MAKAUNIYAR KADDARA 51

       Karan farko AK ya saki ɗan murmushi, dan shikam dai zuciyarsa ta fara raya masa wani abu game da yanayin Mammah da Aunty Zakiyya, ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe da gyara tsaiwarsa. Cikin rashin sakewarsa yace, “Kaga yimata ɗin kamar yanda sukace, dan a ganina zamanta a farken yafi allurar zama matsala ga lafiyar tata”.

       Kai kawai Dr Mahmud ya gyaɗa masa, dan shikam dai baimaga wani alamun ciki a jikin Farah ɗin ba. Yana ƙoƙarin haɗa allurar yace, “Amma cikin nata yakai wata nawane?”.

      Shiru Mammah da aunty Zakiyya sukayi, sai Mahma ce tace, “Kamar dai biyar ko”.

     “Biyar fa?”.

Dr Mahmud ya ambata mamaki ƙarara a fuskarsa. Ɗan duban Farah ɗin dake riƙe jikin Mammah tana kuka da wani ɗan fisge-fisge yayi ya ɗauke kansa. Batare da yace komaiba yay mata allurar kawai ransa fal wasiwasi.

     Yana gama mata allurar ko mintuna biyar ba’a ƙullaba barci ya ƙara ɗaukarsa. Kallon AK Mahma tayi da cewa, “Taimaka ka kai mana ita mota Abdul-Mutallab, ku kuma kumuje shima ya samu ya huta”.

       Babu shiri Mammah tace, “Addah ai shine zai kaimu, taya matarsa na wannan halin yaga wani ta hutu?”.

     Murmushi Mahma tayi na takaici, muryarta aɗan hasale tace, “Duk mu da muke tare da ita bai wadatarba sai shi ya kasance a wajen?. Ai ya kamata a tausaya masa ya huta ga kuma yarinya an kawo zai barta ita kaɗai kenan komi?”.

      A take Mammah ta sake tamke fuska matuƙa. Ta kalli AK da yay tamkar bayama jinsu yanata latsa waya. Sai kuma ta maida kan Mahma, “Addah to in hakane muyi kwanciyarmu anan ɗin kawai basai yayi wahalar da kike gudar masanba..”

     “Bazai yuwuba, tunda dai ga gida can da zamu zauna mu kaɗai bamu takura kowa ba, ba’a takuramu ba, can zamuje. Abdul-Mutallab ɗauketa”.

     Yanda Mahma tayi maganar babu wasa a ciki ya sakashi zura wayarsa aljihu ya tako a hankali inda Mammah ke rungume da Farah. Ɗaukarta yay cak ya fita da ita duk da nauyin datai masa saboda yanda jikinta ya saki sosai. Duk yanda Mammah keta kumbure-kumbure Mahma batabi takantaba ta tasasu gaba suka fice suma. Dan ita aunty Zakiyya ma ta ƙagu subar nanɗin dama suje inda takeson amayar da abinda ke a bakinta.

      Aunty Zakiyya ce ta jasu. Suna ficewa daga gidan AK yaɗan lumshe idanunsa da murza goshinsa yana furzar da huci. Sai kuma yay murmushi da girgiza kansa saboda harar da Mammah keta faman antaya masa da gargaɗi da idanu.  

       Juyawa yay zuwa cikin gidan dan shima wani ma zazzaɓi-zazzaɓi ke neman rufesa, sashen Farah ya koma ya kashe komai da maida ƙofar ya rufe, koda ya fito sashensa ya nufa dan yafi buƙatar watsa ruwa a yanzu.  

      ★★★

    A ɓangaren Zinneerah kam kuka taci sosai, sai da Mahma ta leƙo tai mata sallama akan suma zasu wuce, ta kuma ɗan lallasheta da ƴar nasiha sannan ta sassauta. Fitsarin da takejine ya sakata tashi dole ta shiga toilet ɗin ɗakin tayo, tana fitowa ta sake komawa saman gadon ta kwanta dan zazzaɓi takeji yana neman rufeta ga ciwon kai. Ba tare data damu da cire komai ba ta kwanta a haka dajan bargo ta lulluɓa har kanta saboda sanyi da takeji yana ratsata. Ga kuma ac a ɗakin dake aiki ta kasa kashewa.

        Batafi mintuna goma da kwanciyarba barci ya kwasheta sama-sama. A ɗan firgice ta farka saboda ƙarar buɗe ƙofa da taji, ta ƙanƙame jikinta waje guda jin tabbas mutum ne ya shigo. Sai dai ta kasa ko motsi saboda yanda zuciyarta ke wani harbawa da sauri sauri na tsananin tsoron wanda zataci karo da shi a matsayin mijin nata.

      AK da tun shigowarsa ɗakin idanunsa suka fara sauka akanta ya cigaba da takowa cikin ɗakin a hankali sassanyan ƙamshin turaren wutar da ɗakin yaji, da ƙamshin sabbin furnitures dana fenti na rige-rigen shiga masa hanci, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana ƙarasawa gaban gadon sosai. Hannayensa ya tura duka biyu cikin aljihun wandon blue pyjamas ɗinsa har lokacin idanunsa akan Zinneerah dake ƙudun-dune cikin bargo zuciyarta na nemam faso ƙirjinta ta fito.

       “Assalamu alaiki”. Sassanyar muryarsa ta daki cikin kunnuwanta. Sosai ƙirjin Zinneerah ya buga fiye da farko, dan idan har babu kuskure ai muryar Yayansu taji kam. ‘Kai ina ganganne’ ta ayyana a zuciyarta dake raunana.

       “Nasan ba barci kike ba”. Ta ƙara tsinkayar muryar tasa a karo na biyu, a yanzu kam kasa jurewa tayi dole tai ƙasa da bargon a hankali daga saman fuskarta. A hankali ta buɗe idanunta zuciyarta na gudu dai-dai da jinin jikinta dake tsinkewa daga cikin jijiyoyinta. A wani irin firgice ta yaye bargon babu shiri tana miƙewa zaune jikinta na rawa. “Y…y….Yayanmu!”.

      Ta faɗa da wani irin kiɗimammiyar murya dake nuna tsantsar tashin hankalinta a fili. Sosai yanda tayi ɗin ta bashi dariya, amma sai ya daure ko ɗigon fara’a babu a fuskarsa, sai dai idanunsa kafe suke a kanta ko ƙyaftawa bayayi yana ƙarema ƙwalliyar tata kallo, dan zaburar da tayi ta saka lafayar warwarewa daga saman kanta zuwa jikinta. Sai baƙar rigar jikinta mai dogon hannu data lafe da bayyana  ainahin surarta da gyaran da fatarta ta samu wajen hajiya Falmata.

           Janye idanunsa dake binta da kallon yayi yana maidawa akan fuskarta, ganin yanda take ɗan ja baya da rawar jiki laɓɓanta na rawa alamar sonyin magana ya sakashi lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta yana zare hannayensa daga aljihun wandon barcin nasa. Cikin nuna rashin damuwa da yanayin nata ya kai zaune a bakin gadon yana facing ɗinta. Hannunsa ɗaya yakai akan goshinsa yaɗan shiga murzawa. Sai kuma ya ɗago ya dubeta da birkitattun idanunsa dake rikitata, batare da yace uffanba ya miƙa mata hannunsa ɗaya alamar tazo.

     Kanta ta shiga jujjuyawa tana ƙara nanema fuskar gadon, hawaye na gudu a saman fuskarta kamar an buɗe fanfo. “Yayanmu dan ALLAH kace bakai bane ba”. Ta faɗa cikin tsananin rauni da rawar harshe.

      A karan farko ya ɗanyi luuu da idanunsa da sakin guntun murmushin da ita ko alamarsama bata ganiba, ya ɗan ƙara ware idanunsa a kanta da kai hannunsa ya shafi sajensa dake a kwance luf duk da ba gyaransa yay ba, dan koda yay wankan ma turare kawai yasa da kayan barci ya fito domin dubata. Cikin muryarsa ta rashin sakewa yace, “Bani bane mi?”.

       Cijin suɓucewar baki Zinneerah tace, “Miji!, mijin da aka kawoni gidansa matsayin matars…….”

     Ta kasa ƙarasawa saboda yanda yay bala’in kafeta da idanunsa masu cikar gashi da kwarjini. “Ban cancanta bane?”. Ya faɗa yana cigaba da tsatstsareta da idanu.

    Babu shiri tai ƙasa da kanta kuka na sake kufce mata. Kansa ya ɗauke daga kanta jin wayarsa na vibration, hannu yasa ya cirota daga aljihun wandon barcinsa yana jan guntun tsaki alamar baiso shigiwar kiranba dai. Sai dai ganin Number aunty Zakiyya ya sakashi yi kamar bazai ɗagaba sai kuma ya ɗaga ɗin batare da yayi magana ba.

      Cikin sake fusata daga can Mammah tace, “Abdul-Mutallab nasan kana jina”. 

     Runtse idanunsa yay da cije lip ɗinsa na ƙasa. yay ƙoƙarin daidaita kansa wajen faɗin, “Am sorry, bansan ke bace ba”.

       “Ai yanzu ka sani, na kiraka ne na gargaɗeka, wlhy ka taɓa musu yarinya sai ranka yay mummunan ɓaci, dan nayi alƙawarin wannan auren sai na tsinkashi wlhy, saboda haka karma ka ƙwaɗaitama kanka abinda zai dameka daga baya na faɗa maka”.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button