MADADI Page 71 to 80

Naja’atu tayi wani qwal-qwal! hawaye na kokarin sauko mata sai dai ta daure murya na rawa tace”Anty maryam kina magana da Naja’atu.”
Cike da farin ciki Aunty maryam tace”Naja’atu idonki kenan? ashe kina nan kin ya damu kwana biyu me ya samu wayarki ne sai ayi ta kira bata shiga.”
Murya na rawa tace”Lalacewa tayi.” Tace”Ayya! shiyasa mana to ina fatan dai kina lafiya ya maigidanki.”? Tace”Lafiya anty ya nake jin hayaniya a kusa dake.”
aunty maryam tace”Ina gidan Alhaji wallahi muna aiki Gobe bayan sakkowa daga sallar juma’a Abbah Abbas zai daura aure.” Aunty Maryam bata fad’i maganar da wata manufa ba tsakaninta da Allah ta fadi maganar ba dan ta cuzgunawa naja’atu ba tunda ita a ganinta ai babu wata alaqa a tsakaninsu da zai sanya taji zafi dan zaiyi aure.
Ita kuwa Naja’atu ji tayi tamkar Naja’atu maryam din ta fad’a mata ranar mutuwarta wani irin zazzafan gumi ya shiga yanko mata….Zazzafan kishi! ya turnuqeta! murya na rawa tace”Aunty maryam wace magana naji kina yi waye zaiyi aure ban fahimce ki ba.”?
Aunty maryam ta fuskanci sauyin yanayi a tattare da Naja’atun sai ta sassauta murya tace”Abbah Abbas nake nufi nace dake gobe zai daura aure insha Allahu.”
Kuka ta fashe dashi murya na rawa tace.”Aunty maryam da bakinki kike fad’a min wannan maganar shin kin san halin masifar da nake ciki kuwa.”? Aunty maryam tayi kasaqe da waya a kunnanta jikinta yayi sanyi jin irin kukan da Naja’atun takeyi, tace”Kiyi shuru dan Allah kiyi min bayanin abinda ke faruwa.”
Kai tsaye tace”Aunty Maryam Bash! Yayi min saki uku yau kwana uku da suka wuce.”…..”Innalilihi wa’ina ilahi raji’un! kalmar da aunty maryam ta furta kanan wacce tayi dadai da zuwan hajia gurin tana tambayar ta abinda yake faruwa take furta wannan kalmar………
*Littafin na kudi ne…!*
Koda zaki ganshi a gruopa na sata ne idan kina bukatar biyar kudinn karatu ga yanda abin yake…
Vip gruop#600 normal group#300 account.. 0542382124…Binta umar gtbank…Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
Barkamu da Juma’a My Fans???? Ina rokon Allah ya sadamu da alkairan dake cikinta ????????
58 Hajia Abu ta qaraso inda aunty Maryam take hankali a tashe take tambayarta abinda ke faruwa. Aunty Maryam jiki a sanyaye tace”Naja’atu bari zan kira ki anjima.”Sai kawai ta kashe wayar tana kallon hajian bakinta sai rawa yake yi tsabar fargaba da tashin hankali ya hanata magana, ita ma Hajian jin ta ambaci sunan Naja’atu sai gabanta ya tsananta faduwa ta zauna kusa da ita tare da dafa kafadarta tace”Maryam me yake faruwa da Naja’atu? jikina yana bani akwai mumman abinda ke faruwa da rayuwarta.”Aunty Maryam tayi qasa da kanta tana tunanin yanda zata fad’a mata maganar….Aure wata uku kacal har anyi angama kuma saki har uku dan tsabar wulakanci a ganinta ko wane irin laifi naja’atu tayi bai cancani a wulakantata irin haka ba(Hausawa nacewa ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne) hakika aunty maryam ta tausayawa Naja’atu sosai yarinya da quruciyar ta da komai maza sai katantawa suke da ita, koda yake na farko itace taqi to amma wannan a tunaninta ba daga gurinta bane kawai ta had’u da sharrin d’a namiji….Sai da ta dan samu nutsuwa tukkuna ta d’ago kanta cikin tararrabi da alhini tace”Hajia al’amarin ne babu dadin ji wallahi shiyasa kikaga duk jikina yayi sanyi Naja’atu ce ta kira ni take tabbatar min da cewar wai mijinta ya saketa saki har uku kwana uku da suka wuce.”
Hajia tayi salati tana sanar da Ubangiji tace “A kan me? me tayi masa yayi mata wannan wulakancin saki Uku!!? innalillahi wa’ina ilaihi raji’un! Ai kafin kice kwabo palon ya cika da jama’ar da suke waje mafi akasari ‘yan uwan Alhaji ne da hajian sai kuma Yaya Ramlatu! dukkanisu suka dinga tambayar ba’asin abinda yake faruwa, Aunty Maryam da hajia sukayi shuru domin sirrinta al’amarin, irin wannan maganar ba mai dadin fada bace shiyasa sukayi shuru…..Yaya Ramlatu tayi murmushi tana girgiza kanta tace” Hajia meye abun ‘boye magana nifa dama nasan sai haka ta faru shuru kawai nayi muku ban sanar miki da halin da ake ciki ba, kwana uku da suka wuce na samu labarin abinda ya faru da mijin data aura ashe d’an fashi ne ‘barawo d’an shaye-shaye d’an Luwadi ne manemin mata! ke mutumin daj mugun mai laifi ne jam’ian tsaro sun jima suna nemansa sai a ranar dubunsu ta cika shida abokanan harkarsa sun shiga wani bank sunyi sata sun fito asirinsu ya tuno yanzu dai ‘yan sanda sun samu nasarar kama abokan harkar tasa shi kuma ya tsere amma sun damqe mahaifiyarsa jiya na sake samun labarin cewar sunje har inda mahaifinsa yake sun damqe shi, yanzu dai sun baza binkice sosai dan gano inda yake shima su damqe shi! ai wallahi naso harda ita shegiyar suka damqe dama ai duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa kan doka! makwadaita kawai gashi nan sun dauki ‘yarsu saboda tsabar kwadayi sun aurawa ‘barawo.”
Palon yayi tsit! kowa yana mamaki da salati a cikin zuciyarsa! Yaya Ramlatu ta cigaba tsinewa Baba malam dashi da zuriarsa tana kwashe musu albarka! Hajia da taga abun nata na nema ya wuce gona da iri sai ta tsawatar mata Yaya Ramlatu ta fita daga palon tana cigaba da surutai….Hajia ta sallami kowa tace kowa ya koma ya cigaba da aikinsa.
Shuru palon yayi bayan fitar jama’ar hajia ta kalli anty maryam dake zaune da waya a hannu tace”Sake kiran number data kira ki da ita.” Aunty Maryam ta duba numbar da sauri ta shiga kira… swich up wayar a kashe take! tayi ta kira ana ce mata a kashe take, cike da mamaki tace”Yanzu fa mukayi waya amma duba suna cewa a kashe wayar take.”
A sanyaye hajia tace”To watakila babu chaji a wayar anjima kadan kafin ki tafi sai ki sake gwadawa mugani.” Aunty maryam tace”To shikkenan.
Naja’atu bayan gama wayarsu da aunty maryam kwanciya kawai tayi tana kukan bakin ciki! gami da nadama da dana sani! Hakika tasan duk abinda ya faru da ita itace ta janyowa kanta, gashi yanzu tazo tana dana sani wanda hausawa ke cewa qeya ce! da tasan auran Bash ba zai tsinana mata komai ba data hakura ta zauna a dakin mijinta data san Bash amanarta zai ci to da babu abinda zai sanyata ta fujirewa auran *MADADI* da iyayenta sukayi mata, hakika da tasan Bash ba mutumin kwarai bane to da babu abinda zai saka ta za’be shi a matsayin abokin rayuwarta…Data san ! data san! Data san! (babu wanda yasan gaibu sai Allah kuma komai ya faru da rayuwarki qaddara ce amma kuma akwai son zuciya da qin jin maganar magabata mafi akasari iyaye zasu za’bawa d’ansu abunda yake alkairi ga rayuwarsu sai su kuma ‘Ya’yan fujire su nuna ga abinda suke so, hausawa nacewa abinda babba ya hango yaro ko ya hau bishiyar rimi ba zai hango ba)
Mmn Sajida data gaji da rarrashinta sai kawai ta fita gurin sana’arta ta qyaleta dan al’amarin Naja’atun tana gani kamar yafi karfinta……Mmn Sajida da wayarta ta fita tana so ta bayar a kai mata chaji kasancewar kwana biyu wutar unguwar ta lalace sai ta ajiyeta a kusa da ita ta cigaba da hada hada da jama’a! kawai wani d’an bana bakwai yazo siyan abinci ya dauketa yasa a aljihu a gurguje ya cinye abincinsa ya bar gurun…..Sim card din ya cire ya yar ya qara gaba abinsa.