MAKAUNIYAR KADDARA 50

Tsabar yanda zuciyar Mammah takai maƙura a hasala sai kawai ta fashe musu da kuka. “Wlhy bazan yardaba, bazan yarda a rabani da ƴaƴana ba tunda nice na haifi abuna bayan wahalar rainon cikinsu dana sha. Ita matar Ahmad data kwace miki shi miyasa kika kasa komai sai ni zakibi ki sama ido akan nawa ƴaƴ…….”
“Hindatu!!”.
Baffah ya daka mata tsawa jikinsa har rawa yake na ɓacin rai. Murmushi hajiya iya tayi da ɗaga masa hannu. ta duba Mammah da ƙyau tana faɗin, “Itama ba ƙarfina tafi ba, kamar yanda kika ɗauke su moddibo muka barki yanzu kuma lokacin dawowarsu cikinmu yayi, itama lokacin da zan nuna mata nina haifi Ahmad ɗin yayi ai”.
“Wlhy ni kuma nayi alƙawarin yin amfani da ƙarfina na uwa wajen raba wannan auren, ɗa kuma da suka haifa a waje zaimin bayanine dalla-dalla dan ubansa”.
Ran Mahma da yay matuƙar ɓaci da abinda Mammah keyi bayan sai da ta ƙwaɓeta kafin su taho ta kama hannunta ta maidata ta zaunar a fusace. “Hindatu wai mike damun kanki? A ganina kamata yay ki nutsu ayi magana ta fahimta amma kinzo kinama mutane shirme. Kifa sani yanda kike da haƙƙi akansu Adilah haka shima mahaifinsu keda haƙƙi a kansu, yakumayi iya bakin ƙoƙarin sa wajen yimiki kawaici akansu, ai idan kinason yaranki su kasance dake basai ta hanyar ƙarfi da iko ba tunda suma sunsan ke uwa ce a garesu. maimakon ki damu dajin ta yanda akai Abdul-Mutallab ya samar da yarog yarinya a waje ke damuwarki kawai ƴaƴanki zasu suɓuce miki, haba wane kalar son kai ne wannan?”.
Kuka sosai Mammah keyi, tace, “Haba Addah kinajinfa yanda suka haɗa kai zasumin taron dangi, taya zasu ma yaro aure bada saninaba haka ake rayuwa?……”
“Ke sanda kikai masa aure bada saninmu ba wace gadarace baki manaba”. Baffah ya katseta a fusace. Ransa a ƙololuwar ɓace ya cigaba da faɗin, “Hindatu idan kin manta bara na tuna miki, matar da Adnan ke aure karki manta sai ana gobe ɗaurin aurensa da ita kika faɗa mana, amma duk da rannmu ya ɓaci Inna ta tilasta mana haƙuri mu barki tunda aurene, yarinyar kuma ƴar uwarki ce. Haka muka danne zukatanmu muka amsheta a cikinmu da hannu bibbiyu amma ki ka ɗorata akan keken ɓera wajen nuna mata muɗin mutanen banza ne bama sonki da ƙaunarki, sai kuma a yanzu dan mun maimaita abinda kika aikata zakiji zafi? Ai dama na faɗa miki ƴaƴana sai sun dawo gareni tunda ke bakisan mutunciba, burinki kawai ki nisantasu dani da ƴan uwana to muzuba mu gani ɗan halak ka fasa ni da ke a garin nan”.
Mammah zata sake magana Mahma ta dakatar da ita da sauri. “Kuyi haƙuri Kabeer, tabbas Hindatu ta aikata laifi, amma inason ku fahimceta itama, kunsan a duk sanda mace ta rabu da uban ƴaƴanta babbar fargabarta shine barin masa ƴaƴanta wata tazo ta cuta musu koshi uban ya nisantasu da ita. Na tabbata wannan shine fargabar Hindatu tun a wancan lokaci da yanzu haka. Amma bawai hakan na nufin ina goya mata baya akan abinda takeyi nason ganin ita ta nisantasu da ku ba duk da kawaicin da kukai mata na tsayin shekaru. Ina son dan ALLAH a wannan gaɓar mu haɗu wajen yafema juna, mukuma fahimci juna dan mu duka munada ƙarfin iko akan Adilah da Abdul-Mutallab. Sai dai hakan ba yana nufin mu cigaba da raba hankalinsu ba da ƙarfin ikon da ALLAH ya bamu akansuba na iyaye”.
Tsit falon yayi dan maganar Mahma tayi tasiri a zukatansu sunkuma san gaskiya ta faɗa. Hakan yasa AK dake tsaye tun ɗazun daga bakin ƙofa ya ƙarasa shigiwa. Zama yay ya gaidasu batare da ya yarda ya haɗa ido da kowaba dan ransa a jagule yake babu daɗi.
Mahma ce ta dubesa da kulawa, “Abdul-Mutallab nasan duk kaji mike faruwa. Sai dai jin naka bashine mai muhimmanci ba, a yanzu mu munfi buƙatar son sanin a ina aka haihu a ragaya game da haihuwar yaro mai sunanka?”.
Iska yaɗan furzar kansa a ƙasa. “Mahma wlhy nima ban saniba”.
“Kamarya baka saniba, a ruwa ake shan ciki balle kace mana itama acan tasha?”. Aunty Zakiyya tai magana karon farko tun shigowarsu a hasale
“Tabbas ba’a sha, amma inaga itakam dai acan ta shashi. Dan ni dai ban taɓa tarayya da wata mace bayan matata ba ALLAH shine shaidata. Sannan ban taɓa ganin yarinyarnan da idanuna ba sai a gidan nan. Amma kuma tabbas na yarda Abdul-Mutallab ɗa nane, ina kuma kan binciken ta yadda aka samar dashi insha ALLAH”.
Shiru falon yayi tsahon lokaci, sai Uncle Ahmad da wani tunani yazo masa a zuciya dan shidai shedane akan AK bai iya ƙaryaba yace, “Abdul-Mutallab maganar nan ba wadda mutane zasu ɗauka bace balle su fahimceka. Amma sai nake tunanin ko kun taɓa yunƙurin yin wannan dashen na zamani da aketa nusar al’ummar musulmi rashin anfaninsa?”.
A karon farko AK ya ɗago ya duba Uncle ɗin nasa da rinannun idanunsa. Hakama Mammah da aunty Zakiyya a razane suka dubi Uncle Ahmad har hakan ya bama Mahma da Hajiya iya mamaki. Da sauri AK ya girgiza masa kansa. “Wlhy Uncle ni ban taɓa son hakanba dan bayama birgeni, na tabbatar idan ALLAH yaso zai bani, da bai baniba kuma ƙila haka shine mafi alkairi a gareni”.
Cikin jinjina kai Uncle Ahmad yace, “Na yarda da kai Adnan dan baka taɓa min ƙaryaba, sai dai wannan al’amarin na buƙatar bincike, musamman ga matarka kota taɓa wannan yunƙurin aka samu kuskuren ɗaukar sparm ɗinka aka saka ga ita yarinyar bada sanin ku ba ku duka tunda wannan matsalar kan faru saboda son zuciyar wasu likitocin, kokuma daga likitocin matsalar take baki ɗaya”.
Wani irin mugun tarine ya sarƙe aunty Zakiyya har sai da aka bata ruwa. Ita kanta Mammah sai zufa take gogewa a kaikaice. Cikin rawar murya tace, “Hakan bamai yuwuwa bane, tayaya za’ai yunƙurin hakan shi bada saninsa ba, kuma shi da ke a london yarinyar na ƙauyen katsina taya ya hakan zai faru, yadai zauna yayi tunani ko wani akasi ya taɓa faruwa”.
Hajiya iya da zuciyarta keta kaikawo da nazarin kowa a wajen tace, “Inaga to wannan maganar babbace gaskiya, mu ajiyeta a yanzu idan an gama biki lafiya saimu yita a tsanake, dan yanzu haka ga Huzaifa nata kirana kunsan ana jiranmu a wajen walimar can”.
Baffah da shi kansa tunanin zuciyarsa ya fara canjawa daga akalar zargin Ak da yake har yanzu zuwa zancen ɗan uwansa cikin gamsuwa yace, “Hakan shine dai-dai Inna”.
Tabbas a wannan gaɓar suma su Mammah sunfi buƙatar tsayawar zancen su sami dama da sararin yin nazari, dan haka duk suka amince. Sai dai basuso zuwa wajen walimarba Mahma ta takura musu akan saifa sunjeta dole ko shima AK ɗin zaiji sanyi a ransa ai.
Gudun zargin wani abu daban daga AK yasasu yarda zasuje. Dan ya tsatstsare su da idanunsa da gaba ɗaya suke a birkuce da abubuwa kala-kala da shima baisan adadinsu ba.
★★
Sun isa ƙaton hall ɗin da za’a gudanar da walima and liyafar cin abinci rana daya ƙawatu matuƙa. Ya kuma cika taf da al’ummar MANZON ALLAH (S.A.W). Ga manya manyan malamai da zasu gabatar da lectures. Sashin mata daban na maza daban babu ruwan wani da wani, hakkane ya samama AK nutsuwar da yake buƙatar samu. Suna isowa aka gabatar da addu’oi da suka shafi komai na rayuwa bayan ma’auratan, kafin a fara abinda ya tara mutane.