mmn Sajida tace”Eh tana nan Dantalle ya gida ya iyali.”? Ya amsa idanunsa a tsaye a kan Naja’atu.” Yace.” ‘Yan mata ya kike ya gari ya jin dadi.”? Naja’atu duk da halin ciwon da take ciki sai da ya bata dariya, wai shi dole sai ya burgeta ta lura mutumin yana so ya wuce gona da iri….Tace”Lafiya lau jin dadi na gurinku.”‘ Dantalle dadi ya isheshi ya kalli Mmn Sajida yace yau babu abinci naga alamar ma kamar daga unguwa kuka dawo ko.”? Mmn sajida tace wallahi kuwa munje wani guri ne.” Yace.”To bbu laifi bari naje na dawo kada ku rufe gida da wuri.” Mmn Sajida tace”To shikkenan.” Ya juya da sauri ya nufi inda lifan dinsa yake…..Su kuma suka shiga gidan Mmn Sajida na fad’in “Wahalalle kawai ya fito ya bar iyalinsa yana biye biyen gidajen abinci gabad’aya Dantalle baiyi ba wallahi.” Naja’atu murmushi tayi tace.”Ni kam gani nayi ma kamar sonki yake.” Mmn Sajida na kokarin bude dakinta tace”Ai ko maza sun kare a duniya ba zan auri dantalle ba Gwara nayi ta zama a haka.”
Walid da Sajida tuntuni sunyi bacci da yake Walid nada wayo shine yayi musu shimfida ya daura musu net suka kwanta, ita kuma Mmn Sajida kicin ta nufa da sauri da yake tana da karamin gas sai ta fara kokarin d’ora ruwa ta dafa musu indomee sai kawai sukaji sallamar Dantalle daga waje….Mmn Sajida tace”Naja’atu gashi can ya dawo ko zaki ‘kokarta kije kiji dame yazo.” Naja’atu tace”Rabani da wannan guy Mmn Sajida ki daure dai kije kada yace an masa wulakanci.” Mmn Sajida ta dauki mayafinta ta fita….Minti biyar sai gata ta shigo hannunta rike da manya manyan ledoji Dantalle yaje ya kashe musu kudi gurin siyayyar kayan ciye ciye gami da kayan masarufi.” Sosai Naja’atu ta dinga mamakin siyayyar tafi ta dubu biyar haka kawai bai ka gidansa ba yazo yana bawa duniya kai Allah ya shiryi mazan dakewa iyalinsu mugunta suna bayarwa a waje….Mmn Sajida tace”Kadan kika gani in dai Dantalle ne kuma wannan hidimar da yake yi da biyu yake wallahi ko shakka bana yi saboda dake yake yi.
Naja’atu ta shiga girgiza kanta tana mamakin al’amarin wasu mazan……..To Sai da suka zo kwanciya Mmn Sajida take tambayarta dazu da wa tayi a waya a asibiti…Naja’atu kai tsaye tace mahaifinta ne anan Mmn Sajida tace na fada miki dama suma iyayen naki suna can hankalinsu a tashe dan Allah kiyi hakuri ki koma garesu ko kya samu nutsuwar zuciyarki idan kina zaune a gurina lalattatun maza irinsu Dantalle zasuyi ta kawo miki farmaki.” Tace”Mmn Sajida insha Allah zan tafi gida amma sai jikina ya warware tukkuna.” Mmn Sajida tace to Ubangiji Allah ya baki lafiya mai amfani kuma ya rabaki da abinda ke cikin ki lafiya.”
Bayan wata biyu cikin Naja’atu yayi wata hudu da ‘yan kwanaki….A lokacin ne Allah ya azurta Zainab da samun nata cikin, murna a gurinta tamkar me! shima Abbah Abbas din sosai ya nuna farin cikinsa a kan karuwar daya samu, ya shiga lalla’bata gami da nuna mata so da kulawa, yarinyar ta samu sake sosai sai abinda take so takeyi a gidan……Halisa ta sake shiga cikin wani irin hali na tashin hankali da damuwa dan duk irin kokarin sauke hakkinta da maigidan yake yi gani take kamar baya adalci a tsakaninsu tana gani tamkar yafi fifita Zainab din a kanta lokaci guda tayi wata iriyar rama mara kyawun gani…..Zainab mai wayo gami da so ta siye zuciyar mijinta ai tuni ta janye yaran sun koma bangaranta yanzu komai nasu na gurinta haka take kulawa dasu gami da sanyasu farin ciki, tuni yaran suka manta da wata Naja’atu saboda sun samu wacce ta maye musu gurbinta sai dai sa’i da lokaci Mussadiq yana tunawa da ita…….Ranar wata Alhamis da yamma Yaya Ramlatu ta dira a gidan, kai tsaye bangaran Halisa ta nufa, ta zauna suna gaisawa! Halisa tace”Yaya Ramlatu sai yau aka tuna dani.”? Ta’be bakinta tayi tace”Halisa kenan ai lamarin ki ne yake bani haushi wallahi dubeki dan Allah duk kin lalace yarinya qarama tazo ta kwace miki miji da gida da yara kin kyaleta ba zaki dauki mataki ba.”
Halisa tayi shuru tana nazarin maganar Tace”Yaya kenan ni yanzu ba tashin hankali ne a gabana ba ingantuwar lafiyata kawai nake bukata.” Ramaltu ta ta’be bakinta tace” ai shikkenan tunda kin mayar da kanki sususu!! ni kinga tafiyata.” Sai kawai ta miqe ta kama hanya ta futa.
Tana fitowa ta durfafi bangaran Zainab, lokacin suna zaune ita da yara a palo suna kallo suna wasa da dariya! Kawai sai ganin mace tayi ta shigo mata babu sallama……Yaran duk sukayi tsuru-tsuru murya na rawa suka shiga gaisheta! Ramlatu ta samu guri ta zauna tana muzurai sai bin palon da kallo take tana watsawa Zainab kallon banza…..Zainab dama a ciki take da matar domin ta tsani d’abiar da take mata kamar ba babba ba sai ta dinga shigo mata babu sallama…sai kawai ta dauke kanta taqi kallonta ballantana ma ta gaisheta.