MAKAUNIYAR KADDARA 46

bakin ɗorawar kan hanya na jira Hajja Lanti zamuje anguwa. Ban musa
mataba naje na canja kayana na fito, saita sake korani da cewar naje na
saka kayan sallata. Zuwa nai na sake canjo kayan na fito, a gabansu na
tafi inda tace naje na jira hajja Lanti ɗin. Na jima a bakin ɗorawa
zaune sannan hajja lanti tazo ita da wasu yara da ban sansu ba. Batare
da itama tamin bayaniba ta bani hijjabi da nikab wai na saka. Nidai ban
musa mataba na saka. bayan na sakane ta kira masu mashin su uku suka
daukemu zuwa Gozarki. A Gozarki muka kwana dan maraice ya rufa lokacin.
Washe gari tunda farar safiya muka tafi inda ake hawa mota muka shiga
motar Katsina da naji ana faɗi a wajen. Nasha mamaki amma a raina ina
ɗoki zanje katsina da nakeji a labari. Koda muka isa Katsina an saukemu
a wani waje mai tarin jama’a, mudai muka shiɗa a motar kamar yanda tace
mana. Daga nan an ɗibemu a napep zuwa wani waje da naji hajja Lanti ta
kira da suna anguwar yari.
Kamar yanda ƴan uwan tafiyata basa gane komai a wannan tafiya
nima dai ba ganewa nakeba. Sai dai ina lure da komai da akeyi. Kamar
sunayen wajajen da muka sauka da inda muke tafiya. Mun isa anguwar yari
da tace a kaimu. Inda aka saukemu a wani gida mai matsakaicin ƙyau da
girma.
Koda muka shiga cikin gidan mun samu kusan mutane goma a
cikinsa, Sai wata dattijuwar mata da tafi hajja Lanti shekaru dajin
daɗi. Yanda ta tarbemu ne yasa naji ɗan dadi ga raina. Sai dai yanda
maza da mata ke shiga da fita gidan baiminba a rai. Mun jima zaune suna
hira kafin a kawo mana abinci muci, bayan mun koshi aka haɗamu da wata a
gidan mai suna Sadiya. Itace ta kaimu wani ɗaki wai anan zamu zauna.
Nidai kallon kowa nake da mamaki da tunanin mi mukazoyi nan? Miyasa Inna
tace na biyo wannan matar nan batare da Baba ma ya sani ba?. Banda mai
bani amsa, shiyyasa naja bakina na tsuke. Daga wannan lokaci ban sake
ganin hajja Lanti ba a gidan, ban kawo komai a rainaba sai tunanin ko
taje wani wajene ta dawo tazo mu dawo gida. Amma sai naji shiru har
tsayin kwana biyu. Duk da ana bamu abinci muci mu ƙoshi, ga television
muna kallo hakan baisa hankalina ya kwantaba, sai dai inajin tsoron na
tambayi wani ina hajja Lanti take?. A randa muka cika kwanaki uku a
gidan naga an kwashi abokan tafiyata su uku aka fita dasu a gidan, daga
haka ban sake ganinsuba suma. Hankalina ya tashi na shiga yi musu kuka
akan nidai su maidani garinmu, danni na ɗauka kodai ƴan yankan kai ne
ma. Ranar naga ruwan masifa wajen matar nan, dan kamar zata dakani a
turmi saboda masufar data dinga min. Dolena shanye kukana saboda
tsoronta. Da maraice aka sake kwashe sauran abokan tafiyata su biyu da
suka rage aka barni ni kaɗai sai waɗanda na samu a gidan. Ranarma nayi
kuka har takaini gayin masassara.
Magani kawai suka bani nasha, daga haka babu wanda ya sake bi
takaina, sai ma da daddare kusan ƙarfe takwas hajiyar tace a tasoni zamu
fita. Ina jinta daga ɗaki danba barci nakeba, tunanin asibiti zata kaini
yasa ban kawo komai a rainaba na tashi na fito bayan na saka hijjab
ɗina. Tsaye na sameta a tsakar gida cikin gayu, na gaisheta jikina duk a
sanyaye saboda zazzaɓi dake cina. Gaba tai na bita baya batare damin
maganaba. Muna fitowa ƙofar gida muka iske mota mai ƙyau.
Motarnan muka shiga, gabana nata faɗuwa nidai inata tunanin
lokacin yanke nawa kan yayi. Dan haka naita addu’a kala-kala ina sharar
hawaye a ɓoye da roƙon gafarar babana a zuciya, a haka muka iso wata
babbar anguwa dabansan sunantaba, sai dai yanda ko’ina ke ƙwanyar da
hasken lantarki zai tabbatar maka da anguwar masu kuɗice. Katafaren gida
mai blue gate aka buɗe mana muka shiga, kasancewar darene bazan iya
banbance tsarin gidanba, sai dai lallai ya haɗu matuƙa. Koda muka fito a
motar hajiya ce ta kama hannuna muka shiga ciki. Anan ne na sake
tabbatar da gidan ya haɗu, masu shi kuma sunada kuɗi.
Waɗanda muka samu a falon ne sukai mana iso zuwa ciki bayan mun
gaisa, an sake kaimu wani falon, inda muka zauna zaman jiran matar
gidan. Munfi ƙarfin awa ɗaya zaune kafin ta fito, ƙyaƙyƙyawa ce sosai
baƙa, daka ganta kaga bafulatanar bakatsiniya, dan ƙyawun nata ya fita
sosai masha ALLAH. Sai da ta gama mana kallon tsaf kafin ta amsa mana
gaisuwa tana sake ƙaremin kallo, cikin maganar daban ganeba hajiya tace,
“Ranki ya daɗe ga wata ki duba ko zata iya, yau kwana uku da kawomin su
daga wani ƙauye”.
Kallona ta sakeyi sama da ƙasa tana ɗan yamutsa fusaka. Ta ɗage
kafaɗunta cike da isa tana faɗin, “Uhm babu laifi kam, dan tafi waccan
komai, girma kawai waccan zata fita. Amma ina zuwa”. Tai maganar tana
miƙewa, fita tai, babu jimawa sai gata ta dawo ɗauke da waya, batare da
tayimana maganaba ta shiga haskani da hasken wayarta daban fahimci
ma’anarsaba a wancan karon, sai dai a yanzu inaji a raina camara ne.
Bayan ta gama kuma ta fara waya, da turanci take magana shiyyasa banji
komaiba, bansan dai ga hajiya ba. Ta ɗauki lokaci mai tsaho tanayi kafin
ta ajiye ta dubi hajiyar, “Ba damuwa zamu gwada mu gani, bara na ɗakko
miki sauran saƙonki ko, idan akwai wani matsala zan nemiki daga baya
kafin ki wuce, namafison sai mun kammala komai mun fara wucewa kafin
taki tafiya”.
Baki a washe Hajiya tace, “Ato babu damuwa ranki ya daɗe, ni bani
da matsala duk yanda kukeso sai ayi, fatana dai ALLAH yasa a dace
akumayi nasara”.
Cike da yanga ta amsa da amin. Daga haka taje ta kawo mata saƙon da
tace. Inaji ina gani hajiya ta miƙe tana faɗamin aini nan zata barni,
nanne zanyi nawa aikin, dan haka sai nayi biyayya, yi nayi bari na bari.
Sosai na fara hawayen fili saɓanin na zuci, yanda zuciyata kemin
zugi da zafi ya hanani yin magana harta fice ta tafi bayan ta bani ɗari
biyar a kuɗin danaga an bata masu yawa, itama haijiyar gidan ta shige
batare damin maganaba. Da wannan damar nai zaman kuka na kusan awa ɗaya
kafin wata tazo cikin wanda muka fara tararwa a falon farko ta kama
hannuna muka fice.
In taƙaita miki Granny tun daga ranar zazzaɓina ya ƙaru, inaga
ganin yanda nake galabaita yasa Hajiyarnan ɗaukata a washe gari takaini
wani asibiti mai ƙyau da alama na kuɗine. Anan aka bani gado. Sosai
likitan yaytamin tambayoyi harnaji nama ƙosa dashi, amma na daure dan
lafiyata nake nema ai. Kwanana shidda a asibitin nan na warke sarai aka
sallamoni, sai dai kuma hajiya ta kaini wani gida ba nata da aka fara
kainiba, naji tsoro sosai, dan can babu kowa sai wata dattijiwar mata
mai suna Harirah.