MAKAUNIYAR KADDARA 44

Wata ƴar dariya ce ta suɓucema Baffah babu zato, ya shafa kan Little yanayin kayarsa hankali kwance. Kafin ya ɗago yana nuna mata little. “Wannan shine tunani mafi gurɓata da kika taɓayi a rayuwarki Hindatu, kinsanfa ance abin cikin ƙwan yafi ƙwan daɗi. Dan haka ki sani wannan da kike gani zuciyata ne da duk ma wanda yake rayuwa a gidan nan. Kinsan kuwa raba zuciya da gangar jiki abune mai wahala ga ɓarawo. Amma tunda kema kin shirya wasan muzuba, ɗan halak ka fasa. Sai dai ki sani wasa zamuyi da basira bada hauka ba. Ki cire wannan shirmen a ranki ki nutsu waje guda wajen farautar dawo da Abdul-Mutallab gareki, nima zanyi farautar ganin ya dawo gareni daga shi har Maryam (Adilah) sannan kuma na haɗa da ɗan jikallena abin cikin ƙwan”. Ya ƙare da wani salon ɗage mata gira ɗaya.
Da ƙarfi ta rumtse ido da cije baki, harshenta har harɗewa yake wajen ambaton, “Muje zuwa mana, kaima kasan Hindatu, nama ƙwata ada da kake jin kanka Kabeer Shira balle yanzun. Wlhy saina tabbatar maka dani Hindatu bakatsiniyace ƴar asali”.
“Kika dai sata. Kamar yanda nima sai na ƙara tabbatar miki dani Kabeer jinin bauchi ne gaba da baya babu gauraye”.
Fuuuuu Mammah taja hannun Farah dake kuka dan duk a firgice take suka fice. Dama tun jiya da dare suka iso a hotel sukai masauki.
“Amma Yaya miyasa zaka biye mata? Kasan fa Hindatu dama can ƴar zafin kai ce. Dan ALLAH karku saka yaranku a rikicinku, gashi ma harda jiƙa da shi baima gama saninkuba da ƙyau har yanzun”.
Murmushi Baffah yayi yana kallon little. Hankalinsa kwance yace, “Zai sammu ne Bilkisu. Zafin kan Hindatu kuwa zan sauke mata shi a wannan karon dan na fita itama ta sani. Wasu dalilaine kawai yasa na barta ko a can baya ɗinma”.
Shiru falon yayi zuciyar kowa da fargaba. Musamman ma Momie da ayanzu ta gama sallama ma bala’i da gadarar Hindatu.
Silalewa Huzaifa yayi ya fice, dan abinda kawai zuciyarsa ke basa da wannan game ɗin kafin a farashi Hajiya iya ta dawo gidan nan. Inba hakaba Mammah zata iya bin ta wata hanyar ta sace koda little ne ta gudu dashi idan Ak ya gagareta a yanzun. Wayar Khalipha ya kira.
A lokacin yana kwance zazzaɓi ya rufesa, dan duk yanda yaketa ƙoƙarin danne damuwar rasa Zinneerah hakan na neman fallasa kansa. Amma dai yanata roƙon ALLAH ya rufa masa asiri ya cire masa ita a rai, dan baya buƙatar Yayansu dawowa ya gansa a wannan halin. Ɗagawa yay cikin dauriya, bayan sun gaisa Huzaifa ke tambayarsa ko lafiya?. Cikin dakewa yace masa a barci ya tashi.
Cikin gamsuwa Huzaifa yace ya haɗasa da Hajiya iya, shima kuma ya zauna a wajenta dan maganar ta shafesa. Amsa masa da to Khalipha yayi yana tashi ya fito. A falo ya samesu su duka zaune suna hira da kallo. Ya miƙama Hajiya iya wayar yana sanar mata Huzaifa ne.
Amsa tai cikin tsokana ta fara da faɗin, “Ɗan nema mun shirya kenan? Bandama abinka nima ai bazanso aima autata kishiya ba”.
Damuwar da Huzaifa ke a ciki ta tashin hankalin daya gani ya sakashi cewa “Granny magana zamuyi ni dake da Khalipha ”.
“Lafiya dai ko?”.
“Da sauƙi dai”.
Tsaye hajiya iya ta miƙe tabar wajen zuwa ɗaki Khalipha ya bita. Daga haka Huzaifa ya yanke kiran shi kuma ya kirasu a video call. Bai ɓoyema Hajiya iya da Khalipha komaiba daya gama faruwa yanzun nan. Cikin matsanancin mamaki Khalipha yace, “Dama Nigeria wai su aunty Farah ɗin suka taho?”..
“Gasu harma suna ƙulla game da Baffah. Granny inaga ki dawo gaskiya dan wannan al’amarin ba wasa bane. Na tabbata Mammah zata iya sace little shima, dan nidai yanda ta nuna ɗin na tsorata. Ni kuma wlhy yanda na fahimci Yayanmu nason Abdul-Mutallab banason ta rabashi da shi. Bama shiba koni yaron ya shiga raina. Hakama yaran gidan nan wlhy suna tsananin ƙaunarsa, dan yanda suka shaƙu da shi aduk da ba gidan yake ba ya isa amsa gamai kallo. Khalipha zan turo kuɗi a shiyama Granny tahowa, idan lokacin ganin likitan yayi saita koma”.
Cikin gamsuwa Khalipha ya gyaɗa masa kai kawai. Dan shima ya gamsu da hakan, shi kansa zai bisu dan yasan Yayansu nacan cikin damuwa da tashin hankaki dama gashi ya tafi a birkice.
A ɓangaren AK kam koda ya koma ɗakinsa duk abinda ke faruwa tsakanin Baffah da Mammah yana jiyosa, har game ɗin da suka ƙulla tsaf yaji, mamakin Mammah ya sake kamashi jin kuma little ɗinma ya zama abin harinta bayan ita ta gama bala’i ranar a london.
Safa da marwa ya shigayi a ɗakin yana tunani da nazarin matakin dazai ɗauka akan Farah dan harga ALLAH yana tsoron Mammah ta cigaba da busar masa da idonta akan wannan halayen da sam basa birgesa. Dolene yayi wani abu kafin wankin hula ya kaisa dare.
Ciwon da kansa ke masane ya sakashi tattara komai ya ajiye ya koma gado ya kwanta. Duk da tarin ayyukan dake garesa a yinin yau dan yanason komawa london gobe idan ALLAH ya kaimu baijin zai iya fita a gidan. Maganar komawama babu ita tunda su Mammah sukazo nan ɗin. Dan dole ya haƙura har sai yaga sun koma.
_________________★
Babu wanda yasan mi Huzaifa ya ƙulla. Cikin dare sai ga baƙin london. AK na zaune bisa sallaya yana karatun Al-qur’ani bayan kammala nafilfilinsa ya ɗanji maganganu sama-sama. Mamaki ya kamashi duk tunaninsa Farah da Mammah ne suka kwana a gidan, dan shi da wuri yay barci jiya saboda allura da Dr Mahmud yazo yay masa kasancewar jininsa ya hau sama sosai dalilin ɓacin ran safiyar jiyan. Little ma yau a wajen su Momie ya kwana, tunma fitar da Baffah yay dashi bai sake ganisa ba sai da yamma Huzaifa ya shigo tare dashi duba jikinsa. Da Abidah kuma ta shigo kawo musu abinci ya maƙale mata.
Bai tashi ba sai da yakai inda ya dace, Al-qur’anin ya rufe ya tashi ya fita a ɗakin. Turus ya tsaya yana kallonsu Meenal dake shigowa da kaya, ga Hajiya iya zaune cikin kujera tana shan ruwan da Zinneerah ta ɗakko mata a kitchen. Murmushin kwantar da hankali Hajiya Iya tai masa. Yayinda su Jamal suka shiga gaishesa murya ƙasa-ƙasa dan darene sosai kusan ƙarfe uku ma.
Da ƙyar ya iya ɗaga ƙafarsa ya tako garesu, Zinneerah da sai yanzu hankalintama yakai garesa dan ta juya baya a yanda take tsaye ta ɗan matsa ta bashi hanya murya ƙasa-ƙasa tace, “Barka da dare Yayanmu”…………✍
[ad_2]