MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 60

     Duk da takaici da zafin da inna keji a ranta da labarin ɗaukakar da Zinneerah ta samu hakan bai hanata zaman jin labari a bakinsu Atine dakeyi suna 

gatsine-gatsine ba kishi fal ransu. Abinda kuma sukazo dashi sai faman ci suke har Inna ɗin dan tace raba mugu da makami ibada ne..   (????????gaskiya kam aunty 

Asabe)

      Shi Baba ma da amaryarsa dake jiyosu daga ƙofar ɗaki dariya suka basu, musamman Inna da baba yasan shegen kwaɗayinta bazai barta ta kasa cin abinda 

akazo da shi dinba koda kuwa tanaci tana kuka ne.

     Washe gari da safe jikin Tinene ya ƙara tsananta, tun dare taketa kwara amai har safiya ta tashi a galabaice. Baba ya ce ta shirya suje asibi maybe dai 

typhoid ne ke damunta, dan itace kesa zazzaɓi mai zafi haka da naci. Amaryar baba ba sanin ciki tai ba sosai, Inna kuma idanunta ya rufe da damuwar ɗaukakar 

Zinneerah sam taƙi fahimtar halin da Tinene ke ciki. Su kuma su Karima tsoron faɗar abinda ransu ke raya musu inna ta hau tsinarsu sukeyi.

     Ana haka sai ga Gwaggo Laritu tazo domin ai zaman raba alkairin da AK ya basu, bata jima da zama ba Yaya Gajeje ta iso itama. Cikinsu babu wanda yay 

magana akan shirin kai Tinene asibiti da baba ke shirin yi. Sai da Gwaggo Laritu tai wani tunani sannan tai magana.

       “Niko Yaya nakega kai Tinene asibiti bazai jawo komai a garin nanba sai kace nace. Musamman ma daya kasance asibitin garin nan zakuje”.

     Da mamaki baba yace, “Kace nace kuma Laritu, akan ciwon?”.

     “Tabbas kuwa Yaya, dan banga amfanin aita ɓoye-ɓoye ba akan abinda kowa yasan dama wajib ne. Dan shi dai sharri ɗan aike ne dama shiyyasa ake nusar 

damu illarsa ga aikama kowa. Asabe tama Zinneerah fata kuma ALLAH ya karɓa mata, sai dai kuma ga sakamakon nan ya dawo ga Tinene. Dan babu wani taifot dake 

damunta ciki ne jikin wannan yarinyar wlhy”.

    Ba baba da amaryarsaba hatta da Inna dake jiran Gwaggo Laritu takai ƙarshe ta sauke mata kwandunan bala’in da take Tattarowa a take ta saki robar ruwan 

wankan ƴar Karima data ɗauka zata sako ruwan zafi, ALLAH yasotama bata kai ga zubawarba.

      Wani irin shuuu taji abu ya gitta mata cikin idanu da ƙwaƙwalwa saboda tsabar razani. Cikin rawar baki tace, “Munahika annamimiya, Laritu kirasa wanda 

zakima wannan sherin sai ɗiyar zumunki. To wlhy sai dai kiga ciki a jikin jikokinki, ALLAH ya isa kuma sherin da kikaima yarinyata”.

     Murmushi kawai Gwaggo Laritu tayi. amma uffan bata sake cewa ba. sai Yaya Gajeje ce tace, “Inna ya kamata ki fahimci zancen Gwaggo, ku kuma nutsu wajen 

karantar Tinene wlhy cikine da yarinyar nan da gaske”.

        Baki sake tabi Gajeje da kallo, sai jitai Atine tace, “Wlhy Inna da gaske ne, ki kalla Tinene da ƙyau zaki tabbatar”.

         Tsitt gidan yayi saboda kakarin aman Tinene, Inna ta fashe da kuka jikinta na wani irin rawa lokacin da idonta ya sauka akan Tinene da har ciki ya 

fara tasawa sama kaɗan, da alama ma ya wuce watannin da suke hasashensa. Baba kansa baya yay sai da amaryarsa ta riƙosa jikinta na rawa itama dan batason 

damuwa sam, musamman ma yanzu data samu cikin nan. Kafin wani ya samu damar sake cewa uffan sukaji ana rangaɗa sallama daga waje. Da ƙyar baba ya iya amsawa 

da nufar hanyar ƙofar gidan domin duba wanene. Da Laminu ƙanin Babawo yaci karo, Laminu ya gaishesa da girmamawa yana miƙa masa takardar hannunsa da nuna 

masa kayan daya sauke a mashin ƙasa. “Baba Sule gashi inji Yayana Babawo, yace a bama Karima tare da waɗan nan kayan. Yace a sanar mata ta tuna yau saura 

sati biyu wa’adin da kotu ta bata na kai kuɗin sarƙar hajiyar data satamawa ya cika”.

     Cikin rashin fahimta baba yace, “Laminu ban fahimcekaba nikam sam, amma kaga shigo daga ciki kai bayani agaban Karimar”.

    Babu musu kuwa yabi baba ciki, bayanin daya zayyana masa shiya sake maimaitawa Karima.

    Gani kawai sukai ta saki ƴar sai da Atine tai azamar tarota tana ambaton, “Na shiga uku Karima baki da hankaline?”.

    Ina Karima ba saurarenta takeba, dan atakema gani sukai ta yanke jiki ta faɗi, Inna ma da tun fara bayanin garin ke juya mata da wata irin hajijiya sai 

tabi bayan Karima ta zube ƙasa.

     Ƙarar da Atine da Sa’a suka ƙwalla na firgici ya saka amaryar baba dafe bango saboda wani irin murɗawa da mararta tayi alamar tahowar naƙuda………

____________________

    *_KANO_*

  Bayan wucewar su mmn Halima

salla kawai Zinneerah ta samu tayi ta la’asar. Duk yanda taso daurewa da zazzaɓin daya rufeta kasawa tai, dole ta rrrafa saman gado ta kwanta dajan bargo ta 

lulluɓe tana rawar ɗari. 

      Cikin barcin daya ɗan fara figarta little ya faɗo mata a jiki yana faɗin, “Aunty!” cike da farin cikin ganinta. Buɗe idanu tayi da ƙyar tana kallon 

ƙyaƙyƙyawar fuskar yaron mai tsananin kama da mahaifinsa. Ta ɗan lumshe ta buɗe da ciro hannunta a bargon da ƙyar ta shafa kansa. 

        “Kaga ka tadani daga ɗan barcin dana fara sweetheart, waye ya kawoka?”.

       “Abbana”. 

Ya bata amsa kansa tsaye yana ƙara daka tsalle akanta.

       “Wai ALLAH little karka ƙarasani dan ALLAH, ka tausaya mani”. Ta faɗa tana yunƙurin miƙewa zaune. Idontane suka sauka akan AK dake bakin ƙifa tsaye 

kawai yana binsu da kallo tamkar ya samu television.

      “Barka da dawowa” tai maganar da maida idonta ƙasa. Batare daya amsaba ya tako ciki sosai, a kusa da ita ya zauna da kamo little dake ɗane mata 

wuya………..✍

     

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button