HAUSA NOVELMATAN GIDA Complete Hausa Novel

MATAN GIDA Complete Hausa Novel

1⃣4⃣
Na

Fauziya Usman Kogo

Nafisa na’am inasan idan munsha ruwa mutafi mukarasa siyayyarsu Safwan domin gobe insha Allah zankai Safna Kano gurin Ummi kinga kema saikiyi taki soyayyar garlokaci yashige tayi murmushi to Allah yakaimu anjimar lafiya ya’amsa da Amin Farouq yace Dady nima zantafi Salim yayi murmushi to shikenan zantafi dakai saika rakani yace Dady nima zankwana agurin Ummi tare da Aunty Safna Salim yace a’a Abbana garmuyi haka dakai kayi hakuri muntafi tare mudawo tare basai kakwana ba yaturo baki yana fishi Dady ni acan nakesan nakwana Salim yaja numfashi kaga Farouq saidaifa kahakura amma bazaka kwana acanba tare zani dawo dakai aikuwa sai fishinsa yakaru Nafisa takallesa tace Safwan kuji bakinsa su Safna sai dariyarsa suke abin yabata ransa yasaki kuka Salim yace haba Nafisa Abban nawa kuke tsokana to bazandaukaba wannan aini kukeyiwa bashiba kudena banaso yajanyo hannunsa yadorasa akan cinyarsa yana rarrashinsa cikin muryar kuka yace Dady Kaga sunayimin dariya rabu dasu duk nabata dasu yayi dariya yauwa Dadyna haka sukaci gaba da firarsu harzuwa wani lokaci Salim yafita Nafisa kuma tashiga kicin domin gudanar da abincin buda baki tayi girkinta takarasa akan lokaci tagyata gidanta sannan tashiga wanka tafito tashirya tsab takuma shirya yaranta bayan wani lokaci Salim yadawo yasamesu sunata fira cikin raha wasa da dariya su Safna da gudu suka nufi inda yake sunayimasa oyoyo bayan yazauna Nafisa tayi masa sannu da zuwa ya’amsa yana maiyin murmushi sannu da kokari yauwa tamika tsaye to mutafi kayi wanka lokaci yakaraso ok yatashi sunshiga ciki tahada masa ruwa yatafi yayi wanka yafito yashirya tsab sunfito bajimawa akakira salla suntashi sunnufi gurincin abinci dominyin buda baki bayan sunkarasa Salim yafita zuwa masallaci yatafi tare da Safwan da Farouq Nafisa da Safna kuma sukayi tasu sallar agida bayan sundawo daga masallaci Salim yace to idan kinshirya saimutafi ko ok to mutafi suntashi sunfita gaba dayansu

Suntafi sunyi siyayya maiyawan gaske bayan sunkatasa sunnufi gidan Safwan saidai basu samesu agidanba Salim yakira layin Safwan yatambayesa suna ina sunzo gidansu basanan yace aiya muna gidan Zainab munzo duba Ahmad ok nima dama inatinanin zuwa gidan ok to saina shigo ok ashigo lafiya sunjiya sunnufi gidan Zainab sun’isa sunshiga Zainab tashiga yimasu sannu da zuwa sunzauna singaisa gaba daya suyiwa Ahmad yajiki yasami sauki to Allah yakara afuwa Amin Safna tamikawa Ahmad ledar dake hannunta tace Ahmad gawannan inji Dadyna Aimana kema ganaki mungode Aunty Safna Hafiz yace uncle zakuyiwa godiya ba Safna ba uncle mungode bakomai Allah yaimaku albarka Amin Zainab da Hafiz sunyi masa godiya yayi murmushi bakomai bayan wani lokaci sukayi masu sallama tare suka fito dasu Safwan ganin dare yayi yasa yabasu Salma siyayyarsu batare dasunkoma gidansuba su Safna sunyi masa godiya sosai yakuma fada masu cewar gobe Safna zata tafi Kano gurin Ummi acan zatayi sallah Allah sarki to Allah yakiyaye Salma tace uncle nima xanbi Aunty ina zuwa gurin Ummi to shikenan kishirya gobe saimitafi kiraka Safna idan zandawo saimudawo tare a’a Dady ni acan zankwana zanzauna tare da Aunty, Salma Safwan yace a’a Salim kabarta mana sutafi to shikenan Allah yakaimu goben lafiya sun’amsa da Amin Safna taji dadi sosai jintare da Salma zata sunyi wa juna sallama suntafi

Washe gari Nafisa takarasawa Safna shirinta tatafi tashirya Salim ma yagama shirinsa yafito sunfito sunyafi Safwan kawai suka bari shima harda kukansa saiyabisu sunnufi gidan Safwan domin daukar Salma sunsameta takarasa shirinsa tayi sallama da Safina da Salman suntafi Safina harda kuka domin tasaba da Salma sosai kasancewar sunkasance tamkar tagwaye kasancewar bawata tserewa atsakaninsu Safna ce rarrashinta tare da bata hakuri garki damu yayarki zata dawo badaiimawa ba kinji tadaga mata kai alamar eh

Sun’isa garin Kano cikin koshin lafiya sunshigo ciki Ummi tashiga yimasu sannu da zuwa ganin sunjima kuma basuga Abba ba yasa Salim yace Ummi ina Abbana kafin tace wani abu Farouq yace Dady gani anan sunyi dariya dukansu Safna tace dan Allah dubeshi waishine Abban Dady to jabakinka kayi shiru domin nakai akenufiba Dady wai kaji abinda Aunty take fada eh rabuda ita Salim yakalleta yace Safna kinfa rainamin Abbana to bazandauka ba Ummi tace Abbanka yanzunnan zaidawo insha Allah aidan baisan da zuwanku bane shiyasa yafita bajimawa kuwa saigashi yanashigowa su Safna sunyi gurinsa da gudu tare da rike kafafunsa Abba sannu da zuwa yauwa sannunku da zuwa bayan yazauna singaisa da Salim Ummi tace lallaima yarannan yanzu agabana kuke kokawar rkemin miji to bazanyarda da wannanba sunyi dariya dukansu Salim yajima anan daga bsani yayasu sallama yace Farouq mutafi yace Dady ni bazaniba bazakaba eh a’a Farouq garmuyi haka dakai yayi iyayinsa amma yace sam bazashiba saida yayi masa takarfi da kukansa sannan suka dawo da yamma sosai ya iso gida yanashigowa ana kiran magariba toilet kawai yashiga yayi alwala yafito suka nifi gurin buda baki Nafisa tace Farouq fishinme kake waibazai dawoba saina harda anan kinsan nikuma bazan’iya barinsa acanba shine abinda yakeyiwa kuka bayan sunkarasa buda baki Salim yanufi masallaci bayan yadawo yadan huta gajiya sannan yatashi yashiga ciki Nafisa tahada masa ruwa yayi wanka yafito yashirya yakwanta Nafisa tashiga yimasa tausa domin tafahimci yana tare da gajiya yakalleta yana murmushi nagode sosai bakomai mijina yace kinsan wani abu kuwa saika fada yace dubacan kiga yakai kallonta ga inda yayimata nuni dashi bata’ankaraba saiji tayi yarungumota takwanta jkinsa yana wasa da lips dinsa itakuwa saimurmushi kawai take yasunbaceta abaki daga bisani kuma suka kashe fitilar dakin sai komai yacigaba da wakana

To masu karatu sai kuma gobe idan Allah yasake hadani daku da wannan nakecewa musha ruwa lafiya

By. Fauziya Usman Kogo
[1/2, 19:51] Maman Adyan: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀
MATAN GIDA
????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

 

1⃣5⃣
Na

Fauziya Usman Kogo

Toh hauwasa dai nacewa maihali baya basa halinsa sai kuwa idan na’arone hakama sunce matar bari intashi bata kosar da mijinta kwance take sai faman malalowa take duk da cewa yau ba’aiki amma wannan sam baisatajin kuzari ajikiba takai kallonta ga agogon dake manne jikin bango taga karfe 03:30pm gata ba’abinda ta’aikatawa kanta taimakonta daya tagyara gidanta taja numfashi tare da tashi zaune tana maicewa Allah yanunaman wucewar azumin nan lafiya domin wannan mutuwar jiki tayimin yawa sai naji sam banasan aikawa kaina komai da zarar nafarajin yunwa to shikenan komai nasa yatsaya hakadai tatashi tashiga kicin domin tasamu abinda zata sarrafa masu susami abin buda baki arzikinta daya da su Intisar suke gidan Mama da saitanema masu abincin rana kafin dora na buda baki hakadai cikin mutuwar jiki da kasala tayi aikinta harta karasa dakyar ta’iya gyara kicin din tadawo falo tayi kwance kan kujera baifi da mintuna ashirinba saiga Pikram yadawo yashigo yasameta akwance tamkar wata marar lafiya cikin wata irin murya take yimasa sannu da zuwa yakalleta yana murmushi Ikram lafiya kuwa hum taja numfashi to da sauki yanzu nafito kicin ko wanka nagagara tashi nayi jikina duk amace yake yunwa duk tazagaye ko wanne lungu da tsako na jikina abin ba’acewa komai yayi dariya gaskiya Ikram kinfiye rali da yawa takallesa tare da dan harararsa aidole zaka fadi haka tinda bakasan yanda nakejiba to Allah yabaki hakuri am kinsan wani abu kuwa saikafada yau su Ihsan zasu dawo tana kwance tayi saurin tashi maikafada su Elham zasu dawo to maiyasa zasu dawo saboda suna bukatar haka nikuma inasan abinda sukeso hakane yaya Pikram nikaina inasan abinda sukeso wallahi bayan kai bantabasan wani abuba acikin duniyarnan fiye dasu Entisar ba ina kaunarsu inasan farin cikinsu fiye danawa farin cikin hakama inasan kasan cewa atare dasu wallahi yaya Pikram bantaba tinanin zan’iya hakurin rashinsu Ehsan ba koda kuwa na wuni dayane kaima shaidane akan haka ko yanzunma nabarsune kawai saboda ina da tabbacin zasu sami kuwa agurin Mama fiye dani saboda ni idan har watan Ramadan yatsaya to banida wani sauran kugari ni kuma bazan’iya hakurin ganin yarana acikin yanayin matsatsiba wannan yasa duk azumi nake kaisu agidan Mama da wannan nake naiman alfarmar kabarsu acan harzuwa ranar salla sai sudawo Pikram sai faman kallonta yake yayi murmushi sosai tare da fadar sunanta Zara kenan to Allah yakaimu sallar lafiya Amin yarabbi tafada tana murmushi yauwa maigidana godiya nake murmushi kawai yamata batare da yace da ita komaiba suna haka sukaji kiran sallah suntashi sunnufi gurin rebur domin gudanar da buda baki sun’isa gurin taja masa kujera ya zauna itama tazauna bayan da tazuba masu abinci bayan sunkarasa Pikram yanufi masallaci ita kuma tanufi bandaki tayi wanka tare da yowar alwala tafito tafarayin salla sannan tayi shirinta tana karasawa ana kiran esha tatashi tayi sallar tare da azkar bayan takarasa tamika domin fita tana kokarin fita Pikram nashigowa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button