MAKAUNIYAR KADDARA 44

 *page 44*

………..A gajiye suka shigo gidan gab da magriba, dama sun ajiye Dr Mahmud a gidansa. Little kuwa yayi barci jikin Abbansa dan Huzaifa ne yay driving ɗin. 

        Koda Huzaifa yay fakin a inda ya dace AK fita yay ɗauke da little a kafaɗa, kai tsaye sashen Hajiya iya ya nufa batare da ya saurari maganar da Huzaifa ke masaba. Kasancewar bayan tafiyarsu Abidah ta shigo ta gyara masa sashen sai ko ina ya kasance ƙal ga kuma ƙamshi, sosai yakejin kewar rashin Granny a sashen. Dan haka baima son zama ya yini a gidan sam.

      A hankali ya kwantar da little dake barcinsa. Duk da ya ɓata jikinsa sosai a can bai tadashiba, sai dai shi ya cire nasa kayan ya nufi bayi a gurguje saboda lokacin sallar magrib yayi. 

     Wankan ma a gaggauce ya yisa ya fito, jallabiya kawai ya zura ya ɗan saka turare ya fito yana addu’ar ALLAH yasa kar little ya farka harya dawo. 

     Bayan an idar da salla bai zaunaba ya nufo gida saboda tunanin barin little da yayi shi kaɗai. Koda ya leƙo yaga barcinsa yake har yanzu sai ya koma massallacin. Sai da akai sallar isha’i suka taho shi da ƴan uwansa da Baffah gwanin sha’awa. 

       A gajiye yake matuƙa, dan haka ya wuce sashen hajiya iya kai tsaye yana cema Mas’ood yasa cikinsu Safiyya wani ya kawo masa tea da abinci kaɗan saboda little karya farka ya nema. Da to Mas’ood ya amsa masa cikin girmamawa. 

      Harya nufi hanyar sashen hajiya iya baffah dake ƙoƙarin shigewa nasa sashe shima ya juyi ya dubi AK ɗin. “Karfa suga mun musu ƙarfa-ƙarfa akan yaron nan, daga zuwa ya gaida Bilkisu”.

      Juyiwa AK yay zuciyarsa na harbawa, harga ALLAH baya fatan abinda zaisa Baffah yace ya sake rabuwa da little ɗin a yanzu, danshi yanzu haka yana shiryama zuciyarsa tafiya da yaron nema london. Amma yanzu sai ya ɗan murmusa, murya a sanyaye yace, “Baffah zai koma ai sonake saina tashi tafiya”.

      “Sai da safe”. Baffah ya faɗa yana shigewarsa. Shima cigaba yay da tafiya zuciyarsa na masa rauni akan iya sake rabuwa da gudan jinin nasa gaskiya.

      Washe gari da safe bayan idar da sallar asuba koda suka dawo sake kwanciya yayi, dan cikin dare Little ya farka da kuka, sai da yay masa wanka ya bashi abinci suka sami salama. Shiyyasa yau ya tashi kansa na masa ciwo. To ɗan barcin daya samu ya sake komawane kuma yana tsaka ya ringajin hayaniya na tashi sama-sama a cikin sashen nasu. Duk yanda yaso daurewa karya tashi hakan ya gagara. Dole ya miƙe da ƙyar yana jan tsaki. Mamaki ya kamashi ganin babu little a ɗakin, tashi yay ya zira doguwar riga bayan ya shiga toilet ya fito, yasa Slippers ya fita. Ganin babu little a ɗan corridor ɗin wajen nanma ya fita da sauri, abinda ya gani ya sakashi tsayawa cak. Ashe a falon hajiya iya ake hayaniyar shiyyasa yake jinta sosai. Ba kuma kowa keyiba sai Mammahn sa, Farah na gefenta tana kuka kamar zata shiɗe.

     Yabi Baffah dake ɗauke da little da kallo, daga shi har Mommy suna zaune kawai sun zubama Mammah idanu tana ta zabga musu azabar masifa akan abinda shi yama kasa fahimta kai tsaye. A matan gidan Momie ce kawai, dan ita kaɗai Baffah ya bama damar zuwa lokacin da Saifudden yazo ya sanar masa da zuwan Farah da Mammah duk da sau ɗaya ya taɓa ganinta kuma suna yara sannan, amma tsananin kamarta da Yayansu yasa yaji a ransa lallai itace Mammah, hakama yaran babu ko ɗaya a waje sai Huzaifa kawai.

     Ji AK yayi tamkar ya fasa kuka dan takaici, dan har cikin ransa yaji haushin wannan zuwa da sukai. A hankali ya fara takowa zuwa tsakkiyar falon cikin izzar da fushi ya haddasa masa, fuskarnan tai kicin-kicin kamar zata fashe dan ɓacin rai.

         Wani shegen tsawa data saka little fashewa da kuka yana ƙanƙame Baffah ya dakama Farah dake ƙoƙarin fara magana dan daga ita har Mammah basuga zuwansa wajenba. Ba Farah ba har Mammah sai da tai ɓam da bakinta ta juyo tana tana kallonsa ranta a matuƙar ɓace.

       Yi yay kamar baiga Mammah ba ya fara saukema Farah duk fushin nasa. “Da izinin ubanwa kikazo Nigeria? Wai Farah kin maidani ɗan iskane da duk abinda ranki ya raya miki kikeyinsa komi?. Ki maida hankalinki fa…….”

         A fusace Mammah ta katsesa da cewar, “Ubanka yace tazo, taƙi ta maida hankalin nata kuma, yanzu nan Abdul-Mutallab ko kunyar ALLAH bakaji a gabana kake cimata mutunci?”.

         “Mammah!” ya faɗa ransa a ɓace, danya fahimci idan har ba nuna mata ɓacin ran nasa yayiba itama to zata cigaba da bauɗar masa da Farah da banzar aƙidarta. Cikin rufewar ido yace, “Please Mammah ba maganar wasa nakeba, wane kalar rashin mutuncine sai dai ta ɗauka ƙafa daga wata ƙasa ta taho bada izinina ba, kodan taga wancan karon na mata shirune? To wlhy ni bazan ɗauka wannan iskancin ba, na bata nanda awanni goma ta koma inda ta fito, inba hakaba wlhy saina tabbatar mata da ainahina na Abdul-Mutallab Kabeer Abdul-Mutallab Shira”.

     Daga haka ya juya ya koma ɗakinsa. Wani ɗan murmushi Baffah yayi na manya ganin yanda Mammah tabi AK da kallo baki buɗe kamar sokuwa. Ƙara rungumesa little yayi da sumbatar goshinsa, shiko yaro ya ƙara lafe masa a jiki saboda tsorata da bala’in daddynsa.

       Juyowa Mammah tayi tana kallon Baffah cike da tashin hankali. Idanu ya ɗan waro mata alamar minene? murmushi ɗauke a fuskarsa har yanzu.

      Ƙara ƙufula tai da salon nasa, dan babu abinda ta gani sai Kabeer ɗinta masoyinta na da, muryarta har rawa take wajen faɗin, “Kabeer haka ka maidamin yaro?”.

     “Dama haka kika haifi abinki”. Baffah ya bata amsa kansa tsaye yana sake sumbatar goshin little. Sai kuma ya kalleta yana ƴar dariya, “Hindatu ko iya haka muka tsaya kin sami amsarki akan Adnan, dan kinji dai abinda yace, sunansa Abdul-Mutallab Kabeer Abdul-Mutallab Shira. Ba Abdul-Mutallab Hindatu Umar Kaita ba. Ballantana yanzu muka fara wasan ni da ke wlhy, dan sai na tabbatar miki ke kaɗai kikazo gidan nan badasu ba”.

      “Kabeer Shira!”.

Ta faɗa a tsawace. 

     Shima Baffah a fusacen yace, 

“Yes! I am. Hindatu Kaita!”.

       Ganin yanda Baffah da Mammah sukai ɗin ya tayarma Mommy da Momie hankali, shi kansa Huzaifa ƙarjinsa sai bugawa yake dan tamkar AK yake bayason hayaniya, barshi dai da shegen surutu shima yafiyi ga wanda ya sani sosai. Farah kuwa ai sake tsurewa tayi dan bata taɓa tunanin haka Baffah yakeba. Kallon mutum mai sauƙin kan tsiya take masa.

      “Dan ALLAH kuyi haƙuri ni banga abin tashin hankali ananba Yaya”. Mommy ta faɗa hankalinta tashe tana dawowa kusa da Baffah. 

        A fusace Mammah ta miƙe tare da kama hannun Farah da duk jikinta ke ɓari. Ta duba Baffah da manyan idanunta da har ƙwalla suke tarawa dan bala’i. “Banzo Nigeria da niyar yin fitina da kai ba Kabeer, amma tunda har kace ka shirya muje zuwa. Ina mai tabbatar maka bazan bar ƙasar nanba sai da yarona, sai kuma nasan uwar data haifa wannan ɗan da shi. In ko har aure ka ɗaura masa da ita aka samar da shi sai ya saketa, na haɗa da yaron kuma na wuce, dan yazama nawa shima”.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button