MADADI Page 71 to 80

Sai bayan jama’a sun tsagaita ta qwalawa Walid kira ya fito daga cikin gidan Mmn Ladi yana amsawa, ta laluba kusa da ita zata dauki wayar taji wayam! tashi tayi tana zazzage jikinta tana dubawa babu waya babu dalilinta, ta dudduba bata ganta ba sai tace”Shiga cikin gida ka tambayi Naja’atu ko wayar ta nan watakila dama ban fito da ita ba.
Yaron ya shiga gidan da sauri ita kuma ta cigaba da abinda take….Minti biyar Walid ya fito yace.”Mama wai tace baki wayar a cikin gidan ba da ita kika fito kika ce zaki bada chaji .”
Mmn Sajida tace”Shikkenan sun sace yau kuma tsautsayin a kan wayata ya afka ai shikkenan Allah ya mayar min da alkairi.” Mutanan dake tsaye a kanta suka shiga jajanta mata, tace”Wallahi ni layina ma nake ji.” Da sauri daya yace”Bani numbar na kira muji.” Da sauri ta shiga fada masa yasa a wayarsa a take aka ce masa wayar a kashe take, ya dinga kiran yana sake bude hands free domin taji! Girgiza kanta tayi tace”qyale kawai ai duk wanda ya dauka dama ba zai barta a kunne ba yaje yayi min guzirin kiyama zai biyani a inda bashi dashi.” Mutumin yace.”Kinyi magana hajia Allah ya mayar miki da alkairi shi kuma daya dauka Allah ya tona asirinsa.
Amma yana da kyau kije ayi miki swapping d’in layin naki saboda jama’arki.” Tace”Habu sai na samu lokaci zanje kana ganin dai irin sana’a ta bani da lokacin kaina amma insha Allahu na samu lokaci zanje ayi min.
Naja’atu taji takaicin sace wayar da akayi, haka sukayi ta maganar kafin su hakura, Mmn Sajida ta cigaba da sabgoginta kamar ma ‘batan wayar bai dameta ba ita kuwa Naja’atu damuwa ta shiga sosai ta dinga tunanin hanyar da za tabi domin ganin ta taimaki kanta da kanta.
Aunty Maryam dai haka ta gaji da kiran waya ta hakura domun har ta zo tafiya wayar bata shiga ba, Hajiyar tace ta bari kawai tunda taqi shiga….Gabadaya da ita da hajiyan a sanyaye suka rabu da juna
Tun a mota take so tayi wa mijin nata maganar tana jin tsoro dan akwai sanda ta ta’ba yi masa maganar yarinyar ya nuna mata koda wasa kada ta kuskura ta sakeyi mata maganarta, ya nuna mata cewar shi babu ruwansa da yarinyar, a lokacin har sa’bani suka samu sabida hakan, ya daina mata magana tsayin kwana uku, al’amarin ya dinga bata mamaki! mutum da ‘yar uwarsa ina laifinta dan ta nuna kulawarta a kanta zai dinga gaba da ita, sai itama ta fusata ta dauke masa wuta! kwana uku dan karan kansa ya sakko ya nemi shiri da ita to tun daga ranar bata sake yi masa maganar yarinyar ba…Sai yanzu da take ganin dole ta fad’a masa abinda ke faruwa tunda dai yarinyar babu wanda ta fara nema da maganar sai ita to tilas ta fad’a masa koda kuwa zai dauki gaba da ita kamar wancan karon….Ta kalleshi a nutse tace”Wai kasan abinda yake faruwa da Naja’atu kuwa.? Abbah Magaji na driving yace.”Maryam ashe ban hanaki yi min maganar yarinyar nan ba.”? Tace” Kamar yaya? wannan wai wace irin magana kakeyi Naja’atu fa kanwarka ce uwa daya uba daya duk abinda zanyi a kanta saboda kai zanyi amma sai ka dinga nuna wani abu daban.
Yace.”To bana so na fad’a miki babu ruwana da yarinyar nan, kada ki sake ki tunzura min zuciyata duk abinda ya faru da ita itace ta janyowa kanta.” Murmushin takaici tayi tace”Au! ashe kasan abinda yake faruwa tsayin kwana uku kayi shuru da bakin ka ko.”? Yace.” Na sani asirin mijinta ya tuno wanda nasan dama komai daran dadewa dole sai haka ta faru dashi wannan yaron mugun mai laifi ne ni ganau ne ba jiyau ba shiyasa lokacin auran naqi saka kaina a ciki saboda nasan karshe ba zaiyi kyau ba.”
Tace”To dai yanzu duk wata magana ta qare tashin ma maganar bacin rai ne dan Allah kayi hakuri ka yafe mata kuma ku duba halin da take ciki! Dazu ta kirani a waya tana kuka take sheda min cewar ya saketa saki uku! Tsabar tashin hankalin dana shiga a lokacin yasa na kasa tambayarta inda take, na kashe wayar, to kuma dana sake kira sai wayar taqi shiga nida hajia mun shiga damuwa sosai da sosai A nan ne nima nasan abinda ke faruwa a bakin Ramaltu…..Yace.”Maryam ki rabu da yarinyar nan dan Allah! ai tasan hanyar gida, tunda ya saketa to zaman me takeyi sai ta tattaro ta dawo gida. Buqatarta ta biya.”
Maryam shuru kawai tayi tana jimanta al’amarin Eh wannan itace shawara mai kyau tunda babu aure a tsakaninta da Bash din to zaman da takeyi a gidan bai da amfani ta tattaro ta dawo gida ta nemi gafarar iyayenta.
Washe garin ranar haka kowa ya wayi gari cikin alhini da damuwar abinda ya faru da Naja’atu, dan Hajia kasa barin maganar tayi a ranta a daran ta samu alhaji ta sheda masa halin da ake ciki….Alhaji Sama’aila ya shiga tashin hankali gami da damuwar abinda ya faru da rayuwar Naja’atu, mutumin kasa bacci yayi a daran saboda alhini da asubah kuwa suna fitowa daga massalaci ya samu malam suka ke’be guri daya, kafin ya sheda masa abunda ke da akwai sai da yayi masa nasiha sosai sannan ya sheda masa rayuwar da Naja’atu take ciki….Baba malam ya jima kansa a kasa yana kiran sunan Allah kafin ya d’ago kansa ya kalli Alhaji a nutse yace.”Allah yasa haka shi yafi alkairi a rayuwata, hakika na jima banji abinda ya tayar min da hankali irin wannan ba ashe dama yaron nan dashi da mahaifinsa ba mutanan arziki bane suka zo suka yaudaremu muka dauki amanar yarinya muka basu, to babu komai ai tunda da alkairi muka nufe su suka nufe mu da sharri ina rokon Allah yasa haka shi yafi alkairi.” Alhaji yace.”Wannan adduar itace abinda ya kamata sabida haka yanzu na yanke shawara cewa bayan anyi daurin auran nan hankali ya kwanta gobe da wuri zan sa direba ya dauki Hajia Rabi tunda ita tasan gidan taje ta dauko yarinyar ina ganin wannan shine abinda yafi kamata muyi.
Baba malam yace.”To hakan yayi Alhaji nagode kwarai da gaske ina rokan Allah ya dubi gabanka da bayanka halinka nagari ya bika a duk inda kake.” Alhaji Sama’ila ya mika masa hannu tare da fad’in “Babu komai malam Naja’atu tamkar ‘yar cikina haka na dauketa dole ne na tsaya a cikin al’amuranta inayi mana fatan alkairi gabad’ayan mu.”
*ANGO*
A shirya ya fito daga dakinsa yana sanye da wata dakakkiyar geznar milk color babbar riga da ‘yar ciki da wani irin sirfani mai kyau a wuyan babbar rigar! Kasancewar shadda mai haske ce yasa yayi amfani da baqar hula had’e da bakin takalmi sau ciki agogon dake daure a hannunsa na dama shima baki ne, kai hatta da links din da yayi amfani dasu masu duhu ne! Wani irin kamshin turare yake mai dadi irin na manyan mutane! Kallo guda nayi masa na tabbatar da cewar ya amsa sunansa na ango sai dai kuma yanayin rashin walwala dake fuskarsa yasa na gane cewar akwai abinda ke damunsa.
Koda ya fito bai tunkari ko ina ba sai dakin Halisa…Tana zaune kasan kafet abin duniya ya taru yayi mata yawa, ga tarin magunguna nan a gabanta Halisa har yanzu taqi lafiya daga an toshe waccar matsalar sai wata ta bayyana yanzu wasu irin qananun kuraje ne suka feso mata a gabanta da matsematsin cinyarta kullum cikin susa take duk ta kwailaye fatar jikinta! Wannan dalilin yasa Abbah Abbas baya yarda wata mu’amula ta aure ta shiga tsakaninsa da ita ko toilet dinta baya shiga yayi wani uziri saboda a gabansa Dr Sa’adatu ta tabbatar masa da cewar Halisa na dauke da mugun sanyi wanda yayi masifar cin karfinta, wannan dalilin yasa ya janye jikinsa sosai da ita sai dai kuma duk wani abu da take bukata yana yi mata kuma yana tsaye kan duk wani maganin da Dr zata bada umarnin siya komai tsadarsa kuwa zai fitar da kudi ya siya sannan kuma ya jajurce a kan ta tayi amfani da maganin a kan ka’ida