MADADI 1-END

MADADI Page 71 to 80

Yaya Ramlatu ta fusata! sosai ! tace”Ke baki san matsayina bane da ba zaki gaisheni ki bani girma ba.”? Wani irin kallo Zainab tayi mata tace”Nasan matsayin ki mana kina so nayi miki sujjada ne.”?

Ya Ramlatu tace”Ko baki yi min sujjada ba ai sai ki mutuntani a matsayina na yayar mijinki.” Zainab ta ta’be bakinta tare da dauke kanta….Wannan abun da tayi ya fusata Yaya Ramlatu mutuka, sai kawai ta shiga zaginta tana fad’in “Ita bata daukar raini wallahi idan tace rashin kunya za tayi  mata sai taci mutuncinta.

Zainab tace”Kinga dan Allah ki tashi ki fice min a gida ni ban gayyatoki ba haka kawai kizo kina min masifa me nayi miki kike zagin iyayena to bari kiji ni ba Naja’atu da kuka raina bace nasan daraja da mutuncin iyayena.” Ya Ramlatu ta miqe ta iska inda take tana zaginta hade da dungure mata kai tace.”Za kici ubanki zanyi maganin…..Kafin ta qarasa yarinyar ta miqe a fusace! ta wanke ta da mari! Tace”Wallahi ba zanji kunyar cin mutuncinki ba mutukar zaki ta’ba martabar iyayena.

Yaya Ramltu ta dafe kumatunta jikinta na wani irin tsuma mamaki da al’ajabi kamar ya kasheta  ‘yar qaramar yarinya da bata wuce jikarta ba itace ta mareta! Sai kawai ta rufe ta da duka ta ko’ina! Zainab ta dinga ihu! tana kokarin kwatar kanta Ramlatu ta haye kanta sai jibga take…..A kid’ime! Saddiqa taje ta fad’awa Halisa halin da ake ciki sai gata sun shigo ita da Baba Larai! gabadayansu sun firgita da ganin duk da Ramlatu takewa Zainab! da kyar suka janyeta sai haki take tana fad’in “Tunda take a duniya babu wanda ya ta’ba marinta sai yarinyar na saboda haka sai ta dauki tsatstsauran mataki a kanta…Baba Larai ta bude bakinta za tayi magana ta buga mata tsawa da fadin tayi mata shuru bata son munuafurci. Yafan mayafinta ta gyara ta dauki jakarta ta kama hanyar fita sai zage zage take…

Halisa ma juyawa tayi ta nufi gurinta uffan ba tace ba dama itama haushin zainab din take ji shiyasa taji  dadin dukan da Ramlatu tayi mata

Baba Larai ta taimaka mata ta tashi zaune tana kuka kamar ranta zai fita Baba larai ta rarrasheta gami da yi mata nasiha  akan ta zauna lafiya sannan ta fita daga sabgar Ramlatu tunda ba mutunci ne da ita ba, Zainab jinta kawai takeyi saboda haka tana fita ta dauki wayarta ta kira mijinta tana wani irin kuka ta shiga zayyane masa abinda ke faruwa tace tana kwance ta kasa tashi cikinta sai ciwo yake…..Wannan al’amarin ya daga masa hankali sosai ashe Ramlatu ba zata kyaleshi ya huta ba! Dama yana jin haushin abinda tayi masa a kan Halisa kawai ya kyaleta ne, to yanzu kuma shine taje har gidansa ta daki matarsa da ‘karamin ciki a jikinta wannan karan zai dauki mataki a kanta….Kasuwar ya bari ya nufi gidan, ya dauki Zainab sukaje asibiti aka dubata sosai komai lafiya ya dawo da ita gida  tare da tarin siye siyen da yayi mata a hanya, yarinyar sai narkewa take tana kuka gami da riqe cikinta ya dinga rarrashinta yana bata hakuri da kyar ta barshi ya koma kasuwa…………Koda ya tashi daga kasuwa, wani jami’in ‘Dan sanda yaje ya dauko a motarsa suka nufi gidan Ramlatu dake tudun wuzurci…Tana zaune a tsakar gida tana gyara kayan miya,  yaro ya shigo yace.”Wai Ramlatu tazo su gaisa da dan uwanta yana waje. duk a tunaninta Alhassan ne saboda sa’i da lokaci yakan kawo mata ziyara, ta yafa mayafi ta fita, sai ganin Abbas tayi da dan sanda! jikinta a sanyaye take kallonsa yayi bala’in shan kunu tare da umartar d’ansandan ya daure mata hannu! Kuka ta fashe dashi taje “Abbas ni zaka tozarta a kan matarka.”? Ko kallonta baiyi ba ya sake Umartar dansandan da maganar, Yaya Ramlatu ta juyo da sauri zata shiga gidanta shi kuma police din nan ya kama hannunta ta baya yasa mata takunkumi! Yara suka cika a gurin Sakina kishiyarta ta fito tana tambayar ba’asi! Abbah kuwa yana ganin an soma taruwa a gurin ya shiga mota ya sauke glass din motarsa mai duhu yana hango artabun da police din keyi da ita taqi sai turjewa take tana kuka da fad’in ” Dan uwana ne fa matarsa ce tasa yazo yaci mutuncina wallahi banyi laifin komai ba.” Jama’a sai kace kace ake a gurin  ya cika sosai….Abbah Abbas Yana kokarin jan motarsa ya bar gurun Salim yayi parking din motarsa ganin abinda ke faruwa yasa hankalinsa ya tashi  har ya nufi inda mahaifiyarsa take Abbah ya dan sauke glass din motar ya kirashi…Da sauri ya karaso gurin yana risinawa! Abbah yace.”Ina fatan ka kammala ayyukan dana sanya ka kafin barowa ta kasuwa.”? Yace.”Eh Kawu na had’a komai kamar yanda kace!.” Yace.”Okey jeka ce da wancan D’an sandan nace ya kwance mata abinda ya daura mata a hannu.” Salim yace.”Kawu wai meke faruwa ne.”? Yana kokarin kunna motarsa domin  barin gurin yace kaje ka tambayeta zata fada maka.” Kawai yaja motarsa da sauri ya bar gurin ba tare da mutane sun farga dashi ba

Yaya Ramlatu ta muzanta mutu’ka kafin police din ya kwance mata hannunta ya qara gaba abunsa ita kuwa yara ne suka kewayeta suna surutai a kanta gami da qananun maganganu! Salim jikinsa a sanyaye yaja hannunta tana wani irin kuka na tsantsar kunya da takaicin tozarcin da dan uwanta yayi mata cikin unguwa a kan titi tunda gidan nata a kan titi yake shiyasa jamaa yara da manya suka cika gurin cikin gidan suka shiga ita da Salim rayukansu a  mugun ‘bace…..’Karya da gaskiya Ramlatu ta shiga fad’awa ‘Danta tana kuka da fad’in ”Yana da kyau ya dauki mataki kan irin tozarcin da Dan uwan nata yayi mata, Salim ya fusata sosai bai ta’ba jin tsanar Kawun nasa ba sai ranar ko lokacin da ya auri naja’atu bai ji haushinsa ba kamar yanzu yace.”Kiyi hakuri Mama nagane abinda yasa mutumin nan yake miki wulakanci saboda Allah ya fifitashi a kanku yana da kudi yana da iko shiyasa duk wulakancinsa yake qarewa a kanki to insha Allah sai nayi miki maganinsa sai kinji mummunan labari wallahi sai na daukar miki fansar tozarcin da yayi miki a unguwa.” Ramlatu jin furucin da yaron nata yayi yasa ta tsagaita da kukan da take tana qara tunzura masa zuciya a kan yabi ta qarqashin qasa ya   tagayyara Dan uwan nata

‘Bangaran Naja’atu sai dai godiyar Allah dan wannan cikin na jikinta da alama lafiyyye ne ya hanata sakat! kullum cikin ciye ciye  kwadayi iri iri idan ba taci kaza mai kuli kuli ba ji take tamkar zata mutu! al’amarin ya dinga bawa Mmn Sajida tsoro wannan wane irin d’an gayun ciki ne, duk kokarinta sai da ta gaza domin yau da gobe kayan Allah ne kuma tana jin tsoron saka Dantalle cikin harkar sabida kada ya nemi ya fanshe hidimarsa ta rasa bakin magana…..Kawai sai ta shirya da sassafe tayi mata sallama tace zata je wani guri! Asibiti ta nufa, cikin ikon Allah kuwa ta hadu da Dr shima shigowarsa kenan, suka gaisa a mutunce kafin ta tambayeshi bukatar da ta kawo ta, Dr yace to Allah yasa bangoge numbar ba bari na duba dai.” Tace”To Allah yasa dai baka goge ba.

Ya jima yana dube dube a wayar tasa kafin yace.”Alhamdullhi kinga number nan. Ajiyar zuciya ta sauke tace to dan Allah rubuta min a takarda bani da waya wallahi.” Biro ya ciro a gaban aljihunsa ya bude wallet dinsa ya dan yagi  jikin wata takarda ya rubuta mata number a gurguje ya mika mata ya wuce cikin asibitin….Tana murna ta fita daga cikin asibitin ta danyi tafiya kadan ta samu masu communication tace”Dan Allah zanyi waya ta minti biyar ko goma nawa zan biya.”? Guy yace.”Kawo naira dari.” Ta bashi kudin had’e da miqa masa number yasa a wayar tana fara ringing ya miqa mata  gurin ta bari ta samu inda babu mutane……Abbah Abbas na kokarin shiga toilet domin yin wanka yaji kira a shigo wayarsa dawowa yayi ya dauki wayar yana duba number, ganin sabuwar number daga Jos yasa yayi saurin dagawa tare da yin sallama….Mmn Sajida ta gaishi a nutse ya amsa yana tambayarta wacece ita, tace”Alhaji ni sunana Safiyya ina zaune a jos  nice kuma wacce Naja’atu take zaune a gurinta dama na kira kane domin na fad’a maka halin da take ciki! Alhaji Naja’atu tana cikin halin taimako ga cikinta kullum sai qara girma yake  a matsayinku na iyayenta yana da kyau kuyi hakuri ku gafarceta akan sa’ba muku da tayi ku dubi halin da take ciki kuzo ku dauketa dan nayi nayi da ita akan ta dawo gareku ta’ki! wannan dalilin yasa nace bari na kira ku a waya na fad’a muku halin da take ciki sabida bana so har lokacin haihuwarta yazo bata gaban iyayenta”……..Ajiyar zuciya ya sauke  bayan ya gama jin bayaninta yace.”Sannu da kokari Safiyya Allah ya baki ladan taimakon da kikayi akan yarinyar nan kuma naji dadi sosai da kikayi tunanin sanar damu halin da ake ciki Allah ya saka miki da alkairi  mungode sosai Insha Allah cikin satin nan zan turo da mota a dauketa watakila ma ni da kaina zanzo Okey dik dai yanda tayi wu zaki bani cikakken address din inda kuke.” Tace”To shikkenan Alhaji insha Allah yanzu zan turo maka  text za kaga address d’in idan ma baka gane ba kana shigowa unguwar sai ka tambayi Mmn Sajida mai abincin siyarwa insha Allah za’a nuna maka.” Yace.”To masha Allah mungode kwarai.” Sallama sukayi da juna Mmn Sajida tayi saurin tura masa text din ta mikawa mai wayar, ya duba balance da sauri yace sai kin ciko talatin kin qara minti uku akai.” Hamsin ta mika masa ya dauka ya bata sanjinta tayi saurin tarar Napep ta shiga domin komawa gida.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button