MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 60

*Page 60*

………..Fitowa tai da sanɗa kanta a ƙasa saboda tunani da kunyar su Granny da take zaton har yanzu suna gidan. Yayinda AK dake zaune a falon shi kaɗai 

yana latsa waya mayataccen ƙamshin haɗin khumrah ɗinta ya samu nasarar kaiwa ga hancinsa. A hankali ya ɗago yana kallon sashen ƙofar bedroom ɗin nasa 

zuciyarsa na wani motsawa a cikin ƙirji.

       A kan laɓɓansa ya ambaci kalmar “Mash ALLAH” yana wani lumshe idanunsa. Ganin tana nufar hanyar fita da sanɗar da takeyi ya ɗan murmusa, sai da ta 

ɗan gotashi yace, “Nan zaki zo ai”.

         Ina ƙasa Zinneerah ta shige dan kunya, har mamakinsa take ganin shi ko’a jikinsa tamkar bai aikata wani aika-aika ba. 

      “Kona taso?”.

Taji ya sake ambata. Kafinma ya gama rufe baki ta nufosa dan shi ba abin wasanta bane, abinda ya shiga tsakaninsu kuma bai rage masa kimarsa da girmansa a 

idanuntaba sai ma ƙaruwa da yayi. Ta ɗanji sanyin ganin babu su Granny, dan haka taso kaiwa tsugunne gabansa.

          Bai motsa daga kishin giɗar da yay a kujera yana mata kallon ƙasan ido ba, ya kamo hannunta ganin zata tsugunna. A saman cinyarsa yay mata 

masauki. Hakan ya sata saurin kallonsa. Da wannan damar yay amfani wajen riƙe idanunta cikin nasa. Duk yanda taso ta janye ta gagara. Sai neman kashe mata 

jiki yake da wani sakaltaccen kalo dake tada mata tsigar jiki. Babu shiri idanunta suka fara tara hawaye.

       Karan farko tun shigowarta falon guntun murmushi ya bayyana a fuskarsa, ya lumshe ido ya buɗe a kanta yana kamo fuskarta cikin tafukan hannunsa. 

“Miyasa ke raguwane?.”

      Cikin suɓutar baki tace, “Tsoro kallon yake bani”.

      Harga ALLAH ta bashi dariya, duk yanda yaso danneta kar yayi kuma hakan bai yuwuba, sai gashi da sakin murmushin da har haƙwaransa na bayyana. Shagala 

tai da kallonsa dan tabbas murmushi na masa ƙyau musamman wanda ke bayyana haƙwaransa irin wannan. Nisan da tai a nazari yasa harya iso da fuskarsa gab da 

tata bama ta saniba. Sai jin saukar laɓɓansa kawai tayi akan nata. Duk yanda taso ta nuna zamewa hakan ya gagara. Dan wani irin sallo da tunda uwarta ta 

haifeta ba’a taɓa mata shiba yake sarrafa lips ɗinta.

        Luf tayi tana amsar rikitaccen karatun na babban yaya data fara haddacewa daga safiyar jiya zuwa yau. Sai da ya tabbatar ya ida zubar da ɗan sauran 

ƙarfin data samu sannan ya barta yana rungumeta a jikinsa gaba ɗayanta. Yanda yaken sauke numfashinsa mai sanyi da nutsuwa a cikin kunnenta yasata sake lafe 

masa a jiki tana rumtse idanu. A ranata ko rayawa take, ‘Yayanmu zaka kasheni da wannan salon naka da yafi ƙarfin shekaruna’.

       Sun kai kusan mintuna uku a haka kafin ya ɗagota yana kallon fuskarta, duk yanda yaso su haɗa ido yanzun kam taƙi yarda. Yatsunsa biyu ya sa ya ɗago 

haɓarta, bai damu daƙin yarda su haɗa ido da taiba. 

        Tana bashi dariya da ƙara birgesa da wannan sanyin nata, dan haka yay wani munafukin murmushi da kamata ya miƙar.

        Dining suka nufa yana riƙe da hannunta, sai da ya zaunar da ita sannan shima ya zauna. Da kanta ta miƙe ta haɗa masa abincin yanata faman binta da 

fitinannen kallon nan nasa dake sakata dabircewa komin jarumtar da taso nunawa.

     Shiko fahimtar da yay kallon nasa na mata tasiri tunma suna can gidan yake sakashi kasheta da su. Bata zuba nataba, bai kumayi maganaba, sai da ta gama 

ta koma ta zauna ta ɗan dubesa. Ganin shima dai kallon nata yake ya sata janye nata idanun gefe.

       Komai baice mataba ya fara cin abincin, sai da yay nisa da ci sannan yay magana batare daya kalletaba. “Juyo nan”. 

      Juyowar tai tana fuskantarsa, sai kawai yay mata alamar ta buɗe bakinta. Ganin yanda fuskar tasa take ya sata buɗewar. Daga haka ya cigaba da ciyar da 

ita yana ci shima har suka cinye. Godiya yayma UBANGIJI yana miƙewa ya barta a wajen. Hakan ya sata miƙewa itama ta tattare kayan a basket ɗin da aka kawo, 

sam batajin daɗin jikinta, a yanzu haka tafi buƙatar ta samu waje ta kwanta. Sashen ta bari baki ɗaya zuwa nata, tana shiga ta sauke ajiyar zuciya da nufar 

kitchen. 

      Tana cikin wanke kwanikan ya shigo kitchen ɗin, waiwayowa tai ta dubesa. Ya canja kayansa zuwa shadda fara tas da tai masa tsananin ƙyau, ga 

mayataccen ƙamshinsa mai cika hancin mai shaƙa da bashi nutsuwa. Ya ɗan janye idanunsa daga kanta yana kallon agogon hannunsa. “Bara na gaishe da su Mammah 

kina buƙatar wani abu ne?”.

          Duk da tayi mamakin jin zancen Mammah sai batace komaiba taɗan girgiza masa kanta. 

     Takowa yay gabanta yana ɗago fuskarta suka kalli juna. “Baza’amin addu’a ba?.” ya faɗa a wani irin sanyin murya.

        Tana mamakin a yanda ya iya sarrafa yanayinsa a salo daban-daban, kuma duk cikin kame kansa babu wani rawan kai ko gaggawa tattare da shi. Idan 

badan ita da take ganin true color ɗinsa a tsakanin jiya zuwa yau ba babu wanda za’a faɗama haka yake ya yarda, dan ko’ita idan yay abu ya basar sai take 

ganin tamkar ba shine ya aikataba. Ya barta da kunya shiko ko’a jikinsa…….

       “ALLAH ya tsare ya dawo da kai lafiya Yayanmu”.

     Haɓarta ya saki da tura duka hannayensa a aljihunsa yana kallonta,  “Har yanzu matsayin Yayan kawai gareni?”. Ya faɗa yana tsatstsare ta da idanunsa 

masu kaifi a gareta.

        Ɗan ɗago idanu tai ta kallesa, ya wani juya mata nasa manyan idanun yana ƙara tsuke fuska.

      “Yanzu ni waye a wajenki?” 

  Ya faɗa cikin muryarnan tasa ta rashin sakewa.

     Mamaki tambayar tasa ta bata, da ɗan rawar murya da kunyarsa ta haifar mata tace, “Yayanmu!”.

      “Daga nan fa?”.

    Duk da ta fahimci abinda yake son jin sai ta noƙe dan itama ɗin dai gwanace a miskilancin. 

      “Zaki magantune”. Ya faɗa yana sake kallon agogonsa da juyawa zai fita. Jitai duk babu daɗi, 

      “Kayi haƙuri idan na ɓata maka rai Yayanmu”.

        “Ba haka matata ke bani haƙuri ba, dan haka sai ki shirya ta yanda nafi buƙata kafin na dawo”. Ya faɗa yana ficewa batare da ya waiwayota ba.

         Kallo ta bisa da shi zuciyarta na maimaito mata karatun hajiya Falmata daki-daki. Ganin tunanin bazai kaita ko inaba ta cigaba da aikinta cikin 

dauriya dan wani sabon zazzaɓi ke neman saukar mata, ga wajen itakam har yanzu zafi yake mata kaɗan-kaɗan. Duk da yanda take jin nata haka tai juriyar gyara 

gidan har sashensa, sauƙintama ba wani datti bane. Turaren wuta ta saka har General falo da ƴar barandar waje. Ta bi kuma da fresheners masu daɗi. Sosai 

nutsuwa ta ƙara saukar mata jin ko’ina ya ɗauka ƙamshi kamar yanda take buƙata. Daga haka ta taƙarƙara ta koma bedroom ta kwanta kozata samu barci ya 

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button