MAKAUNIYAR KADDARA 50

     Malamai sun ragargaza lectures masu ratsa jiki akan aure da zamantakewar rayuwa data saka jikin mutane da yawa yin sanyi, Zinneerah amarya da duk da basan waye mijin nataba tasha kuka itama, lectures ɗin kuma sun shigeta matuƙa. Lokacin salla nayi aka fita akai sallar zuhur sannan aka dawo aka ɗora dacin abinci, a hakanma dai malamai na cigaba da aikinsu har zuwa la’asar da aka rufe da addu’oin fatan alkairi ga ma’aurata damu da muke a gidan auren sannan aka tashi.

      Da yawan mutane daga nan suka fara kama gabansu, wasu kuma suka koma gidansu AK domin rakiyar amarya ɗakinta da za’ayi da wuri, duk da dai hajiya iya tace ƴan danya bazasu koma a yau ba kamar yanda suka sanar, tace su bari sai ALLAH ya kaimu gobe su da ƴan ɗan musa saisu tafi.

       Sunkiji daɗin haka dan sam garin ba isarsu yayiba. Musamman da kowa yake samun isashen abinci mai rai da lafiya nama har ba’a cewa komai.

     Suna dawowa ba’a zaunaba Hajiya falmata ta hau yima amarya shiri na musamman wanda ya kaisu har bayan isha’i, ana idar da salla ta kammala naɗeta cikin haɗaɗɗiyar lifaya datai mata matuƙar ƙyau kamar ba an Zinnin danya mai tallar riɗi da gyaɗa ba. Daga haka aka miƙata wajen su Baffah da manyan iyaye ƴan bauchi sukai mata faɗa da nasiha matsayinsu na iyaye gareta, sai ga hajiya iya na sharar hawaye kuma, hakama su Meenal kuka rurus suke sha abin tausayi, Sa’a ma sai ta kama kuka dama tasha wani a danya. Tinene kuwa tana kwance rijib babu lafiya dan ko a wajen walima kasa sakewa tayi, danma Yaya Atine nata mata masifa wai harda langwai daga zazzaɓi.

     Yaya Gajeje najinsu dai bata tankaba dan ita tasan mita hango tattare da Tinene ɗin, tanata ƙoƙarin dannewane harsu koma lafiya gida kawai.      

         Bayan an kwashi masu rakkiyar amarya a motoci aka fito da amarya daketa rusar kuka wadda Hajiya iya zatai mata rakkiya har ɗakin mijinta. Aiko Zinneerah na naɗe a jikinta tanata kuka ranta fal fargabar wanda zata tarar matsayin mijin nata har suka iso ƙyaƙyƙyawan gidan na AK da yaji kayan more rayuwa. Duk da yace kar iyayenta suyi komai sai da suka nuna bajintarsu suma gwargwadon ƙarfinsu. Dan kuɗin baba dana abba aka dunƙule waje ɗaya akai mata kaya ƴan ubansu da gara, hajiya iya kuwa dama itace tayi komai na kayan kitchen. 

      Ɓangaren ta daban na Farah daban, duk da dai babban falon farkon shigowa ya haɗa ɓangarorin gidan uku, dole ta cikinsa zaka doshi kowanne ɓangare harna mai gidan, amma kuma kowacce a sashenta tanada faluka guda biyu kuma da bedrooms har uku sai kitchen. Tun kafin fitowa mota sai da hajiya iya ta saka zinneerah dake lulluɓe har kanta tana kuka yin addu’a, hakama da zasu shiga babban falon da sashenta.

      A lokacin da ƴan kawo amarya ke shigowa su Mammah suna sashen Farah cikin tashin hankalin sumar da tayi, dan tunda aka taso wajen walima su nan gidan suka nufo kai tsaye, tarbarau tayi da murnarta dan batasan mike faruwaba, kuma ko daɗewa dayin waya da AK bataiba. Sai dai halin da taga aunty Zakiyya da Mammah a ciki ya ɗaga mata hankali ta shiga tambayarsu lafiya? Duk yanda Mahma taso ƙwaɓar aunty Zakiyya da ido akan karta sanar mata sai da aunty Zakiyya da hankalinta ke tashe da zancen Uncle Ahmad na dashen ciki tai suɓutar baki wajen sanarma Farah zancen auren AK. Ko rufe baki batayiba Farah ta yanke jiki ta faɗi a sume.

    ALLAH ya sosu hakan yay dai-dai da shigowar AK gidan a gajiye. Hankalin sane ya tashi matuƙa shima, babu shiri ya tsaida Dr Mahmud da ya kawosa gida. Tofa shine tun lokaci suka rufu akanta da ƙyar suka samu ta farfaɗo Dr Mahmud daya sa aka kawo masa kayan aiki daga asibiti yay mata allurar barci mai nauyi da har yanzu take kanyi bata farkaba.

       Mammah sai masifa take akan wlhy idan Farah ta rasa ranta sai tayima Kabeer abinda bazai taɓa mantawa da ita a duniya ba. Tanayi tana sharar hawaye hakama aunty Zakiyya kuka take rurus dan tana tsananin ƙaunar autar tasu Farah da tausayinta ke damunsu saboda mahaifiyarsu na haihuwarta ta rasa ranta ko ganin Farah ɗin ma batayiba.

     Koda sukaji an kawo amarya Mahma ce kawai tai ƙarfin halin fita tarbarsu kar ace babu kowa a cikinsu tunda ansan suna gidan kuma. Bata nunama hajiya iya komai na halin da ake cikiba ta rungume Zinneerah tana mata barka da zuwa cikinsu. Ita dai Zinneerah ba sanin wacece tayiba tunda kanta a rufe yake, tanata dai sharar hawayenta musamman da taji mutane nata sallama suna ficewa dan ance ba zama za’ai ba. Duk maison ganin ɗakin amarya yazo gobe idan ALLAH ya kaimu ya gani da ƙyau.

     Wannan yasa Zinneerah batasan sanda hajiya iya ta sulale ta gudu ba ita dasu Yaya Gajeje. Kafinma ta farga sai jin hayaniyar tayi ta ɗauke ɗaf daga inda take sai acan harabar gidan take jiyosu.

    Zamewa tai a gadon ta kwanta tare da sake fashewa da wani irin sabon kuka maiban tausayi dacin rai………….✍

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button