MAKAUNIYAR KADDARA 45

tace, “I miss you my heart, ALLAH ya albarkaci rayuwarka, ya baka kariya
a kowanne sakan na agogo”.
A ɗakin hajiya iya kuwa koda AK ya shiga tararwa yay su Baffah na
magana. Baffah na zayyanema Hajiya iyan yanda sukai da Mammah. Gaishesu
yayi, duk suka amsa masa da kulawa. ya yunƙura da nufin fitowa ya basu
waje Hajiya iya ta dakatar dashi ranta a ɓace dajin abinda Mammah tazo
tayi.
Komawa yayi ya zauna kansa a ƙasa dan yaƙi yarda ya kalli kowansu,
bayason suga damuwar dake kwance a cikin idanunsa.
Cikin kaushin murya Hajiya iya tace, “Ina maka murna da samun
yarinyar ƙwarai kamar Zinneerah moddibo, itama kuma ina tayata murna da
samunka matsayin miji. duk da har yanzu zuciyata ta gaza hasaso ko
tunanin ta yanda kuka samar da Abdul-Mutallab. Amma a dalilin wani
bayani da Khalipha yaymin yasani shiga wasuwasi, zuciyata kuma ta ƙara
shiga ruɗani da bayanin mahaifinka akan abinda ya faru randa aka sanar
maka yaron jininka ne. Sai dai hakan dakai ba shike nuna zan yarda dakai
ɗari bisa ɗari ba Moddibo har saina san gaskiyar al’amarin nan. Amma zan
cigaba da roƙon ALLAH ya bayyanamin gaskiyar kafin nabar duniya. Ada
nayi tunanin barin tarewar Zinneerah harta kammala karatunta na
sakandire. Yanzu kuma na canja shawara saboda dalilai masu yawa. Ciki
kuwa harda gadaran da mahaifiyarka keson nuna mana akanka da ƴar uwarka,
tunda dai ita na fahimci batasan kawaiciba. Kaje daga yau ka fara gyaran
gidanka, ka kuma shirya haɗama Inno lefe dan nan da kwanaki goma zata
tare”.
Ba AK kawai ba hatta Baffah da Mommy sai da suka ɗago suka kalli
Hajiya iya. Cinkin ɗan rawar baki Baffah yace, “Amma Inna karatunta
fa?”.
“Tayi a gidansa”.
Ta bama Baffah amsa kai tsaye babu alamar wasa ko sassauci a saman
fuskarta. Ɗan ajiyar zuciya Baffah ya sauke duk da shima bawai yana
nufin wani dogon zango Zinneerah zata kaiba. Dama dai tunaninsa bai wuce
ta gama zana jarabawarta ta ssce da zasu fara kwanan nanba. Amma kuma
tunda hajiya iya ta yanke hukunci shi hakan ya masa kodan ya sake
tabbatarma Hindatu shine boss.
Mommy ce tai ɗan murmushi tana kallon hajiya iyan, cikin kwantar
da murya tace, “Innarmu baƙya ganin anyi gaggawa. Mu bashi damar
shiryawa a tsanake sai a haɗa danasu Ni’ima tunda wata biyu ne kawai ya
rage”.
“Na riga na gama yanke hukunci Bilkisu, ba kuma zan canjaba
saboda shine dai-dai. Anjima kaɗan za’a kaini gidan Hauwa’u itama”.
Dole Baffah da Mommy suka amsa da to, AK kuwa uffan baice mataba.
Dan shi yanzuma hankalinsa ba’a kansu yakeba. Tunanin wace magana?
Khalipha ya sanarma Hajiya iyan yakeyi.
Ganin yanda yayi ɗinne yasa hajiya iya kallonsa a ƙufule.
“Saboda an manna maka abinda ka ɓata yasa kaimin shiru Abdul-Mutallab?”.
Yanda ta faɗi real name nashi ya tabbatar masa da har zuciyarta
ne. Dan haka ya ɗago ya kalleta, wani ɗan murmushi ya sakar mata yana
miƙewa, “Indai nine kamar ki ɓata ranki, duk yanda kikeso haka za’ayi”.
Daga haka ya nufi ƙofar fita abinsa.
Su duka da kallo suka bisa. Hajiya iya dake masa kallon harara tace,
“Munafuki kama fito ka faɗa kowa ya sani”.
Babu shiri dariya ta suɓucema Baffah da Mommy, dan yanda Granny
tai maganar dolene ta baka dariya. Itako tai kicin-kicin da fuska kamar
ba ita ta faɗa ba.
Koda AK ya fita baiko kalli kowa a falonba ya fice, garden ya
nufa kai tsaye, yana shiga ya ciro wayarsa a aljihu ya dannama Khalipha
kira. Cikin sa’a kuwa ta shiga. Ring ɗaya ana biyu Khalipha ya ɗaga dan
yaga sanda Yayan nasu ya fita daga falon kamar a fusace.
“Ka sameni a garden”. Ya faɗa kawai yana yankewa.
Miƙewa Khalipha yayi da sauri ya fice shima sauran yaran na binsa
da kallo. Tun kafin ya ƙaraso cikin garden ɗin ya hango AK daketa safa
da narwa hannayensa duka biyu goye a bayansa. Sai da ya iso daf da shi
sannan yay sallama. Juyowa AK yayi ya zuba masa birkitattun idanunsa da
suka gama tsorata Khaliphan a take. Duk yanda yaso daurewa sai ya kasa
dole ya risinar da kansa ƙasa. Cikin harɗewar harshe yace, “Yayanmu
gani”.
“Na ganka ai”.
AK ya faɗa yana nufar kujera ya zauna. Fahimtar da Khalipha yayi yau a
yaya yake ba besty ba sai ya nufesa shima ya zauna kusa da shi cikin
rauni.
“Yayanmu wani abu ya faru ne?”.
“Zai dai faru Khalipha”.
Ƙara daurewa Khalipha yayi, dan shi duk tunaninsa ko Yayansu bayason
auren Zinneerah ne, duk da yanajin zafin rasata bazai so Yayansu rabuwa
da itaba dan sun dace. Duk da kuma yanada mata ya fisu buƙatar Zinneerah
a yanzu.
Cikin nuna damuwarsa a bayyane yace, “Yayanmu dan ALLAH miya
faru? Wlhy tsoratani kake sakeyi”.
Kamar AK bazai tankaba sai kuma ya gyara zamansa yana duban
Khalipha ɗin da ƙyau. Zazzafar iska ya furzar idanunsa na sake rinewa.
Kai tsaye yace, “Wace magana kukai da Granny?”.
“Granny kuma? Ni?”.
Khalipha ya faɗa cikin jinjinawa da son tunanowa.
Shiru AK yayi baice komaiba. Hakan ya bama Khalipha damar shiga
kundin tunani na tsahon mintuna huɗu. Sai kuma ya duba AK yana ɗan
jinjina kansa. “A sanina dai gaskiya babu wata magana da nayi da ita. In
badai akan maganar IV……”.
Sai kuma ya kasa ƙarasawa.
Da idanu AK yay masa alamar cigaba. Dole Khalipha ya ɗan haɗiye yawu
yana maida kansa kasa. Maganar da suka tattauna da Hajiya iya akan
hanyoyin iya samuwar ciki ya sanar masa. Har yakai aya AK baice komaiba,
dan tun a fara bayanin ya raba hankalinsa biyu, ɗaya ga Khalipha ɗaya ga
nazari da fashin baƙin dukkan kalma ɗaya dake fita a zancen Khalipha
ɗin.
“Amma kai miyasa kayi wannan hasashen?”. AK yay tambayar yana
duban Khalipha cikin ido.
“Ba hasashe nayiba Yayanmu, kawai dai yanda ita Granny tai maganar
hanyoyin iya samuwar cikine sai ta dalili ɗaya yasa nai mata fashin baƙi
akai cewar yanzu akwai wasu hanyoyi da suka ɓullo a likitance. Ni wlhy
bamma ɗauka zata riƙi maganar serious ba sam”.
Karan farko AK ya saki wani lallausan murmushi da ɗaura hannunsa
akan kafaɗar Khalipha ya dan bubbuga tare da miƙewa. Daga haka baice
komaiba ya nufi barin garden ɗin yabar Khalipha binsa da kallo.
Sai da ya ɓacema ganinsa sannan ya sauke numfashi shima da ɗaura
hannunsa akan kumatu yayi tagumi. A fili ya furta, ‘Anya kuwa nima ban