HAUSA NOVELMATAN GIDA Complete Hausa Novel

MATAN GIDA Complete Hausa Novel

Saif kuwa nafitowa part din Suhaila yanufa yasami falon ba kowa yashiga dakin Suhaila saidai baisameta ananba yafito kaitsaye dakin Seedar yanufa yasameta zaune kankujera tanajiransa yakarasa wanka tafito dashi Saif yakalleta sannu da kokari yauwa sannu da shigowa yauwa yasami guri yazauna kusa da ita bayan Seedar yakama wanka tatafi tarikosa yafito tadauko masa kayan da zaisaka bayan yakarasa shirinsa tafiya tabashi guri Saif yakallesa Seedar sannu da kokari yauwa Dad shima yafita yabarshi yashirta sunfito sunsami Sahla zaune itama tagama nata shirin tagaisa da Saif bayan wani lokaci Sahla tatafi yafito da Seedar Dad kuma yafita zuwa office

To masu karatu zamu taya anan sai kuma gobe idan Allah yakaimu da fatan munsha ruwa lafiya

By. Fauziya Usman Kogo
[1/2, 19:51] Maman Adyan: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀
MATAN GIDA
????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

1⃣3⃣
Na

Fauziya Usman Kogo

Zaune take tayi zugum sai tinanin abinda tayiwa Salim take tabbas bata kyautaba domin matsayin Salim yafi da haka hakama yau da Ummi zataji abinda ta’aikatawa Salim to da bazata taba gafarta mataba domin abinda ta’aikata yana da matukar girman gaske itakanta tabajin tsanar kanta to ina kuma ga Salim shida ta’aikata mawa zuwa yanzu ko wane irin kallo Salim yake yimata domin tanaji aranta bazaitaba yarda da itaba har’abada tadora hannuwa aka tana maicewa nashiga uku nalalace ni Nafisa maiyasa aikatawa kaina wannan mummunar illar wadda balallai ta’iya gushewa ba tabbas niban kasance mace tagariba hakama bancan-canci yabo daga gurin ko wane irin namijiba kasan cewar halaiyata gaba daya banagari wallahi inatakaicin abinda na’aikatawa yaya Salim tasami kanta da fashewa da wani irin kuka duk abinda take akan ido Salim take yaki tausayinta yagama kamasa yatashi daga inda yake yatafi gurinta yazauna yakallera tare da kiran sunanta Nafisa tadago takallesa batare da tace dashi komaiba yayinda idanuwanta suke zubar da wasu irin zafafan hawaye yaja numfashi tare da girgiza mata kai a’a Nafisa nafada maki banasan kukan nan kidena amma sam kingagara denawa maiyasa zakarika damun kanki da irin jarabawar Allah yayi maki komaifa da kike gani yakan iyasauyawa hakama bawanda yake wucewa kaddararsa dan haka kidena azabtar da kanki tahanyar barin kanki acikin kunci da bacin rai saboda nikaima wallahi banasan ganinki acikin irin wannan yanayin domin kuwa ina bukatar ganin farin ciki atare dake Nafisa duk dan halak baya manta alkhairi Nafisa kinyimin alkhairai da dama arayuwata wadanda suke mantar dani illarki Nafisa karki manta bayan Abba da Ummi babu wani wanda yataimakeni aduniyarnan fiye dake wallahi ina alfaharin kasan cewar amatsayin matata uwar ‘ya’yana hakama ina kaunarki fiye da yanda nake sanki wallahi Nafisa harzuwa wannan lokacin soyayyarki bata fita azuciyata ba domin kuwa soyayyar gaskiya nake maki kinkuwasan soyayyar gaskiya bata rushewa kiyarda dani Nafisa wallahi iya gaskiyata nake fada maki ina sanki hakama ina neman alfarmar kimanta da abinda yawuce domin musamu murayu cikin farin ciki

Cikin kasa-kasa da murya irinta ladabi tace wallahi yaya Salim abinne da akwai damuwa idan natina sainaji duk natsani kaina hakama sam nagagara mantawa domin abin yazauna azuciyata matuka naji amma duk da haka kiyi kokarin denawa kinji badankeba a’a saidan samun farin cikina ok zanyi kokarin yinhakan yauwa Nafisa Allah yabaki iko Amin yarabbi toni bara natashi nadaukosu Farouq daga makaranta ok adawo lafiya Allah yasa Amin yatashi yatafi tabishi da kallo tana murmushi tare dajin mamakinsa tafada azuciyarsa tabbas nayi dace da miji naga ya Ubangijina ka’azirtani dayimasa biyayya kamar yanda yakamata ta’amasa sa Amin tare da mikewa tashiga daga ciki tafada bandaki tadauro alwala tafito tana idar da salla su Safna nashigowa takallesu to sannunku da zuwa yauwa Mama Nafisa takai kallonta ga Safna tare da kiran sunanta Safna na’am Mama kishiga dasu ciki kucire kayanku kudaura towul kafin nashigo nayimaku wanka ta’amsa da to Mama taja hannanyansu suntafi Salim yabisu da kallo bayan sunshige yakalli Nafisa tare da daga mata gira to yakikaga yaran tayi murmushi abin sha’awa shima murmushi yake Allah yaraya manasu Amin Abban Safna kuma yayan Safna yayi dariya nagode da wannan kirarin naki murmushi kawai tayi masa tare da mikewa tsaye to bara natafi nayi masu wanka nafito nashiga kicin ok afito lafiya tanufi dakinsu Safna tayiwa Farouq da Safwan wanka ita kuma Safna tayi da kanta tafito tashiryasu Safna ma tashirya sunfito Salim sai kallonsu yake yana murmurshi yace wow Safna kinyikyau sosai nagode Dady yakalli Farouq yace Abbana kaima kayikyau Safwan yakallesa Dady nifa kaima kayikyau sosai sunyi dariya dukansu Safna tace Dady kakaimu gidan Mummy yaushe yanzu to shikenan kutashi mutafi Nafisa takallesa yanzu dankawai Safna tace kutafi saikutafi to yazanyi sam banasan nabata ran ‘ya’yana inabukatar ganin farin ciki atare dasu wannan yasa nakeyin duk abinda sukeso barinma idan yayi dai-dai da ra’ayina dama Dady yayimin waya akan muhadu gida zuwa yamma to kinga idan natafi yanzu saimuyi komai mugama akan lokaci to shikenan Allah yakiyaye adawo lafiya Allah yayarda Amin ya Allah yadaukesu suntafi

Ita kuma tabisu da kallo tana dariya taja numfashi tare da suke ajiyar zuciya tafadi sunansa cikin wani irin yanayi yaya Salim wallahi ina kaunarka tatashi tashiga kicin domin gudanar da abincin buda baki tayi girkinta tsab tagama tagyara gidanta tare dayimasa tiraran wuta tako ina saikamshi ketashi tashiga wanka tafito tashirya cikin wani kyakkyawan material tayikyau sosai wanda ita kanta tasan tahadu bakarya fitowarta yayi dai-dai da shigowar Salim saidai shikadai yake tataresa damurmushi tare da yimasa sannu da zuwa ya’amsa tare da mayarmata da murmushi yace wow Nafisa kinganki kuwa wallahi kinyi masifarkyau kai masha Allah tayi dariya sosai magode yaya Salim am yanaganka kaidaya inasu Safwan suna gidan mummy nikuma daga gurin tsafsir nake Allah sarki to sannu da zuwa yauwa am nahadama ruwan wanka eh hadamin ok tajuya tanufi dakinsa tahadamasa ruwan tafito tasamesa yana kokarin cire kayansa tataimaka masa yacire Sannan yashiga wanka tadauko masa kayan dazaisa bayan yafito yashirya yasa kayansa irin nata shima material ne kalar blue takallesa kayikyau yayi murmushi nagode sunfito falo baifi muntuna ashirinba akakira salla suntashi sunnufi gurin cin abinci suna cikin buda baki yace Nafisa albishirinki goro fari kal kayanmu sunfito kuma har sunkawo hannu tace masha Allah Alhamdulillah ina tayaka murna Allah yatsare gaba Amin nagode tayi murmushi sosai bakomai sunci gaba da buda bakinsu bayan sunkarasa yatafi masallaci bayan yadawo yadauketa suntafi gidansu mummy sunyi masu barka da shan ruwa da zasu dawo suka dawo dasu Safna

Toh nasu karatu sai kuma gobe idan munsake haduwa daku dafatan munsha ruwa lafiya

By. Fauziya Usman Kogo
[1/2, 19:51] Maman Adyan: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀
MATAN GIDA
????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button