MADADI 1-END

MADADI Page 71 to 80

******

Naja’atu daina shiga sashen su mommy tayi har sai da ta tabbatar da cewar maigidan ya gama hutunsa ya tafi sannan ta  cigaba da shiga nan ma idan ta shiga da sun gaisa bata dadewa take fitowa! Munira kuwa dama dawowar mahaifin nasu ne yasa ta  tsahirta da abinda take, yana tafiya kuwa ta cigaba da yawace yawacenta sai taje gidan Muktar tayi sati daya ko biyu acan ba tare da damuwar mahaifiyarta ba……….

bash da abokanan sana’arsa sunyi nasarar shiga wani babban bank sunyi gagarimar sata ta maqudan kudade, dama  duk sanda suka bushi iska haka suke shirya irin wannan ta’addacin saboda sun tanadi matakan kare karansu kome zasuje suyi a guri babu wanda zai gansu sai bayan sunyi sun gama ma’aikatan gurin zasu fahimci akwai matsala haka zasuyi ta binkice daga inda matsalar ta afku  idan sun kasa ganowa sai su hakura……To yau dai Allah ya nuna musu ikonsa idan sunayin abu suna ganin babu wanda yake ganinsu to shi yana ganinsu kuma yau yayi nufin tona musu asiri bayan sun fito daga bank din sun shiga motocinsu lokacin CCTVCAMERA ta tona musu asiri dan wani irin qara ta dinga yi tana nuna akwai babbar matsalar dake faruwa, kafin kace kwabo ma’aikata da jamian tsaro kowa ya ankara sun fito hankali a tashe nan suka hangi motacin su Bash na kokarin fita daga bank din, a guje! jama’an tsaro suka shiga mota suka bi bayansu da harbi! abunka da dare gari yayi shuru sai karar harbi ne ke tashi…..Su bash sun tsorata mutuka dan rana bata ta’ba kwace musu irin yau ba, sai kawai kowa ya shiga kokarin tserar da kansa…Bash tunda ya samu ya sunkuci wata jaka wacce take sha’ke! da kudi yayo fit ya fito daga motar ya nausa cikin daji ya dingi gudu shima yana sakin harbi da bundigarsa….Sauran su ganin matakin da bash ya  dauka dama shine garkuwarsu tunda shine kadai  yake da bindaga, sai kawai suka bude mota suka fito da gudu suna kokarin arcewa! Cikin ikon Allah Allah ya bawa  jami’an tsaro sa’a suka rufar musu, da harbi a take suka fad’i a gurin suna wani irin ihu! da rirrike kafafunsu.

Bash kuwa yana samun nasarar shiga gida sai ya sauke ajiyar zuciya ya sake rike jakar kudin dake hannunsa da kyau, yana wata iriyar tafiya ya nufi bangaransa, maigadi dai binsa da kallo yake dan yanda ya shigo gidan a guje kuma a gigice ya nuna masa cewar akwai babbar matsalar dake faruwa.

Naja’atu na tsaka da bacci ta dinga jin motsi da buge buge a firgice ta mike zaune tana kokarin kunna hasken dakin, Shi ta gani yana ta aikin zazzage kudi yana shiryawa cikin wata akwati mai fadi! A tsorace tace”Bash wannan kudin fa.”?…..”Shiiiii.”! Yayi mata hade da dora yatsansa a saman le’bansa! Naja’atu tayi shuru tana kallonsa gabanta sai buguwa yake babu shakka Bash sata yaje yayo a wani gurin….Tana zaune tana kallonsa ya gama shirya kudin tsaf-tsaf taga ya mike ya bude gurin kayansa ya dauko wasu bakake yasa a jikinsa ya sunkufe kansa da bakar hula ya saka face mark a fuskarsa  hankalinta ya tashi miyau ya qafe a bakinta lokacin da taga yazo ya tsaya a kusa da ita sai da ta kusa sakin fitsari! jajayan idanunsa kawai take kallo, taji yace.”Naja’atu yau  karshen zama dake yazo na sakeki saki uku! inaso ki cireni daga rayuwarki ki manta kinsan Bashir a rayuwarki, burina ya cika na samu kudaden da zasu isheni na qetara qasar waje naje naci karena babu babbaka saboda haka wannan itace magana ta dake ta karshe.”! Yana gama maganarsa ya sunkuci! akwatin  kudinsa ya kama hanyar fita……Cikin wani irin masifaffan yanayi na tashin hankali da razani ta d’aga hannunta hade da kiran sunansa *”BASH!!”* Juyowa yayi ya kalleta yayi wani irin murmushi kafin ya  daga mata yatsun hannunsa biyu ya bude kofar dakin ya fita da gaggawa!

“Innalilihi wa” ina ilaihi raji’un.” Kalmar da ta iya furtawa kenan ta kwanta a gurin tana wani irin kuka na tsantsar tashin hankali gami da nadamar rayuwar da Bash ya jefa kansa a ciki…….Haka ta kasance har asubah! lokacin da take yunkurin mikewa domin daura alwala a lokacin ne kuma ta dinga jin kukan motar jama’an tsoro a cikin gidan….A furgice ta mike tsaye ta nemi zaninta ta daura kan rigar baccinta ta zura hijabinta ta fara kokarin fita, tana fitowa palo suka shigo su kusan bakwai ko wanne hannunsa da bindiga suka shiga rarraba idanunsu a palon!! Hannu tasa ta rufe bakinta jikinta na wani irin karkarwa! Babban cikinsu yace.”Ina Bash yake shi kadai muke nema kada ki firgita.” Saboda tsananin firgicin da take ciki kasa magana tayi ta zube a gurin tana sake qumshe bakinta ji takeyi tamkar ana ragargaza mata gwiwowinta…..Tsawa! mai qarfi ya buga mata ya d’ora mata tsinin bindiga a goshinta yace.”Zaki fada mana inda mijinki yake ko sai na sakar miki bullet.”! Allah sarki Naja’atu fitsari ne ya kwace mata a gurin, cikin wata iriyar magana tace”Ya had’a kayansa ya fice daga gidan tun misalin biyu da rabi ya shigo naga yana hada kudi a kwati da nayi magana yace nayi shuru bayan ya gama ya tsaya a kaina tare da fad’a min hukuncin da ya yanke a kaina ya sake ni saki uku.”

Bakin bindigar ya cire daga kanta yace.”Tashi muje kiyi mana jagora cikin gidan inda iyayensa suke. Ta mike da sauri suka tasa ta a gaba har dakin Mommy wacce take ta sharar baccinta…..Jin tsinin bindiga a saman goshinta yasa ta tashi a firgice tana zazzare ido! ganin jamian tsaro yasa gabanta ya yanke ya fadi! ta kalli naja’atu a tsorace tace”Me yake faruwa ne? naja’atu yanzu sai dai kika tonawa mijinki asiri.”?

Jin wannan magana da tayi yasa babban cikinsu yace.”Ina Bash.”? Ta kalleshi cike da fargaba tace me yayi muku kuke nemansa wallahi matarsa sharri tayi masa.”

Lafiyayyan mari ya kwada mata ya kalli na gefansa hade da umartarsa daya daura mata ankwa! Mommy ta dinga kuka tana musu magiyar su kyaleta da fadin duk zargin da suke akan yaronta ba gaskiya bane…..Yace.”Tunda mun samu labari daga bakin maigadi cewa uban yaron baya gari to ke zamu kama mu daure a madadinsa duk inda yake  idan yaji labarin kina hannunmu zai bayyana kansa dama mun dade muna bunkice a kansa alhamdullhi yau Allah ya bayyana mana shi.” Mommy kuka kawai takeyi tana basu hakuri sunki kulata suka angiza keyarta

Naja’atu kasa motsi tayi jikinta sai rawa yake tana kallo suka sata a cikin motarsu  tana kuka tana kiran sunanta tare da fadin ta taimaka mata, hakika ranar taji tausayin matar sosai da sosai! babu shakka  son zuciyarsu shine ya janyo musu shiga wannan masifar su haifi d’a a cikinsu amma su dinga turashi yana sata ai dama hausawa nacewa duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwan kan doka, tabbas da haihuwar d’a irin Bash to gwara Allah ya barka babu  haihuwa domin hakan shi zai fi maka alkairi a rayuwarka….A sanyaye ta juya domin zuwa taje ta had’a kayanta.

*????Yau akwai Celaberation Vip madadi  ga pege din da kuke ta jira ya iso???? Sai dai kuma akwai sauran qalubale anya kuwa  mutumin naku zai mayar da Naja’atu dakinta kuwa? duba da cewar Allah yayi masa sauyi na Alkairi ina ganin da qyar idan zai waiwayi naja’atu da maganar kome amma dai bari mu gani????*

*Littafin na kudi ne….*

Koda zaki ganshi a groups na  sata ne idan kina da bukatar biyan kudin karatu ga yanda abin yake Vip group #600 normal #300 accont numbar…0542382124…Binta umar gtbank…Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button