MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 60

ɗauketa kafin sallar la’asar.

      Tana kwanciya ana fara knocking, dole ta miƙe kamar zatai kuka. Hijjab ta saka sannan ta fito ta buɗe. Ganin su maman halima yasa fara’arta bayyana 

tana jera musu sannu da zuwa. Suma cike da kulawa suke amsa mata suna shiga da kayayyakin da sukazo dashi. Akwatinanta ne na lefe da tarkacen ƴan kayayyaki. 

Sai kayan gara da suka bata mamaki. 

      Naziru daya kawosu ne yace ta buɗe ƙofar kitchen ta baya a saka tacan zaifi sauƙi. Dan yasan hanyar tunda da shi aka kawo furnitures ɗinta. Cike da 

girmamawa ta karɓa masa. Taje ta buɗe ƙofar shi da maigadi suka dinga jigilar shiga dasu su Sakina na tayasu da wanda zasu iya. Hardasu kayan cin-cin. Jitai 

ƙwalla ya cika mata ido najin daɗi da tausayin su baba. Iyaye dabanne, duk da sunsan babu abin AK ɗin ya rasa a rayuwarsa sunyi hoɓɓasa ɗin ganin sun cika 

mata darajarta akan abinda al’ada ta tanadar. Dan dai gara al’adace da ƙyautatawar iyaye ga miji bawai wajib bace kamar yanda samarin yanzu suke kallo, 

harma suke samun damar yarfa mace in ba’ai mataba saboda son zuciya.

       Sai da aka gama shiga da komai sannan ta kawo musu ruwa da lemo sukai zaman gaisawa. Sakina sai kalle-kalle take da jinjina wannan gida a ranta, duk 

da da ita aka kawo amarya yau dai tafi kallon komai yanda ya kamata dan shiyyasama ta nace sai tazo. Aiko sai gashi ƙiri-ƙiri tana nuna hassadanta a fili 

dan sai wani yamutse-yamutsen fuska take ita da uwarta dake ji kamar ta fidda Zinneerah ɗin ta kawo sakina ciki.

      Ita dai Zinneerah bama bi takansu taiba, dan akwai sauran ƴan ɗan musa da sukazo tare su uku sai maƙwaftansu mmn sadiq ɗin abokan arziƙinta suma su 

uku, sai ƴaƴan mmn halima da ita, da matar Naziru.

       Kasancewar su mmn halima tsaffin mata ya sasu fahimtar yanayin Zinneerah ɗin, sai mamaki ya kama irinsu mmn sakina da matar Naziru da ita kanta mmn 

Haliman dan sudai sunsan Zinneerah ba wannan ne aurenta na farko ba, tunda gata harda little. To amma yanayin nata yayi kama da na wadda namiji ya fara 

taɓawa. Sauran kam dai har ransu gani suke Zinneerah ta kawo mutuncinta, musamman ma ƴan dan musa da babu wanda yasan ƙaddarar data afku ga Zinneerah ɗin 

har yanzu. Duk da kuwa Inna Asabe ta saki maganganu da sukaje danya sai duk suka kallesu matsayin hassada kawai da sharrin baƙin kishinta da bai ɓoyuwa 

harga ƴaƴa. Sai da suka shiga ko ina suna mai yabawa da jera addu’oin fatan alkairi.

★★★

       Koda Mahma ta koma gida bata yarda ta nunama su Mammah komaiba, hasalima dama basusan inda tajeba. Da sukace zasuzo gidan AK ɗin kuma cikin dabara ta 

hanasu akan su bari sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sai a maida Farah baki ɗaya dan ya kamata takoma ɗakin mijinta tunda ta samu sauƙi.

     Da farko Zakiyya ta tubure akan Farah bazata komaba har sai AK ya saki Zinneerah, zuwa lokacin Farahn ta haihu. Kallonta kawai Mahma tai tana gitgiza 

kai da sake yarda da zancen AK. Kamar zatai magana akan cikin Farah ɗin sai tai musu shiru kawai. Dan ita Farah ɗince da kanta tace zata koma gidanta saboda 

tunowa da zafafan gargaɗin AK. Ba aunty Zakiyya da Mammah ba hatta Mahma sai da tai mamakin furicin na Farah, amma sai batace komaiba tai murmushi kawai.

     Aunty Zakiyya kuwa wani shegen harara ta watsa mata da faɗin “Saiki koma ballagaza kawai mayyar miji”.

     Kaucewa dukan nata tayi tana kumbura baki, dan ita dai wlhy shawarar Adilah da sukai waya jiya da daddare zatabi, gara ta koma koma mi za’ayi ayisa 

acan.

★★★

     Hajiya iya kuwa data koma duk da tana fushi da Uncle Ahmad har yanzu taƙi saurarensa dan ta dage sai ya ƙara aure ya ajiye matar a Nigeria koda zata 

barsa ya koma. Kokuma ya bar iyalansa anan. Wannan shine zaɓin data bashi kawai ta tsuke bakinta.

      Zaunar dasu tai shida Baffah da Mommy ta sanar musu komai daya faru. Baffah dai yasha mamaki wannan al’amari, Uncle Ahmad kuwa da dama gaba ɗaya 

hasashensa da nazarinsa ya tafi kacokan a wajen ne tunda Baffah ya bashi labarin abinda ya faru da tarihin Zinneerah sai baiji komai ba sai takaici da 

tausayin Zinneerah ɗin.

        Cikin zafinsa yace, “Aiko indai ta tabbata sune suka aikata yanda sukai wasa da rayuwar yarinyarnan suma tasu saita shiga garari wlhy, dan bazamu 

barsuba sai inda ƙarfinmu ya ƙare. Gatan da suka kalleta da tashinsa a farko har suka aikata mata wannan ta’asar zasu tabbatar da tunaninau gurɓatacce ne 

kuwa”.

       Ɗari bisa ɗari duk suka bashi goyon baya. Suna cikin tattauna yanda zasu ɓulloma al’amarin Khalipha ya shigo gidan, shine ya musu ƙarin bayani akan 

kamo hajiya lanti da sukai a yanzu haka kuma tana hannun hukuma, Alhmdllh kuma ta bada haɗin kai akan cewar zata sadasu da hajiyar data kaima su Zinneerah 

dan itama saboda ita taje katsina. Amma sai ta tarar tana saudia dan can ta koma da zama. dama can sana’arta kai yara saudia aikatau, duniyace tai mata 

gwatson ƙyanwa tunda aka cimimiyota ta dawo kuɗin komawa ya gagareta. To yanzu dai Alhmdllh akwai bikin yaronta da akai a wannan satin rana ɗayama da nasu 

Zinneerah, itama jira take a gama bikin dama ta sameta dan tazo Nigeria. 

       Sunji daɗin jin hakan, a take suka yanke zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu itama a damƙota kawai kafin ta sake tafiya, suma kuma su Mammah karsu bar 

ƙasar.

        A wannan tattaunawar AK da yazo gidan gaishesu ya samesu. Zama yay suka ɗan ƙara tattauna zancen sannan ya shiga ya gaida matan gidan. Daga haka ya 

ɗauka little daya maƙale masa suka wuce gida dan sai da ya fara zuwa ya gaishe dasu Mammah. Acan ɗinma bai nuna musu komaiba, dan koda Farah tace zata koma 

gida gobe a taƙaice yace mata, “Ƙofa abuɗe take”  daga haka yaja bakinsa ya tsuke. Bai kuma bi takantaba harya baro gidan. Aunty Zakiyya kam bata tanka 

masaba shima bai tanka mataba dan idan taurin kai ne gidan ta taras.

______________________

      *_DANYA_*

    Ƴan biki sun dawo gida lafiya, yayinda kowa ya fara ƙoƙarin fesar da maganar daya gumtso akan auren na Zinneerah da daular duniyar da ALLAH ya kaita 

ciki. Ga miji ɗan gaske acewarsu (????ba bily ba????). Wasuma da biyu suke ƙara kambama zancen dan baƙanta ran Inna data haukace musu da bala’in su fice mata a 

gida.

           Ko’a jikinsu, dan da suka fitanma gaba suka ƙara wajen isar da labarai kala-kala harda waɗanda ba’ayiba ma. Gasu Yaya Gajeje kuwa ga labarin a 

ransu ga tsoron tunkarar Inna da batun abinda suke hasashe tattare da Tinene, dan tunda suka shigo gidan ɗaki ta shige ta ƙudundune a zani tana rawar sanyi.

      Da ƙyar Yaya Gajeje taja ƙafafunta ta nufi gidan saboda yara data bari, gashi yamma nayi tunda tana ƙauyen gaba dasune duk da babu nisa.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button