MADADI 1-END

MADADI Page 1 to 10

*NAJA’ATU UMAR ABBALE*

 ~~~~~~~~~~~~~

 *1

“Innalillahi wa’ina ilaihi rajiun.”! Abinda Baba Talatu tafad’a kenan ta kalli Saddiqa dake gefe a tsaye tana hawaye tace” Yi sauri ki d’ebo ruwa suma tayi.” Saddiqa ta futa daga d’akin da sauri, karo suka ci da Baba Malam da Babban d’ansa   Alhaji Magaji.” Baba  Malam yace.”

 wato dai har yanzu Kuka kuke yi ko da alama dai kuna so   ku hana Halima  ta kwanta lafiya a kabarin ta.” Tana girgiza kai had’e da ‘kokarin mayar da hawayen idonta tace”Baba Malam mun daina kuka Yaya Naja’atu ce tafad’i ta  suma   shine Baba Talatu tace na d’ebo ruwa.” Da sauri Baba Malam da Alhaji Magaji suka shiga d’akin. ita kuma ta futa da saurin gaske, ruwa ta d’ebo cikin kofi ta shigo d’akin dashi.

Baba Malam dake tsugune kusa da Naja’atu yana mata addua ya kar’bi ruwa ya shiga yayyafa mata a fuska, Baba Talatu hawaye kawai take sharewa tana girgixa kanta.

Baba malam sai da ya yayyafa mata ruwan sau uku sannan ta saki wata ajiyar zuciya mai kar’fi! idanunta ta shiga kiftawa, sai ta mi’ke zaune da sauri ta shiga rarraba idanunta a kansu.

Baba Talatu ta ri’ke hannunta tana fad’in “Naja’atu  kiyi hakuri kada ki jazawa kanki lalura.” Ihu! ta zumduma! tasa hannu ta toshe kunnuwanta jikinta na wata iriyar kyarma!  tace”Baba Talatu kunnuwa ba zasu iya d’aukar wannanmaganar taki ba! a ina aka ta’ba haka *Uba ya Auri ‘Yarsa* ashe dama dake da Baba malam dashi kansa Abban nawa  dukkanin ku maguzawa ne ku baku san addin……..Kafin ta ‘karasa Alhaji Magaji ya kwad’a mata mari! yace.”Ke ki nutsu ki shiga hankalin ki bama son shirme da shashanci ki saurara ayi miki bayanin yanda al’amura suke.”

A zabure! ta mi’ke tsaye! kamar wacce zata tada iska tace”Baba Magaji ni bazan fuskanci komai ba  ba kuma zan nutsu ba, saboda ni ba kafura bace wallahi sai na kashe kaina idan kuka d’aura min aure d Ubana, wai baku ji sunansa bane Abban Naja’atu fa sunansa amma shine zaku daura mun aure dashi! to dukkaninku sai na kaiku *Hizbah!.* Ta’karashe maganar tana wani irin kuka mai cin rai.

Baba Malam ya goge guntin hawayen idonsa ya ri’ke hannunta da fad’in “Auta zauna ni da kaina zan warware miki abunda baki sani ba.” Fuzge hannunta tayi tana ‘kokarin tsallakeshi ta wuce! Alhaji Magaji yayi sauri tare mata hanya Yace.”Naja bakya jin magana ko? To shikkenan idan baki  kaimu *Hizbah* bakya ‘kaunar Allah.” Yafad’a babu wasa a tare dashi.

Hannunsa ta ri’ke jikinta sai mazari yake tace”Abba Magaji ka duba maganar nan da kyau fa! Kayi duba na tsanaki!  ya za’ayi dan kawai Mamanmu ta mutu sai suce zasu d’aura min aure da Ubana wace irin rayuwa ce wannan.”!!! Tafada cikin wani irin sauti!! Shima a fusace! Yace.”Wai ke waye ya fad’a miki Alhaji Abbas Ubanki ne.”!? Shuru tayi tana binsa da wani irin kallo! bakinta sai rawa yake yi.  da kyar ta iya bud’e bakinta tayi magana…..”Baba Magaji bangane maganar ka ba.”! murya na rawa tayi maganar, Baba Malam ya zaunar da ita kusa dashi hannunsa cikin nata ya rike sosai yana kallonta, tausayi take bashi sosai, tabbas yasan dole ne ta shiga rud’ani da tashin hankali sakamakon bayyanuwar abinda yake rufe tsayin shekaru goma sha shida!  da suka wuce.  Wanda ta d’auka a matsayin mahaifinta dashi ake maganar d’aurin aure a tsakaninsu, babu shakka  duk wanda ko  yaji   wannan lamarin dole ya shiga halin d’imuwa da tashin hankali

‘Dakin ne yayi shuru na tsayin mintina uku kowa jikinsa yayi sanyi mussaman Naja’atu wacce take jin wata irin fargaba da fad’uwar gaba, tunda Abba Magaji yayi furucin cewar ba Abba Abbas ne mahaifinta ba  take wata zabura tana rarraba idonta a kansu bakinta motsi kawai yake tana so tayi magana amma ta rasa me za tace! fashewa tayi da wani kukan tana kallon Baba Malam da kansa yake sunkuye sai zufa yake gogewa, tace”Baba malam kuna so nima na mutu ko? kuna so kamar yanda kuka rasa mamana nima ku rasa ni ko ? zuciyata daf take data daina aiki sakamakon bala’in da kuka jefata a ciki! Baba Magaji yace wai Abbana bashi ne Ubana to shikkenan sai ku fad’a min wanene ya haifeni.”? Murya na rawa ta ‘karasa maganar.

Baba Malam ya d’ago kansa a nutse yace.”Naja’atu Nine Ubanki ni na haife ki Alhaji Abbas Uban ri’kon ki ne kuma miji ga ‘yar uwarki Halimatu.” wani irin kallo ta shiga yi masa tana girgixa kanta sai hawaye ya wanke mata fuska! murya a sanyaye tace”Baba malam ya akayi haka? ya kuka yi mun wasa da hankalina? ni ban yarda kaine mahaifina ba, Abba Abbas shine Ubana shi na sani tunda na taso shine yaci dani yasha dani ya tufartar dani ya tsaya a kaina nayi karatu kuma shi nake so ya aurar dani ga mijin dana za’bawa kaina.”! Ta’karasa maganar cikin yarda da abinda take fad’a.

Abba Magaji ya fusata! sosai ya bud’e baki zaiyi magana Baba malam ya d’aga masa hannu yace.”Kada kayi mata tsawa ko ka hantare ta, dole ne dama haka ta kasance da ita damu bakid’aya, ha’kika mutuwa itace ta janyo mana wannan tashin hankalin dan da Halimatu na raye to babu shakka Naja’atu zata cigaba da zama a matsayin ‘yar data haifa alhalin kuma ‘kanwa take a gareta, Yanzu zamu bari ta nutsu tukkuna zuwa dare sai mu sake wani zaman domin mu sanar da ita abinda ya faru a baya wanda bata sani ba.” Abba Magaji ya sauke ajiyar zuciya a nutse yace.”Shikeenan Allah ya za’ba abinda yafi alkairi.” Baba Malam ya amsa da amin kana ya mi’ke suka futa a tare.

Suna futa, Naja’atu ta kalli Baba Talatu tace”Baba dan Allah dan annabi kada ki bari al’amarin nan ya tabbata, ke macace ce mai hankali da sanin ya kamata kuma kina zuwa isilamiyya kin san dai haramun ne Uba ya auri ‘yar sa ko.”? A zauce! take maganar.

Baba Talatu tace”Naja’atu Alhaji Abbas ba Ubanki bane an fad’a miki Mijin Yayar ki ne Halimatu Allah ya ji’kanta, Alhaji Abbas kinga wacce ya haifa nan ita da ‘yan uwanta su Mussadiq.” Ta nuna mata Saddiqa dake zaune a kusa da ita.

Wani irin kallo ta shiga binsu dashi tana girgiza kanta, ta rasa a’ina zata ajiye wannan babban al’amari a cikin zuciyarta, *Abbah Abbas* ba shine ya haife ta ba *Baba malam* ya haife ta? anya kuwa da gaske suke wannan maganar ko dai kawai suna so bukatarsu ta biya ne gurin ganin sun d’aura mata aure da *Ubanta* tabbas dole ne ta nemawa kanta mafita dan ita kam bata yarda da wannan maganar da suke ba.

Tana kallon Baba Talatu da Saddiqa suka suka futa daga d’akin, ta shiga girgiza kanta tana masifar mamakin a’lamarin, kwanciya tayi kan tabarmar dake shimfid’e a dakin ta shiga tunano rayuwar ta ta baya tare da mutanan data dauka a matsayin iyayenta.

*????️MADADI!!!????*

 _(Ba Haram Bane!!!)_

*NA*

*BINTA UMAR ABBALE????*

~~~~~~~~

*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION????????️*

_’Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi._

~~~~~~~~

~~~~~~~~

*SADAUKARWA GA DUK WANI A HALINA DAKE CIKIN WANNAN UNGUWA♥️*

*2*

*’Kofar Na’isa* Unguwa ce mai cike da d’umbun tarihi, duk wanda ya kwana ya tashi a cikin birnin kano ya san da zaman unguwar. ‘kofar na isa unguwa ce ta malamai masana addini da kuma ‘yan boko masu aiki da iliminsu,  duk wanda yake mu’amula da d’an cikin unguwar zai gane cewar suna da wani irin quality wanda Allah yayi musu,  saboda sun iya mu’amula da mutane sosai! akwai masu kudi a unguwar akwai marasa karfi a ciki, dai-dai gwargwado masu rufin asirin dake cikin unguwar suna taimakawa marasa shi mussaman da azimi suna hidima sosai da sosai da wuya kaji ance maka ga wata hatsaniya ta tashi a unguwar irin ta *Daba!* ko kuma *Sace-sace* dai-dai gwargwado suna bawa yaransu tarbiya had’e  da ilimin addini dana boko! 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button