MADADI Page 71 to 80

Kafin kice kwabo labari ya bazu a gari, tuni masu rumfuna a wajan gurin suka bazamo domin duba dokiyoyinsu…Salim yazo gurin hankalinsa a tashe yana ihu! kamar gaske ya durfafi gate din rumfar da yayi wani irin ja saboda wutar dake cinsa, ihu! yake da wai sai yaje ya bud’e! a take aka rirri’keshi Abbah Magaji da Abbah Alhassan suka janyeshi su kaishi can gefe guda suka ajiye! Kasuwar ta cika da ‘yan a gaji kowa na iya bakin kokarinsa….a takaice dai sai da wuta taci ta cinye komai na cikin rumfar kasuwar Abbah sannan suka samu nasarar tunkarar gate din suka bud’e, nan ma sai da mutane uku suka fad’i suka suma! sakamakon shaqar hayakin da sukayi………Ganin haka yasa jama’a da dama suka tsorata sai kowa yaja da baya haya’ki ba’kikkirinn ya dinga fitowa daga cikin rumfar..
Gidan Mmn Sajida baiyi wa Abbah wahala ba,dan da kansa yaje gidan bayan yayi tambaya a farkon layin wani matashin saurayi ya kwatanta masa, da yake akwai wutar nepa yasa hankulan Mutanan dake gurin ya dauke gurin kallon motar Abbah dake kokarin samun gurin yin parking.
“Alhamdullhi ya furta a fili a nutse ya bud’e murfin motar ya fito, karaf! idanunsa ya sauka kan Naja’atu dake zaune kusa da Mmn Sajida da Plate din abinci a hannunta tana ci, ga wasu zaratan samari a tsaye a kansu da alama abinci zasu siya.
Ya dinga jin wani tsantsar bacin rai da takaici na kokarin fasa masa zuciyarsa, mutum ne shi mai tsananin kishi mussaman a kan abinda yake so, yaushe Naja’atu ta lalace haka? har take zama a kan hanya gaban maza tana cin abinci kamar tunkiya, gaskiya bai ji dadin wannan al’amari ba….Taku d’aya yayi da niyyar isa gurin sai kira ya shigo wayarsa, a nutse ya fito da ita yana dubawa ganin abokinsa ne yasa yaki dagawa, ya cigaba da tafiyarsa yana jin wani kiran na shigowa, dubawa yayi sai yaga Salim ne, sai ya kara wayar a kunnansa tare da yin sallama………..” Innalillahi wa’ina ilaihi raji’un.”!! Wannan kalmar daya ambata itace ta dauki hankulan jama’ar dake gurin, Naja’atu ta miqe zumbur!! tana kallonsa tana so ta tabbatar da shi ne ko ba shi bane!! Jin muryarsa rad’au! na fad’in “Ina fatan wutar ba taci kowa ba.” Salim yace babu wanda taci amma mutum uku sun suma sannan komai dake cikin rumfar ya kone harda kudin da muka shiryasu a cikin drowar.
Yace.”Salim daina maganar kudi da sauran wasu abubuwa wannan duk a duniya na samesu nasan tunda me nema ne ni Allah zai mayar min da gurbin abinda na rasa babban farin ciki na shine wutar bata ci wani ba,nagode Allah da yasa wutar ta tsaya iya kan dukiya bata ta’ba wani ba.
Salim jikinsa ne yayi sanyi baiso yaji haka daga gurinsa ba ya dauka zai gigice koma sitiyarin mota ya k’wace daga hannunsa yayi hatsari! sai kawai yaji shi yana godewa Allah.A sanyaye yace.”To kawu Allah ya mayar maka da alkairi sai ka dawo kenan.? Yace.”Insha Allah gani a inda Naja’atu take kuma komai dare zan dauko hanya tare da ita.” Salim cikin zuciyarsa cewa yayi Allah yasa gurin hanyarka ta dawowa kayi accident kowa ya huta, a zahiri sai yace.”To Allah ya kawo ku lafiya Kawu.” Abbah Abbas ya amsa da amin kafin ya kashe wayarsa…..Yana kallon gabansa yaga Naja’atu a durkushe kasan k’afafunsa tana shashshekar kukan da yayi mugun d’aga masa hankalinsa, damuwarsa a yanzu ganinta da yayi a tsakiyar maza tsakiyar hanya gaban mai abinci ba wai damuwarsa wutar data cinye masa dukiya ba babban damuwarsa wannan hawayen da take zubarwa……….
Share this
[ad_2]