MAKAUNIYAR KADDARA 46

Ɗaki guda aka bani a gidan, wanda yaji duka kayan more rayuwa, ni
harma abin ya ban mamaki amma sai ban tambayaba tunda dai ance aiki
nazoyi. Komai na nema ina samu a gidan, amma sai dai a tsorace nake, dan
haka kawai na kasa yarda da sakin jiki da baba harirah, sai dai kullum
sai ta shigo ɗakina ita ta sakani shan magungunana na asibiti da aka
bani. Hajiyar kuma ban sake ganintaba sai bayan kwanaki sai gata.
Cataimin na shirya muje asibiti likita ya sake dubani, ban kawo komai a
raiba na shirya na bita zuciyata fal fargaba. Munje likita ya sakemin
gwaje-gwaje, sai yace wai akwai wani ciwo dake damuna zasu ban magani.
Daga wannan maganar aka kaini wani ɗaki, tunda akaimin wata allura ban
sake sanin inda nakeba sai a gida. Ni kuma tunda na farka sai tsoro ya
kamani ganin ko baba harirah ɗinma yanzu babu, sai wani gardi abin tsoro
dake a waje. Hankalina ya tashi, da ƙyar na samu nai wanka nayi salla.
ina idarwa na saka kayan danazo dasu daga gidan hajiyar farko da aka
kaini, ALLAH ya taimakeni na silalo na fito daga gidan, ɗari biyar ɗin
da hajiyar ta bani da zata tafi lokacin data kaini can gidan itace ta
taimaka mani na koma Danya. Koda na koma kuma saina kasa bama kowa
labarin abinda ya faru har Babana, duk da inason na faɗa masa kodan
kalmar iskanci da Inna ke dangantani da shi sai dai inajin tsorone”.
Shiru hajiya iya kawai tai tana kallon Zinneerah kamar mai
karanto komai akan fuskarta, sai dai wani irin tausayin yarinyar da
ƙaunarta na sake shigarta. Dan yanda take bata labarin a nutse sai take
ƙara godema ALLAH da samunta matsayin matar jikanta mafi soyuwa a ranta.
Ta ɗan murmusa cike da basarwa tana faɗin, “Uhmm lallai dole ki kasa
mantawa da birnin katsina. To amma ita hajiyar data kaiki gidan baki
koma gidantaba bayan kin baro can?”.
“Wai Granny sokike na koma ta sake maidani, nifa wlhy haka kawai
naji banason hajiyarnan data kaini asibiti, ta cika tsare gida da mulkin
tsiya kamar sarki”.
A karon farko Hajiya iya tai dariya da juyawa tana kallon AK datun
fara maganarta da Zinneerah ya shigo ɗakin, sai dai jin labarin da
Zinneerah ta fara badawa ya sakashi dakatawa batare daya shigoba. Yanda
ya kafe Zinneerah da idanu yana ma labarin nata fashin baƙi da
nazartarsa yasa hajiya iya faɗin, “Amma baki taɓa gamo da maikama da
wancan mutumin a katsina ɗinba?”.
Sai a lokacin Zinneerah ta farga da AK, duk da ta jima tanajin
ƙamshinsa a hancinta bata kawo shi baneba. Kallo ɗaya tai masa tai
saurin maida kanta ƙasa saboda yanda kwarjininsa ke cika mata idanu da
zuciya. Cikin girgiza kai tace, “A’a Granny, anan na fara ganinsa
nikam”.
“Inno bafa wasa nakeba”.
Da iya gaskiyarta tace, “Wlhy kuwa Granny”.
Hajiya iya zata sake magana AK ya katseta da faɗin, “Kin shirya ne
na kaiki gidan Gwaggon?”. (mmn sadiq).
Tsaf hajiya iya ta fahimci dalilinsa na katseta, dan haka tai
guntun murmushi da cewa, “Eh bara na kimtsa, ai hada Inno ma zamuje
saimu barta acan dan da safe idan ALLAH ya kaimu zata dawo akwai inda
zan turata”.
Baice komaiba sai duban Zinneerah ɗin datai ƙasa da kanta yaɗanyi,
ya ɗauke idanunsa ya juya ya fice.
Binsa da kallo Zinneerah tayi, tana ganin ya fice ta sauke ɓoyayyar
ajiyar zuciya da har sai da hajiya iya tai murmushi………….✍
[ad_2]