MADADI 1-END

MADADI Page 71 to 80

Murya na rawa tace”Mmn ladi dan Allah ki dinga sawa zuciyarki ruwan sanyi kafin na shigo gidan nan duk naji irin xage zagen kikeyi dan Allah ki daina babu kyau zagin miji da tsiyatashi ko banza kun haihu da juna idan ya lalace zaki fi kowa jin ciwo saboda yayan da kuka haifa tare.

Mmn ladi ta  sauke gwaron numfashi kafin tace”Wallahi naja’atu mutumin nan bashi da mutunci tunda ya aureni yake bani wuya,  gabadaya baya sauke hakkina da yake kansa kin dai zauna kwana biyu kinga irin rayuwar da nakeyi abinci ma da kyar yake bani! da farko na dauka babu ce sai da nayi bunkice na gane cewar yana samun kudi kawai yana bakin cikin ya kawo gida sai dai yaje ya lalatar a waje da daddare kuma ya isheni da jaraba shiyasa na yanke shawara kan cewa duk ranar da ya nemi yayi wani abu dani sai ya biya ni dan ni ba shashar mace bace.”  Naja’atu shuru tayi tana nazarin maganar matar tace”Mmn ladi ki daina wannan maganar dan Allah musulunci bai hallata hakan ba, ki amince da mijinki a duk lokacin daya bukace ki mutukar ba a cikin tsarki kike ba, sannan dan Allah ki daina kama mijinki da kokawa kuna dambe a gaban yara kinga karfin ku ba daya bane kuma kina da ‘ya mace watarana abinda kika aikatawa akan babanta itama shi zata aikatawa mijinta, kuma idan ban manta ba kwanaki naji mmn sajida na yi miki nasiha kan cewar ki dinga hakuri da kad’an! idan ba zaki iya ba to ki kama sa’ana shi kuma ki kyaleshi da halinsa mutukar yana zalintarki sai ubangiji ya saka miki wannan tashin hankalin da kikeyi da masifa ba shine zai kawo miki kwanciyar hankali ba.

Mmn ladi jikinta yayi sanyi jin nasihar da naja’atu tayi mata tace”Shikkenan na’ajatu zanyi kokarin ganin na dauki shawararki amma wallahi abin ne da ciwo ace dari biyu shine kudin cefanan gida ki duba kiga yanda rayuwar nan ta koma komai yayi tsanani!! kuma yanzu da kike maganar na kama sana’a ina naga jarin da zanyi sana’ar dashi.” ? Ajiyar zuciya ta sauke tace”Insha Allahu ni idan na samu yanda nake so zan baki jari ki dinga sana’a domin ki rufawa kanki asiri amma dan Allah ki daina wannan mummunar d’abiar da kikeyi a gidan auranki.” Allah sarki Naja’atu rayuwa ta koya mata hankali wai yau itace takeyi wa wata nasiha…Mmn Ladi tace”To nagode sosai Naja’atu Allah ya saka da alkairi.” Naja’atu na kokarin yin magana mmn Sajida ta shigo gidan ganin naja’atu yasa ta tsaya tana mamaki! murmushi mai ciwo naja’atu tayi tace”kinyi mamakin ganina ko.”? Mmn sajida tace”Wallahi kuwa ai na dauka kin tafi.” Naja’atu a sanyaye tace”Na tafi mummunar qaddara ce ta sake dawo dani.” Mmn sajida ta rike bakinta had’e da fadin wace irin mummar qaddara kuma.”? Mmn Ladi tace”Nima mamakin maganar nake dama yanzu nake shirin tambayarta sai gashi kin shigo.”

Mmn sajida ta zauna kusa da ita tace”Ni wallahi jikina yayi sanyi da jin wannan maganar naja’atu wace irin qaddara ce ta dawo dake garin jos.”? 

Zafafan hawaye ne suka shigo zubowa daga idonta tana kuka mai tsuma zuciya ta shiga basu labarin abinda yake faruwa,  tun daga farkon  al’amarin harkarshe bata ‘boye musu komai ba sai da ta fad’a musu.

 Maman Ladi ta rike baki cikin mamaki gami da al’ajabi tace Ikon Allah “Yanzu  Naja’atu dama  ashe  kece matar da Bash ya aura? mu dai mun samu labarin cewar yayi aure ya auri yar kano kuma bazawara har a gari a kan dinga surutu da yawa mutane na cewa dama sai da yaje inda ba’asan halinsa ba ya nemi aure dan gabad’aya mu nan mun sanshi kuma mun san mummunar sana’arsa ta 419 (damfara) gami da sace sace a manya gurare uwa uba Harkar luwadi da yake yi……..Gaskiya duk wanda yake da hankali ya kuma san waye bash to ba zai dauki ‘yarsa ya aura masa ba dan a zahirin gaskiya bash ba mutumin arziki bane kuma ba mutumin da zakayi fatan ka had’a zuria dashi bane! sai kuma maganar mahaifinsa da kikace ya kulleki a daki  yana neman lalata dake gaskiya nayi mamaki sosai dan a sanin da jamaar gari sukayi masa mutumin kirki ne! to amma babu mamaki Ubangiji ne yayi nufin tona masa asiri watakila ya dad’e yana lalata da ‘ya’yan mutane sai yanxu asirinsa ya tuno gaskiya duniyar nan a bar tsoroce wallahi naja’atu na tausaya miki da tun farko kinzo ki fad’a min halin da ake ciki wallahi da bazan barki ki auri Bash ba(Allah sarki mmn sajida a lokacin da idanun naja’atu suka rufe kome zaki fada mata a kan auranta da bash ba zata dauka ba) Mmn Ladi tace”Ni wallahi abin ne ma yake bani mamaki na rasa abinda zance Allah dai yasa baki da ciki dan shine babbar matsalar a yanzu.

Naja’atu na goge hawaye tace”Bana tsammanin inada ciki mmn ladi ni tunani na yanda zanyi na ku’buta daga hannun wad’annan mugwayen mutanan.”

Mmn Sajida tace”Gaskiya zamanki a tare dasu bai taso ba yana da kyau ki nemawa kanki mafita kije gida ki shedawa iyayenki halin da ake ciki.” 

“Mmn sajida ina jin kunyar tunkarar iyayena da wata magana wallahi mahaifiyata tayi min gargadi kancewar kada na sake nazo gida da wata matsala tunda dai ni naji na gani da auran bash to naje na zauna nayi hakuri…..Mmn Sajida tace” To ai wannan matsalar babbace dole su san da ita idan baso suke ki shiga cikin masifa ba.” Shuru tayi tana kuka gami da tunanin yanda za tayi.

Naja’atu haka ta wuni a gidan mmn sajida suna ta bata sharwarin yanda za tayi da zata tafi mmn sajida ta bata dari biyar hade da soyayyan nama mai uban yawa, har bakin titi suka rakota ta shiga napep su kuma suka juya suna sake tattauna maganar…

Cikin fargaba ta shiga gidan tayi sauri ya shiga gurinsu ta rufe da key sabida har yanzu tsoro takeji kada ‘katon kwarton gidan yasan ta dawo yazo ya afka mata…..Da yake taci abinci ta koshi a gidan mmn sajida bata damu ba sai tayi kwanciyarta tana ta istigifari a cikin zuciyarta.

*ANGO*

‘bangaran Abbah Abbas kuma al’amura suna ta tafiya cikin tsari da kwanciyar hankali maganar auransa da Zainab ta kammala iyayensa da duk wani makusancinsa yasan da maganar, Halisa ta shiga cikin tsantsar tashin hankali da damuwa jin cewa mijin nata zai auri yarinya mafi karancin shekarun Naja’atu sai duk ta raina kanta kullum tana kwance a daki tana nadamar rayuwa……..Duk abinda ake bukata ango yayi Abbah Abbas yayi wa yarinyar sannan itama halisan yayi mata dadai gwargwado duk domin ya kwantar mata da hankalinta….Gidanshi dake ‘Danbare yasa aka sake qawata shi da abubuwan morewa rayuwa da jin dadi! dama bangare uku ne nashi guda na amarya daya na uwargida daya………Kafin zuwan ranar daurin auren da kansa  yaje har gidan Limamin yaga yarinyar masha Allah  ya yaba sosai da ita Zainab mai matsaikacin tsayi da ‘yar qiba amma ba mai muni ba, kuma masha Allah tana da kyau daidai gwargwado dan ba za’a sata a layin munana ba, sai dai yanda yarinyar ta kar’be shi tana nuna masa iyayi da rashin ta ido abin ya bashi mamaki mutuka ya lura da yarinyar na sonsa sosai mussaman yanda take yawan kiran wayarsa a kai a kai da sassafe zata kirashi ta gaisheshi idan rana tayi zata kirashi ta tambayeshi yanayin kasuwa, idan dare yayi kafin ya kwanta sai ta kirasa tayi masa sai da safe! Sai al’amarin ya dinga bashi mamaki mutuka yana mamakin wayo da dubarar yarinyar babu shakka ko cikin mata uku ya ajiyeta zata iya zama dasu saboda tana da wayo da kuma iya mu’amula ba irin Naja’atunsa sarkin rigima da koke koke ba….Yanzu dai komai ya kammala an kuma tsayar da ranar da za’a daura aure juma’a mai zuwa bayan an gabatar da sallar juma’a.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button