MADADI 1-END

MADADI Page 71 to 80

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

57

Wata qaramar akwati mai tayoyi ta samu a dakin, ta kwashe masa tarkacen kayansa da suke ciki  a guruguje ta shirya ‘yan kayanta da basu kala biyar ba ta rufe da sauri ta gyara hijabinta ta dauki akwatin ta kama hanyar fita daga dakin…..Tana fitowa harabar gidan taga dandazon jama’a harda ‘Yan jarida sun cika gidan suna tayi wa maigadi tambayoyi, tsorata tayi dan gabadaya bata so a watsa hotonta a duniya jama’a su ganta su sheda ta a matsayin matar d’an ta’addah! Tana kokarin ratsesu  ta fita daga gidan wani dan jarida yasha gabanta yana yi mata magana tare da kara mata wayarsa a daidai bakinta, rufe fuskarta tayi da hijabinta muryarta na rawa tace”Dan Allah ka matsa ka bani guri na fita ni ban san a binda ke faruwa ba….Dan jaridar yace.”Hajiya a matsayinki na matar Bash wanda ake zarginsa da aikata munanan ayyuka wanda suka sa’ba dokar qasa da kuma dokokin musulunci  muna bukatar jin ta bakin ki dangane da wannan al’amarin da ya faru.” Jin muryar d’an uwansu yana tambayar Naja’atun yasa da sauri sukayi mata caaaa! a kanta kowa na miqa abin daukar rahotonsa a bakinta…….Tana kakkare fuskarta da hijabin ta tace”Na fad’a maka nima ban san komai ba akan wannan al’amarin kuma ka daina dangantani da Bash domin yanzu ba mijina bane.”! Tana maganar suna daukar hotonta had’e da daukar muryarta……..” Duk da haka hajia ba zaki rasa ta cewa ba a kan wannan abun tunda dai a kan idonki komai ya faru.” Da sauri ta dauki akwatinta ta fice daga gidan, kamar mayu suka bi bayanta har wajen gidan suna daukar hotonta…sai da ta qule tukkuna suka koma cikin gidan tare da titsiye maigadi da tambayoyinsu kamar yanda suka saba.

Dari biyar din da Mmn sajida ta bata kwanakin baya da ita tayi kudin mota mai Napep ya ajiye ta har kofar gidan, ta bashi kudinsa da sauri ta shiga gidan tana jan akwatin hannunta.

Mmn Sajida na yanka salak kawai ta ganta ta shigo a firgice!! Mmn Sajida ta ajiye wukar hannunta da sauri ta miqe ta rike ta tana dudduba jikinta had’e da godewa Allah!

Naja’atu rungume ta tayi ta dinga wani irin kuka na tsantsar tausayin kanta…mmn sajida kasa daurewa tayi sai ta shiga tayata kukan tana rarrashinta da kalamai masu sanyi, har sai da ta samu tayi shuru hankalinta ya dawo jikinta tukkuna tace” Naja’atu naji dadin ganinki wallahi dama tun dazu nida mmn ladi muke zancen ki dukkaninmu mun shiga damuwa sakamakon jin abinda ya faru da mijinki mun samu labari cewar jami’an tsaro sun kama mahaifiyarsa  saboda basu samu nasarar kama shi ba sai muke ta fargaba ko sun hada dake sun daure, mun dade da mmn ladi muna tattauna maganar kafin ta shiga gidanta.

Naja’atu na goge hawayen da suka kasa tsayawa tace”Mmn Sajida tunda nake banta’ba shiga masifa  irin ta jiya da yau ba! Allah ne kawai ya nufa ina da sauran kwana a gaba da tuni sai dai kuji mummunan labari ‘Yan sanda sun harbeni.” Mmn Sajida ta rike ha’ba! cike da tu’ajibin al’amarin tace”Haka kawai baki  ji ba baki gani ba su harbe ki sai kace kece kika turashi yaje yayi sata ai naji dadi da suka kama uwar tasa tunda dama sune suke daure masa gindi nasan yanzu ai duk inda labari yake yajewa Alhaji Aminun shima nasan sai sun daureshi kuma insha Allahu asirinsu sai ya tuno.”

Ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kanta tace”Mmn Sajida na tabbata jami’an tsaron nan da basu tarar da mahaifiyarsa a gidan ba to ni zasu kama a madadinsa kinga kuwa dole na shiga tashin hankali wallahi har yanzu ban dawo daidai ba.”Mmn sajida na kokarin yin magana Mmn Ladi ta shigo gidan, ganin Naja’atu a zaune yasa ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah ta zauna suna sake jajanta al’amarin a nan ne Naja’atu ta tabbatar musu da saki ukun da Bash yayi mata.

Mmn Ladi ta dinga tsine masa tana fad’in ” Allah ya rabaki da masifa Naja’atu fatan mu anan shine Allah yasa baki da ciki shikkenan kin rabu da alaqaqai gabad’aya.” Naja’atu tace”Ni sai maganar ciki kike kina fad’ar min da gaba na fad’a miki tun zuwan da nayi kwanakin baya bani da ciki dan Allah ki daina wannan maganar.” Mmn ladi tace”To shikkenan na daina tunda bakya so Allah ya kiyaye gaba.” gabadayansu suka amsa da “ameeen Ya Allah.”

To labarin al’amarin dake faruwa a garin Jos ya zagaya sauran jahohi ta hanyar kafafan sadarwa, kowa sai fad’ar albarkacin bakinsa yake…To Abbah Abbas ma dai a labaran karfe hudu na tashar freedom redio ya saurara lokacin ma yana kasuwa…… Al’amarin ya firgitashi jin mai gabatar da labaran na fadin sunan Alhaji Aminu dan jarida yana sake jajjadawa cewar a cikin masu laifin harda d’ansa mai suna Bashir wanda dubunsa ta cika  a ranar dama kuma tsohon mai laifine wanda ake nemansa ruwa a jallo……Yana tsaka da mamakin al’amarin yaji  sun sako muryarta lokacin da takewa d’an jaridar nan bayani kan ya kyaleta da tambaya ita bata san komai ba……Wani irin gumi ne ya shiga tsatstsafo masa a saman goshinsa Yasa hankici ya goge yana cigaba da sauraran muryar mai labaran….Sai da a ka gama labaran  tsaf! ya samu damar ajiye wayar ya shiga  mamakin al’amarin  ya jima sosai cikin alhini da tunanin wace irin rayuwa yarinyar take ciki kafin ya sauke ajiyar zuciya   daga bisani  yayi furucin alkairi akan abunda ya faru  tare dayiwa wad’anda ake tuhuma da   laifin adduar shiriya, da fatan Allah yasa ‘karshen masifar kenan….Ammafa jin muryar Naja’atu cikin tashin hankali ya tsaya masa a zuciya yana so yayiwa abokinsa magana idan sun tashi daga kasuwa yana tunanin wani abu, zai dai saurara ya gani ko shi abokin nasa zai fara tuntun’barsa da maganar yasan tabbas ya samu labarin abinda ke faruwa da ‘Yar uwar tasa….

Bayan kwana uku al’amura sunyi sauqi Naja’atu ta samu nutsuwa gidan Mmn Sajida sosai take kulawa da ita gami da bata ingantaccen abinci mai kyau tana ci  ta koshi, sannan idan sun ke’be tayi ta rarrashinta gami da nuna mata ta kwantar da hankalinta ta dauka abunda ya faru da ita qaddara ce bayan nan kuma ta shirya fuskantar iyayenta da maganar  domin su san halin da ake ciki…Duk sanda Mmn Sajida tayi mata wannan maganar takan shiga damuwa sosai da sosai, itafa yanzu gabad’aya kunyar had’a ido take da kowa dan idan ta koma gida bata san da wane ido zata kalli mutane dashi ba, auran data qallafa ranta a kansa gashi anyi mata amma wata uku da kwanaki ya wargaje anyi mata saki mafi muni irin wanda Allah baya so,  to ta yaya ma zata iya yi musu bayanin yanda al’amuran suka kasance, kullum da wannan tunanin take kwana da kuma shi take tashi.

Yau dai Mmn Sajida kafin ta fita gurin sana’arta tace”Lallai dole sai ta kira wayar wani mafi kusa da ita ta fad’a masa ga halin da take ciki dan zaman da takeyi bashi da amfani iyayenta basu san halin da take ciki ba.

Gudun ‘bacin ran Mmn Sajidan yasa ta kar’bi wayar tata ta sanya numbar aunty maryam a kai, gabanta na dukan uku uku ta shiga kiran number

Aunty maryam na gidan Alhaji suna ta shirye shiryen daurin aure kasancewar washe garin ranar daurin auren Abokin mijinta shiyasa  ta yini gidan Alhaji suna ta aikace aikacen walimar da angwaye zasuyi bayan daurin aure…….Duk da bata sheda numbar ba hakan bai hanata dagawa ba tayi sallama a nutse tare da fad’in “Da wa nake magana.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button