MADADI 1-END

MADADI Page 71 to 80

Shi kuwa Abbah Abbas bayan gama wayarsu da Mmn Sajida sai ya yanke shawara kancewa idan ya isa kasuwa zai samu abokinsa ya sheda masa fa halin da ake ciki yana ganin kamar alhakin komai yana kansu tunda yarinyar dai tuntuni ta bar hannunsa to kafin ya zartar da wani hukunci dole sai magabanta ta sun sani. Da wannan shawarar ya mi’ke  ya nufi bandaki domin yayi wanka ya fita harkokinsa….

62******Yau tsawon  kwana uku kenan da Abbah Abbas ya sanar da abokinsa  halin da ake ciki dangane da maganar dauko Naja’atu dake can garin   Jos, ya jima  yana ta sauraran yaji  ta bakinsa a kan a’lamarin Amma Abbah Magaji Yaja bakinsa yayi shuru yaqi cewa komai ballantana ya bada goyon bayan ayi tafiyar……..Shi kuma a lokacin gabad’aya hankalinsa ya kasa kwanciya a tsakanin kwanaki ukun kullum da yarinyar yake kwana yake tashi  a cikin ranshi………..Shi kansa ya kanyi mamaki akan mai yasa yarinyar da cikin dake jikinta suka tsaya masa a zuciyarsa?

 To Yau daya isa kasuwar  ko zama bai bari yayi ba ya nufi rumfar abokin nashi………Koda Abbah Magaji ya ganshi sai da yasha jinin jikinsa gaisawa sukayi a tsanake Abbah Abbas yace.”Wai ya ake ciki ne dangane da maganar da nayi maka kwanaki uku da suka wuce ina ta sauraron naji ta bakinka  har yau baka ce komai ba.”

Abbah Magaji yace.”Dan Allah Alhaji Abbas ka cire kanka daga sabgar yarinyar nan wai shin meye ma na damun kanka a kanta yarinyar nan fa kai ta tozarta amma ka kasa dauke kanka daka kanta, bana so aje inda take a yanzu a rabu da ita duniya ta cigaba da koya mata hankali idan taji uwar bari da kafafunta zata dawo gida.

Abbah Abbas ya girgiza kansa yana kallon abokin nasa yace.”Ban tsammaci jin wannan maganar daka bakinka ba wallahi!  wato kana so Ubangiji yayi fushi damu akan rashin yarda da qaddara ko? to inaso ka sani Naja’atu bata isa ta tsarawa kanta rayuwar da take so tayi a duniya ba, komai ya faru da ita dama a rubuce yake daga Allah! Naja’atu ni tayiwa laifi kuma wallahi tuntuni na yafe mata babu wani ‘kulli a zuciyata dangane da ita…..Sannan naji kana maganar damuwa, dole na damu da yarinyar tunda ni yanzu a matsayin uba nake a gurinta, bayan haka kuma  dole dani da kai da duk wani wanda ya shafeta ya damu da ita ya kula da ita saboda juna biyun da take dauke dashi, ina ganin akan wannan ma Ubangiji na iya tuhumar mu.”

Abbah Magaji yace.” To tunda abun ya kasance haka kai kana iya zuwa ka daukota ko ka tura a daukota ni kam ina da uziri kai ko bani da uziri babu inda zanje wallahi.”

Abbah Abbas ya fusata sosai yace.”Ashe haka kake da ri’ko! ? wai shin me yarinyar nan tayi maka me zafi da kake ‘kinta haka gaskiya ka bani mamaki.”!

Abbah Magaji na murmushi yana kallon abokin nasa dake huci! yace.”Laifin da tayi min bai isa yasa na yanke mata irin wannan hukuncin ba, kai tayi wa laifi ni kuma na ara na yafa amma naga kamar kana so ka watsa min ‘kasa a ido.”

Abbah Abbas ya mi’ke yana jan tsaki! da fad’in “Idan kai baka yafe mata ba ni da tayiwa laifin na yafe mata kuma na fasa turawa a daukota da kaina zanje  wallahi dana san wasa za kayi min da hankali da ban sanar maka da maganar ba sai dai kawai ka budi ido kaga yarinyar a gabanka.” Yana kar’e maganarsa ya buge rigarsa ya kama hanyar futa.

Abbah Magaji ya bishi da kallon Mamaki! to irin wannan fusata da abokinsa yayi anya kuwa  ba so yake ya mayar da yarinyar gidansa ba? Girgiza kansa ya shiga yi yana mamakin al’amarin.

Yana tsaye a tsakiyar katuwar rumfar kasuwarsa  yana magana da yaran dake qarqashinsa,  Salim ya shigo gurun…….Abbah Abbas sallamarsu yayi  da fad’in kowa ya koma gurin zamansa…….ya kalli Salim  fuskarsa babu walwala yace “Zan tafi jos bayan azuhur insha Allah komai dare zan dawo ka cigaba da kula kamar yanda ka saba.” Salim yace.”Insha Allah zan kula amma Kawu ina da maganar da nake so muyi da kai.

Abbah ya tsaya tare da  fadin “Wace irin magana ce.” Salim yace dangane da abinda ya faru tsakaninka da Yayarka ina nufin mahaifiyata.” 

Abbah Abbas ya sake tsuke fuskarsa yace.”Okey ta turoka ne kayi min rashin kunya.” Girgixa kansa yayi yace.”Wallahi ba ita bace nine kawai naga dacewar nayi magana  kan hukuncin daka yanke gaskiya Kawu ba zan boye maka ba raina ya baci sosai ba kayi binkice ba ka yanke hukunci cikin ‘bacin rai! Ashe ita aunty Zainab dince ta fara marin ta shine ita kuma ta kasa hakuri ta doketa.”

Abbah shuru yayi yana nazarin maganar, yace kai waye ya fada maka Zainab ta mari mahaifiyarka.”? Yace.”Aunty Halisa da sauran yaran gidan sune suka tabbatar min da maganar….Abbah ya shiga mamaki mutuka ashe Zainab bata da kunya tunda har zata iya futar da hannu ta mari yayarsa gaskiya al’amarin ya bashi mamaki sosai komai zai dauki mataki a kanta……………amma sai yace”Ni a ganina duk laifin na mahaifiyarka ne a matsayinta na babba mai ya kaita zuwa gidan yara! ko shakka bana yi ita ta tunzura zuciyar yarinyar har ta kai ga ta mareta.”

Salim takaici da bakin ciki kamar ya kasheshi ya girgiza kansa tare da fadin”To Allah ya sawwaqe.” Abbah yace.”Abinda za’ace kenan amma al’amarin mata sai su.

To kamar yanda ya fad’awa Salim cewar bayan yayi sallar a zuhur zai dauki hanya hakane ya kasance Abbah Abbas yayi sallama da yaran rumfarsa ya sake jaddadawa Salim ya kula sosai kana ya shiga motarsa ya dauki hanya ba tare da yayiwa abokinsa sallama ba dan har yanzu bai  daina jin ‘bacin rai dangane da abin da ya faru a tsakaninsu

 *Sharrin zuciya gami da kyashi da hassada!*

Salim  bayan fitar Kawun nasa murmushi yayi yana bin katafariyar rumfar dake ciki da kayan maqudan kudi da kallo! girgiza kansa yayi ya nufi wani qaramin daki dake cikin gurin yasa key ya bude a nutse ya shiga ya rufo kofa!….Wata drowar naga ya bud’e kudad’e ne bandir bandir anan suke shiryawa kafin motar banki tazo ta dauka…..Yasa hannu ya dinga dauko dauri dauri! sai da ya d’auki dauri talatin ya mayar da drowar ya rufe, ya samu wata ‘bakar leda mai  girma da ‘kwari! ya loda kudin a ciki ya daure  bakin ledar tamau! mikewa yayi ya fito daga dakin ya mayar dashi ya rufe…..Yana jiran dare yayi ya aiwatar da  abinda ya tsara!

A ‘ka’idar kasuwar kafin magariba kowa ya tashi idan kaga mutum bai rufe rumfarsa ba to yana da baki sun ri’keshi ko kuma yana wani muhimin abu….Kowa ya tashi sai d’ai-d’ai dan har masu gadi sun iso domin fara aikinsu, Salim sai da yaga duhu ya shigo tukkuna ya fito daga cikin wannan dakin hannunsa rike da ledar kudin daya loda….Lokacin sauran yaran Abbahn sun  tafi sai mutum daya, shima da yaga ledar hannun Salim din bai damu ba saboda ya saba ganin irinta wani sa’in Abbah ya kan sanya shi ya rage kudi ya kai masa banki shiyasa koda Abdulhamid yaga wannan ledar kudin bai damu ba…Tare suka rufe rumfar sannan sukayi sallama kowa ya nufi inda motarsa take….Salim yasa ledar kudin a bayan mota yayi saurin zama a mazauninsa ya figi motar yana d’agawa masu gadi hannu……………..’Karfe takwas da rabi na dare Abbah ya sauka a garin jos a daidai lokacin ne kuma al’amarin ya bayyana wata gagarimar wuta mai tafe da ba’kin hayaki ta dinga tashi a cikin katafariyar rumfar Abbah Abbas dake cikin kasuwar……..Tashin hankali kenan! Hankalin masu gadi ya tashi mutuka suka doshi katon gate din daya rufe rumfar suna kokawar ya za’ayi su bude!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button