UBAYD MALEEK 36

 **************Suna fitowa Kai tsaye wani qaramin underground gidansa dake cikin anguwar suka nufa Wanda keda 2 bedrooms rak da manyan Palo guda biyu sai kitchen me hade da dining acikinsa komai na gidan is milk Mr Omar ne kawai yasanda gidan Babu Wanda yasan gidan nasane Haka gidan komai a kip kip yake anan yake wasu private wayoyinsa da ayyukansa hakama wata maganar me buqatan tsananin sirri anan suke zuwa suyita da Mr Omar.

Parking Mr Omar yayi yafito ya budewa MALEEK yafito kafin yabudewa NURU ita saiya zagaya ya budewa farhat tareda kamo hannunta suka biyo bayan maleek dake gaba tareda NURU dake tafiya ahankali sbd ciwon Mara.

Suna shiga palon NURU ta dago ta kalli koina cikin palon cikeda mamakin tsaruwar gidan da cikin yafi wajenma kyau sosai saidai sbd yanayinta bazata iya qarewa koina kalloba a matse take data samu guri ta kwanta Tasha ruwan zafi masu zafi Sosai ko zata Dan fada Mata tasamu period din ya sauko wahalar ta rage Mata.

A palon farko ya dakata tareda kallonta Yana nuna Mata kofar palon qurya inda bedrooms suke cikin nutsuwa yace”

Ki Shiga ciki zanyi mgn da Mr Omar.

Dan dagowa tayi ta kallesa har lokacin ita yake kallo ta gyada Kai ahankali ta juya farhat na riqeda hannunta suka wuce cikin.

Palon cikin baiyi girman na farkon ba Amma yafisa tsaruwa ta juya gurin bedrooms din ta nufi Wanda yake damarta ta murda tareda budewa ahankali batasan lokacinda ta sauke ajiyar zuciyaba sbd ganin girma da tsaruwar dakin ga makeken gadon daya kusa cika dakin komai fes fes sai qamshi koina gidan keyi da Alama kullum Ana gyara koina agidan ayi mopping Dan ko yau kila anyi Dan qamshin dayake koina dagaji sabon gyarane.

Tana Isa bakin gadon ta sulale ta haye tareda kwantawa tana dungulewa guri daya tana dafe mararta rufe idanuwanta tana Jin Dan dama dama data kwanta din.

Sai daga baya ta bude idanuwanta ahankali ta kalli farhat da duk tayi wani iri sbd halinda aka shiga sai taji yarinyar tasake shiga ranta sbd tausayinta ta cire hannu daya takamota kusada ita ta bude Baki daqyar tace”

Sweetie kadakiji tsoro ko damuwan komai kinji daddy Yana Nan Nima Ina Nan Afia ma zatazo komai lafiya Inshallah,yanzu Kinga Banda lafiya I can’t treat and drss your wound kije kifadawa daddy Akira mum Sarah tazo ko Dr aduba kafanki kafin anjima nasamu naji Dan sauki kinji.

Gyada Kai tayi tareda juyawa ta fice zuwa gurin daddynta din.

Tana fita NURU tasake nadewa guri daya kaman jira Marar keyi ta kwanta tasamu nutsuwa sai ciwon yasake taso Mata wani irin zafi da zufa suka fara karyo Mata ta tashi zaune daqyar ta kunna AC Takoma ta kwanta tana shigewa cikin bargon dake kan gadon me tsananin laushi fari tas.

Kallon Mr Omar maleek yayi yace”

Kasan abinda zakayi next idan an daukosu din.

Gyada Kai Mr Omar yayi Yana cewa”

Za’a kaisu wancan gidan ne na 7579 zibrian kowa yasan aikinsa yakama suyi gyaran koina Kafin zuwa gobe ko jibi ku Isa can din.

Gyada Masa Kai maleek yayi Kai tsaye zai juya saiga farhat ta qaraso gurinsa ta shige jikinsa tana cewa”

Daddy aunt NURU batada lafiya bazata iya duba ciwona ba tace Akira min mum Sarah ko Dr” taqarasa fada tana nuna kafarta.

Kallon kafar sukayi dukkaninsu inda ruwan zafin suka zubar Mata a kafa sai alokacin sukasani ga ‘yar farar kafar tata har tayi ja 

Maleek ya dago ya kalli farhat din yace”

Aunt dinki bazata iya duba Miki qafanba ta gyara?

Eh daddy tun jiya da daddare aunt NURU tace cikinta na ciwo haryanxu be Dena ba gurin karbo Mata tea ne ruwan zafin ya zuba a kafana mum taketa fada.

Shiru maleek yayi kafin ya dago ya kalli Mr Omar dayayi saurin rage kansa Yana cewa”

Za’a kaita gurin Sarah acan zibrian ta kula da qafar kafin ku iso zankira Dr Damien ma yazo ya duba kafan Inshallah.

Kama hannun farhat Mr Omar din yayi Yayi gaba suka fice ya nufi mota ya bude ya sakata ya zagaya yashiga Yana waya da Edward akan idan sun Isa zibrian din da kowa yace Masa eh ankai kowa Babu Wanda aka baro a tsohon gidan sai tsohuwan madam da princess afia.

Kashe wayarsa yayi ya fita harabar gidan yahau hanyar zuwa zibrian din Yana yiwa farhat ‘yar Wasa tadawo yanda take sbd yarinyar ta Dan razana da komai daya faru.

Bayan tafiyar Mr Omar ya juyo Kai tsaye ya nufi hanyar dayan bedroom Wanda ba nasaba ya Murda Kai tsaye ya tura yana kallon koina baiganta acikiba ya fito tareda rufo qofar ya nufi bedroom dinda yake gefe dabam Wanda yake matsayin nasa Yana zuwa ya bude kofar ahankali ya shiga tareda rufowa yana kallon yanda ta kwanta a dungule ya ajiye wayoyinsa kan qaramin glass table dake gefen sofar dakin ya qarasa gadon tareda tsayawa akanta Yana kallonta har saidataji mutum tsaye akanta ta bude idanuwanta ahankali ta dago dasu ta kallesa ta Mayar ta rufe tana yunqurin tashi zaune ya dakatar da ita ta hanyar Kai hannunsa daya ya maidata kwance Yana kallon wuyanta daya taba yaji zafi.

Wayarsace tayi blinkin na wuta batareda ya daukaba ya waiwaya ya kalli wayar yaga massage din Mr Omar ne daya rubuto” _Dr Damien na ya iso Yana kofa_

Zaunawa yayi bakin gadon tareda yaye bargonta ahankali tareda tayarda ita zaune da kansa Yana kallonta ahankali yace”

Dr Damien zai dubaki.

Zuba Masa idanuwanta dasukai laushi tayi tanason ce Masa Bata buqatar likita Amma sai batace komaiba ta gyada Masa Kai tana matsowa bakin gadon ta zura qafafunta qasa ya miqa Mata hannunsa ahankali ta dago ta kallesa kafin ta Dora nata akai ta Kama nasa ya miqar da ita hannunta cikin nasa suka fito Palo suka sake wucewa zuwa na farko acan suka tararda Dr Damien tareda Mr Omar dake tsaye Yana ganin fitowarsu ya sauke Kai tareda juyawa ya fice Dan Basu guri.

Daga yanda Dr Damien yafara tambayarta tabashi amsa Kai tsaye Dr Damien ya fahimci ciwonta yace”

Bawani matsala bane menstrual pains ne kawai 

Ya Bata pain reliever da wasu maganin ya miqe ya fice.

Kallonta maleek yayi Kai tsaye yace”

Kina buqatan wani Abu?

Gyada Kai tayi tana miqewa suka nufi ciki tana cewa”

Zanyiwa Mr Omar texting dinsu.

Kallonta yayi bayan sunshiga dakin ya matsota jikinsa sosai ya ranqwafo da kansa daidai fuskarta yace”

Kiyi online shopping akawo daga can Mr Omar baya buqatan sanin abubuwan dazaki buqata.

Kasa dagowa tayi ta kallesa sbd sai lokacin ma takejin kunyar ciwon nata da maganar Dan kuwa itama bazaso Mr Omar tayi Masa texting su pad da panties da kayan bacci da komaima.

Rintse idanu tayi tareda zamewa ta juya ta nufi bakin gadon ta zauna tana tunanin dame zatayi shopping din ba tunda batada wayarta atareda ita.

Miqa Mata wayarsa yayi bayan ya bude Mata password ya fice daga dakin.

Panties da bra dasu pad sai turaruka da kayan bacci data siya guda uku sbd tasan zuwa anjima ko gobe za’a kawo musu kayansu na sawa itada farhat sai brushes data siya musu itada farhat da kayan baccin farhat din tayi payment dakomai duk da komai nasa kafin ta aje wayar sbd Nanda mintuna goma zuwa Sha biyar kayan zasu iso ta miqe tareda zare doguwar rigar data Dora kan kayanta ta nufi toilet din dakin ta bude taga wani irin girmane dashi tashiga tana mamakin komai na dakin da toilet din harta tube tasakarwa kanta ruwan zafi ta gasa mararta datai nauyi Dan har lokacin be saukoba period din.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button