MADADI 1-END

MADADI Page 71 to 80

Gwajin farko Dr ya tabbatar musu da cewar tana da ciki dan kimanin sati tara! Wata biyu da sati daya! Mmn Sajida Da Mmn Ladi suka shiga cikin mamaki mai tsanani Ciki ciki! lallai Allah ya had’a Naja’atu da babbar qaddara……..

*Littafin na kudi ne…!*

Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake….Vip group #600 normal group #300 accont….0542382124…Binta umar gtbank…Idan katin waya zaki tura sai kiyi min mgn ta wahsap da wannan number 

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

*MANZIR _ALWAFIR ABUJA????????*

_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu  babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya ‘kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_

 *****60 Mmn Ladi tace”Dama fa ni wallahi sai da jikina ya bani cewar haka zata iya kasancewa kawai dai dan yarinyar ta nuna bata san maganar ne yasa nayi shuru amma da tun farko ta dauki maganata da muhimanci munje asibiti sun dubata sosai a lokacin da sai mu san yanda zamuyi da cikin tunda baiyi kwari ba amma yanzu ciki har ya shiga wata na uku ai akwai matsala idan akace za’ayi wani yunkuri a kansa, gaskiya na tausayawa yarinyar domin haihuwa da irin su Bash matsala ne  da da yanda za’ayi kawai a zubar da cikin nan wallahi.

A sanyaye Mmn Sajida tace”Nima dai jikina yayi sanyi wallahi amma bari  ta tashi daga bacci muji hukuncin data yanke.” Ajiyar zuciyarta da shashshekar kukanta sukaji.

da sauri suka kalli gadon da take kwance! Ta bude idonta a hankali hawaye wani na bin wani ta kalli Mmn Sajida murya na rawa tace”Ciki ne dani ko.”? A sanyaye Mmn Sajida ta daga mata kai

Rintse idonta tayi hawaye suka cigaba da zubowa” Innalilihi wa’ina ilaihi raji’un.”! Ta furta wannan kalmar tare da sake bude idonta tana kokarin mikewa zaune…..Mmn Ladi dake kusa da ita ta taimaka mata ta zauna tana goge hawayen fuskarta amma kamar bata gogewa wasu ne suke zubowa.

“Allah na kar’bi wannan kyautar da kayi min ba zan sake yunkurin sa’ba maka ba Ubangiji Allah ka ingata abinda ke cikina Allah kasa ya zama cikon addinin musulunci.” Wannan maganar ta fad’a tana me tsurawa rufin dakin ido.

Mmn Ladi tace”Bamu gane me kike nufi ba Naja’atu yanzu sabida baki da hankali sai ki yarda ki haifi cikin nan to wane labari mai dadi zaki bawa d’an da kika haifa idan ya girma? ai kwanciyar hankalinki da samun nutsuwar ki kawai ki zubar dashi shine yafi alkairi a tattare dake.”

Girgiza kanta ta dinga yi tana kallonsu tana kuka kokarin tsayar da ruwan hawayen dake gudana a fuskarta, tace”Bazan ‘kara aikata kuskuran da nayi a baya ba Mmn Ladi koda ace wannan cikin ta hanyar banza na sameshi ba zan zubar dashi ba sai na haifeshi domin ban san munufar ubangiji a kansa ba. Wallahi mutukar kinga ban haifi cikin nan ba to Allah ne bai nufa domin ni yanzu abinda zai kusantani da ubangiji nake so ba abinda zai nesanta ni dashi ba, a baya nayi kuskure wanda har yanzu nake cikin nadamarsa, to bana fatan na sake aikata wani kuskuran da Allah zai yi fushi dani ya tuhume ni a ranar lahira   kawai  ku dai  taya ni da addua kan  Allah ya rabani dashi lafiya.

Wannan kalaman nata sune suka kashe musu jiki Mmn Sajida tace”To shikkenan Naja’atu zamu cigaba da taya ki addua kan Allah ya saukeki lafiya ya kuma kawo miki mafita a rayuwarki, ammafa yana da kyau ki koma ga iyayenki domin zaman da kike a tare damu bashi da wani amfani na fad’a miki duk inda iyayenki suke suna can hankalinsu a tashe suna neman inda kike me zai sanya ki dinga jin tsoro da tunanin wani abu daban.”

Ajiyar zuciya ta sauke tace”Mmn Sajida ko dai kin gaji da zama dani ne? ko kin gaji da ciyar dani abincinki shiyasa kike wannan maganar.”? Mmn Sajida ta shiga girgiza kanta tana murmushi mai ciwo tace”Gaskiya Naja’atu ban ta’ba tsammanin jin wannan maganar daga gurinki ba Haba dan Allah meye makwanci meye kuma abinci da har kike tunanin saboda su nake cewa kije ga iyayenki! To idan tunanin da kike kenan  ki daina Mmn Sajida ba haka take ba duk wani abu da nake miki inayi miki ne tsakani da Allah bada wata manufa ba.”

Naja’atu qasa tayi da kanta tana nadamar maganar data fad’awa Mmn Sajida dan sai bayan ta fad’i maganar ne ta gane kamar bata kyauta ba, tasan halin Mmn Sajida macace mai karamci da mutuncin itace zata fad’awa wani hakan 

Likita ne ya shigo dakin hannunsa rike da wata farar takarda! Ya mikawa Mmn Sajida da fadin duk wasu bayanai na jikin takardar nan idan kun duba zaku gani.” Mmn Sajida da Mmn Ladi basa jin turanci sosai shiyasa basu fahimci rubutun da likita yayi a jikinta takardar ba.

Naja’atu ta kar’bi takardar tana dubawa, gabanta ne ya fad’i ganin kudin gadon data kwanta yini guda dubo goma sai kudin magungunanta dubu bakwai da dari biyar….qasa tayi da kanta tana jin nauyin fad’a musu abinda ke rubuce a takardar….To a Ina Mmn Sajida taga dubu goma sha bakwai yanzu gabad’aya Jarin abincin siyar wa ta baifi na dubu ashirin ba dashi take ci take sha ita da ‘yayanta yanxu idan ta sanadiyar ta ta ruguza mata sana’arta  me zata ce.?  jikinta ne yayi sanyi sosai ta tsirawa takardar ido tana tunanin yanda za’ayi.

Mmn Sajida tace”Naja’atu me Dr din ya ruboto.” A dan sanyaye tace”Mmn Sajida me yasa kuka kawo ni pravite hospital baku kaini na gomnati ba.”?

Mmn Sajida tace”Naja’atu tsorata nayi da yanayin yanda ganki shiyasa na yanke shawarar kawo ki asibitin kudi domin ayi gaggawar dubaki sanin da nayi cewar idan na gomnati mukaje kafin ma mu samu kati babban aiki ne  sannan idan mukaje gurin ganin likita nan ma sai mun ‘bata lokaci shiyasa kawai na yanke wannan shawarar.” 

Wasu hawaye masu zafi suka sauko a kumatunta gaskiya ta tabbatar da cewar Mmn Sajida masoyiyarta ce   har ta mutu ba zata ta’ba mantawa da karamcinta ba.

Shuru dakin yayi Mmn Sajida jikinta yayi sanyi itama tana jin tsoro da fargabar  abinda ka iya zuwa ya dawo…Tace”Nawa ne kudin gadon dana maganin insha Allahu ba zai gagara ba.”

Ta kalleta tana girgiza kanta tace”Dubu goma sha bakwai da dari biyar.” Mmn Ladi ta ri’ke bakinta cike da mamaki tace”Dubu goma sha bakwai harda wata dari biyar a kai! Tabdijam!  ko awa hud’u ba kiyi a kwance ba har kinci wannan kudin.”

Naja’atu tace”Ba kudin gado bane kadai harda na magani.” Mmn Ladi tace”Duk da haka dai wallahi da tsada haba abin yayi yawa  dubu goma sha bakwai fa ba kad’an bane gaskiya asibitin nan suna da tsada ta’bdijam.”! Mmn Sajida tace”Duk mu bar maganar dan Allah ko nawa suka rubuta ai hakkinsu ne tunda dai mu muka zo neman taimako kuma sun taimaka mana a lokacin da muke bukata bai kamata mu tsaya surutu ba, Yanzu ni abinda ke hannuna gabad’aya dubu bakwai ne dama na ajiyesu saboda wata matsalar, amma yanzu zan koma gida  zan  dauki buhun shinkafar dana siyo shekaran jiya zan kaiwa maigari mai kanti ya siya nasan idan na siyar za’a had’a kudin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button