MADADI Page 71 to 80

A nutse suka gaishe da Zainab suna mata kallon rashin sani, ita kuwa Zainab sai murmushi take tana jan hannun Mussadiq har sai da ta samu nasarar zaunar dashi a kusa da ita tana masa magana, Baba Larai ta kalli Saddiqa tana murmushi tace”Naga sai kallon rashin sani kuke mata itace sabuwar aunty ku Amaryar Abbanku.”
Saddiqa da Mufida suka shiga dariya suna ‘boye fuska, Baba Larai tasa dariya tana fad’in “Au! kunyarta kukeji? To amarya ga ‘ya’yanki nan wai kunyarki sukeji.”
Zainab na dariyar farin ciki tace”Haba dai meye najin kunyata ni mamanku ce ku saki jikinku dani kome kuke so kiyi min magana zanyi muku.”
Mussadiq na murmushi yace.”Aunty ya sunanki.”? Tace.”Sunana Zainab.” Yayi qasa da kansa yana murmushi tare da fad’in “Aunynmu munji dadin kasancewa dake muna miki fatan alkairi.” Cike da nishadi ta amsa da ameen tare da dan rungumeshi a jikinta, aikuwa a kan idon Abbah lokacin da yake fitowa daga dakin Halisa tana biye a bayansa….Ganin yaransa na murmushi ga Mussadiq rungume a jikin Zainab sai yaji wani farin ciki a cikin zuciyarsa yarinyar ta sake samun matsayi a zuciyarsa….Halisa ta danji dama dama dan tayi wanka tayi kwalliya daidai gwargwado amma ganin amarya zainab sai da ya sanya ta shiga cikin halin damuwa, daurewa kawai tayi ta zauna tana dan kauda kanta daga kan yarinyar….(Kishin nan fa dole sai anyi) Itama Zainab din kafin ta gaida Halisan sai da ta dan jima tukkuna tace” Aunt Ina kwana fatan kin tashi lafiya ya jiki kuma.”? Cikin dauriya tace”Lafiya lau jiki da sauki nagode sosai.” Shuru tayi da bakinta tana jin wani irin bakin kishi na taso mata a ganinta ai tunda ya samu wannan ‘yar yarinyar magana ta qare tafi kowa sanin halin mijinta gurin son matan tsiya watakila ma tun daran jiya ya gama da yarinyar, sai taji hawaye na kokarin zubo mata…Ta riga ta tashi daga aiki a gurinsa tunda tsoron ma rike hannunta yake sabida kada ya dauki cuta(Kaico da wannan rayuwa da kika jefa kanki)…..Abbah Abbas na qayataccen murmushi yake kallon Zainab yace.”Ina fata kun gaisa sosai da yaran naki.”
Yarinyar ta wani wulkita ido tana gyara bakinta cikin wata iriyar magana tace”Wallahi mun gaisa dasu sosai kuma naji da dadi dana samesu masu tarbiya da girmama na gaba dasu a gaskiya Habibi family d’inka sun burgeni sosai ina rokan Allah ya albarkace ni da samun zuria da kai.” Palon yayi tsit! Sakamakon maganar da Zainab take yi! Baba Larai da Halisa kasa ‘boye mamakinsu sukayi sai da suka kalli yarinyar suna jimanta bud’ewar idonta kamar ba ‘yar malamai ba???? gata ‘karamar yarinya amma sai firirita take gami da zaro zance ko kunyarsu ba taji.” Shi kuwa lafiyayyan murmushi ne a kwance a fuskarsa yace”Naji dadi kwarai da adduarki zainab Allah ya tabbatar mana da alkairi.” Ta amsa da amin tare da gyara zamanta a kan kujera
Halisa ta daure zuciyarta sosai ta kalleshi a hankali tace”Abbah Mufida ina ganin zan koma na kwanta jikina bana jin dadinsa.” Yace.”Okey kafin ki kwanta ki tabbatar kinyi braek ki kuma tabbatar da kinsha maganinki.” Mikewa Tayi a hankali tare da fad’in.”Insha Allah .” Zainab ta kalleta babu yabo babu fallasa tace”To aunty Allah ya sawaqe.” Ciki ciki ta amsa ta bar gurin, Abbah ya kalli Baba larai a nutse yace.”Komai ya kammala.”? Tace”Eh Alhaji.” Mi’kewa yayi ya kalli Zainab din da yaran yace.”Ku tashi muje mu karya.” Suka mike a nutse suka bi bayansa gurin cin abincin.
To a takaice dai Abbah Abbas bai tunkari amaryarsa da wata magana ba har sai da tayi uku a gidansa tukkuna ya tunkareta da wata bukata! sai kace wacce take jiran zuwansa ta kar’be shi hannu biyu, shi kuma ya shiga gwada mata soyayyarsa mai wahalar samu! Zainab itama ta dinga nuna masa fitinarta sai dai da akazo fad’an qarshe ne ta gane bata da wayo! dan ba wai tausayinta ya tsaya yi ba aiki yayi sosai ya zage a kanta ya bata kashi duk tarin sha’awar da ya tara ta tsayin wattanin da suka gabata ranar sai daya samu cikakkiyar gamusuwar da yake bukata da yarinyar…Zainab taji maza! ai lokaci guda ta shiga hankalinta ta daina rawar kai kullum a tsorace take da angon nata dan tun ranar daya mayar da ita cikakkiyar mace ya daina d’aga mata k’afa kullum sai ya biya bukatarsa har kwanaki bakwai d’inta suka qare, ta dinga murna tana godewa Allah zata sarara.”
******
‘Bangaran Naja’atu kuwa abun babu dad’in ji dan tun ranar data samu labarin auran Abbah Abbas taqi lafiya ciwon kai ciwon kirji da dai sauran ciwoka! Gashi sai ‘boyewa Mmn Sajida take taqi ta bari ta gane bata da lafiya, to itama Mmn Sajidan da yake ‘yar sabga ce bata fahimci komai ba sai dai sa’i da lokaci idan ta kalli Naja’atun takance” Naja’atu duk kin rame kinyi haske dan Allah ki cire damuwa da fargaba daga ranki! wallahi nasan iyayenki nacan hankalinsu a tashe sakamakon rashin ganinki ke kuma sabida wata manufa taki kin’ki kije garesu, duk fa abinda ya faru da rayuwarki qaddarace iyayenki musulmai ne zasu kar’bi qaddarar da Allah ya dora miki ba zasu guje ki ba.”
Duk sanda Mmn Sajida tayi mata wannan maganar ba ta cewa komai sai da tayi murmushi tayi shuru da bakinta.
Mmn Sajida haushi yasa ta tattarata ta qyaleta da taurin kanta.
To kamar yanda suka yanke shawara kancewa Hajia Rabi zata je garin jos domin dauko Naja’atu hakane ya kasance Direba ya dauketa da wurwuri suka nufi garin……..Sai dai tun kafin direban yayi parking din motar suka hango gate din gidan garqame da ‘katon kwado! Ga unguwar shuru babu wanda zasu tambaya…Hajia Rabi ba tayi qasa a gwiwa ba ta dauko wayarta ta kira mijinta domin sanar dashi halin da ake ciki…Alhaji Ya shiga mamaki mutuka yace.”Lallai su samu wani a unguwa wanda zasu tambayi domin yayi musu qarayin bayani …….Direba ya fito ya tsaya jikin mota yana kallon yanayin unguwar…Cikin ikon Allah wani bawan Allah yazo wucewa sai ya tsayar dashi da sauri ya miqa masa hannu suka gaisa yace.”Malam dan Allah ko kana da labarin mutanan nan gidan nan.” Ya fada yana nuna masa gidan
Mutumin ya jima yana kallonsa kafin yace.”Amma ba a garin nan kake ba ko.”? Da sauri yace.”Eh kwarai kuwa.” Mutumin ya girgiza kansa gami da fara bashi labarin abinda ya faru da mutanan gidan ya rufe maganarsa da fad’in ‘Wannan gidan da kake gani yanzu yana hannun bank dan haka tun wuri ku bar gurun nan tun kafin jama’a su ankara daku.” Da
Haruna Direba ya mika masa hannu yana masa godiya ya bude mota ya shiga…Ya kunna da sauri suka fita daga layin gidan….Sai da suka hau titi sosai san Ya sanar da Hajia Rabi abinda mutumin ya fad’a masa… A sanyaye tace”Wannan al’amari baiyi dadi ba ko kadan ko yanzu ina Naja’atu take? Kira ne ya shigo wayar ta ta dauka da sauri dan ganin wanda ya kira.
Alhaji yace.”Ina fata kun samu cikakken bayanin inda Naja’atu take, a sanyaye ta shiga fad’a masa maganar da mutumin nan ya fad’a dangane da gidan Aminu Dan jaridan….Alhaji yayi shuru yana tunanin inda zasu samu Naja’atun a cikin garin Jos.
*ANA WATA GA WATA*
Wani masifaffan amai ne ya tashe ta daga baccin da takeyi na safe! A guje ta dafe kirjinta ta nufi bakin rariya ta dinga kwararawa tana wani irin kakari tare da dafe kirjinta…………Ta kai minti goma tsugune a gurin kafin ta dan samu sassauci ta dauraye bakinta tare da mikewa tana dafa bango(garu) ta ciko buta da ruwa tazo ta wanke gurin data ‘bata, tana tangadi ta koma daki ta zauna tana mayar da numfashi……………Bayan Mintina ashirin tana zaune a takure zazzabi na neman rufeta ta sake jin wani aman ya sake yunkuro mata da masifar qarfi! da sauri ta mike ta nufi bakin rariya ta tsuguna tana yi tana hawaye! tun tana amayo abinci har sai da ta dawo amayo ruwa shima ruwan ya daina fitowa sai miyau da majina ne kadai ke fita, kuka takeyi tana kiran sunan Allah ta samu gefan rariyar (kwata) ta kwanta tana wani irin nishi tare da janyo numfashi da kyar! Naja’atu haka ta yini kwance a bakin rariya daga taji yunkurin amai sai tayi ta kakari amma babu abinda zai fito sai miyau mai dacin gaske…..Haka Mmn Sajida ta dawo daga cefane ta sameta lokacin ma ta galabaita sosai dan jikinta yayi laushi duk ya saki….Hankali a tashe Mmn Sajida ta shiga gidan Mmn Ladi suka fito tare, a daidaita sahu suka samo suka kamata dakyar suka sata a ciki suka zazzauna a gefanta domin ri’keta asibitin kudi Mmn Sajida tace su nufa dan ganin yanda Naja’atun ta galabaita yasa ta yanke wannan shawarar tana jin tsoron kada yarinyar mutane ta mutu a hannunta a tuhumeta shiyasa take gani ko nawa ne zata iya kashewa domin samun lafiyarta.