MATAN GIDA Complete Hausa Novel

Su Farouq sun’iso gida yakasa zaune yakasa tsaye saikaiwa da komowa yake yayinda ransa yayi baki kirin hakama saijin zuciyarsa yake tamkar wuta saboda zafi Fatima tace Farouq waimaiyake faruwane maiyasa kayiwa Rumaisa haka yakamata karika tinawa Rumaisafa amanace agurinka kula da lafiyarta yana akarkashin kulawarka yakamata karka tinawa da wannan yasauke ajiyar zuciya hakane Fatima abinda kika fada to amma Fatima ina mamakin yana Rumaisa sam batajin tsorona ko shakkata maiyasa idan nabata umurni sam batasan tayi anfani da umurni na mainaragi Rumaisa dashi wanda ita sam bata bukatar abinda nakeso mainaiwa Rumaisa da zata zubarmin da ciki mainai mata gaskiya Rumaisa ta’aikatamin laifi maigirman gaske kuma yakamata nahukuntata abisa zunubinta tabbas sainasata taraina kanta agidannan a’a Farouq garkayi saurin yanke hukunci da sauri haka dominvni bana tinanin Rumaisa zata iya aikatama haka bazatayiba amma Fatima kinsan cewa Rumaisa sam bata farin ciki da juna biyun da yake atare da ita nasani yauwa to kinsan tana da kwadayi akan azubar mata da ciki eh nasani amma wannan bayanufin Rumaisa zatayima haka yakamata kayimata uzuri har zuwa lokacin da zatasami lafiya sai kaji komai daga gareta Fatima kenan bazaki ganeba wallahi Rumaisa zata’iyayin komai domin ganin tazubar da cikinta saboda sam bata bukatar haihuwa ayanzu Farouq naji amma dan Allah kayi hakuri nasancewa dole nakai zafi kuma bazaka jidadiba amma duk da haka ina maibaka hakuri daka tafi Kaga halinda Rumaisa take ciki zuwa yanzu bazaniba Farouq nafadamaki bazaniba amma Farouq yadakatar da ita tahanyar daga mata hannu yatashi yanufi dakinsa tabishi da kallo
Toh masu karatu sai kuma gobe idan Allah yakaddaremu da kaiwa da wannan nake cewa barkanmu dashan ruwa
By. Fauziya Usman Kogo
[1/2, 19:51] Maman Adyan: ????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
MATAN GIDA
????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
1⃣7⃣
Na
Fauziya Usman Kogo
Fatima tabishi da kallo tare dajin mamakinsa ganin lokaci yana shigewa yasa tatashi tanufi kicin domin dora girki tana cikin aikinta saiga Fara dauke take da Amrat yayindasu Adeel suke biye da ita Amrat kuwa sai kuka take Fara tace Mamie ina kuka shiga sai naimanku muke dazu nazo bakyanan muntafi part din Ammie itama batanan haka Hajiya mukawaine agidan ga Amrat sai kuka take tana naiman Ammie Fatima takarbeta tana rarrashinta yakalli Fara tace da ita Fara Ammie bayada lafiya yana asibiti Hajiya tana gutinta nima abinci nadawo na girka tace aiya Mamie maiyasami Ammie Fara badole sai kinsan abinda yake damuntaba kawai kiyimata addu’a kinji to Mamie Allah yabata lafiya Amin to kufita kuzauna afalo nima yanzu zanfito nakusa karasawa ok Fara tajasu sundawo falo bayan wani lokaci takarasa tafito tanufi dakin Farouq tasamesa akwance saidai ba barci yakeba ta’isa inda yake tazauna tare da kallonsa Farouq kallonta kawai yayi batare daya amsaba taci gaba da cewa ga abincincan na kammala saikatashi katafi gar lokaci yashige kaga kadan yarage asha ruwa yayi shiru baice da ita komaiba ganin baice da ita komaiba yasa takara mai-maita abinda tafada yace Fatima nafaji basaikinka mai-maitawa ba to amma Farouq yace kai subhanalillah nafada maki naji yakikesan nayine dan Allah kibarni nahuwa mts yaja tsaki tatashi zata fita yakirata Fatima tajuyo tare da amsawa na’am kibawa Fara da Farhan abincin subawa Iro yakaimasu cike da mamaki tace Iro eh amma Farouq maiyasa bazaka kaimasu da kankaba saboda bazan’iyaba Farouq dan Allah garkayi haka aikoba komai kakoma domin duba jikin Rumaisa aikuma saikiyi idan kingaji kyabari yajuya mata baya tare dajan tsaki tajuya tafita tayi komai kamar yanda yafada mata
Zaune suke sunsakata agaba suna kallo yayinda taketa sharar barci Hajiya takai jallonta ga Amir wadda gaba daya yasusuce da ganin irin halinda Rumaisa take ciki takirasa Amir ya’amsa asanyaye na’am Hajiya Amir yakamata katafi gida haka kaga lokaci yatafi da yawa kadan yarage asha ruwa baiso tafiyaba saidai kuma bazai’iyayiwa Hajiya musuba wannan yasa ya’amsa da to tare da mikewa tsaye to Hajiya natafi sainadawo to adawo lafiya kagaidasu Rukaiya zasuji yajuya yafita ya’isa gida jiki asanyaye Rumaisa tazo da gudunta tanayimasa oyoyo yariko hannunta batare da yace da ita komaiba yasami guri yazauna Rukaiya tashiga tambayarsa yaya Amir lafiya maiyake faruwa dan Allah kafadamin cikin kasa-kasa da murya yake fadamata Rumaisa na asibita bata da lafiya tace subhanalillah maiyake damunta tayi barine da sauri tace bari yadaga mata kai alamar eh tace innalillahi wa’inna’ilaihiraji’un kinga kishirya idan munsha ruwa mutafi kidubata ok yaya Amir mutafi nahadama ruwa kayi wanka ok yatashi sunshiga daga ciki tashiga bandaki tahada masa ruwa tafito yashiga tabishi da kallo tafahimci yana tare da damuwa sosai game da ciwon Aunty Rumaisa yafito yana cikin shirinsa akakira salla bayan yakarasa yafito yasamu Rukaiya hartazuba masa abinci yace Rukaiya banajin zan’iyacin abinci tsiyayomin juice kawai nasha bagardama tatsiyaya masa yasha yatashi yanufi masallaci tabishi da kallo yayinda take magana azuciyarta tabbas duk abinda kafara so ba’abinda zairabaka dashi tabbas har kullum har koyaushe zuciyar yaya Amir tana tare da soyayyar Aunty Rumaisa ina da tabbacin da soyayyar Aunty Rumaisa zaikwanta damarsa tatashi tatafi tayi salla ta’idar tana cikin azkar Amir yadawo yakalleta idan kinkarasa saimutafi ta’amsa da to tatashi suntafi
Iro ya’iso asibiti yashiga dakin da Rumaisa take yagaisa da Hajiya tare da tambayarta yamaijiki maijiki Alhamdulillah to Allah yakara lafiya Amin yarabbi yatashi Hajiya nizantafi to Iro asauka lafiya yafita abinsa bajimawa akakira salla Hajiya tatashi tashiga bandaki tadoro alwala tafito tafara gabatar da buda baki sannan tayi salla tana cikin azkar dinta Abba yaturo kofa yashigo bayan sungaisa yashiga tambayarta yajikin Rumaisa jiki Alhamdulillah to Allah yakara afuwa Amin ya Allah suna haka su Rukaiya suka turo kofa suka shigo sungaisa dasu Abba Hajiya tace Amir kadawo eh Hajiya haryanzu bata tashiba eh amma tasha barci aikara tayi barci kuma hakane Allah yayaye mata yabata lafiya Amin Rukaiya tace Hajiya ashe Aunty Rumaisa bata da lafiya ni wallahi bansaniba saiyanzu da yaya Amir yakoma gida yake fadamin wai Aunty Rumaisa tana asibiti batada lafiya tayi bari wallahi kuwa subhanalillah to Allah yabata lafiya yatsare gaba Amin suna haka bayan wani lokaci Rumaisa tafarka ahankali take bude idanta har suka bude su Hajiya sunshiga yimata yajiki ta’amsa da Alhamdulillah to Allah yabaki lafiya Amin su Amir sunjima anan sai dare sosai suka tafi haka Abba yarage daga ita sai Hajiya abinda yafi bata mamaki shine rashin ganin Fatima da Farouq zata’iyawa Fatima uzuri saboda yara tomai zaihana yaya Farouq zuwa gurinta ko dasu bata gansaba maihakan yake nufi tashiga tinanin tafada azuciyarta nashiga uku ni Rumaisa kardai yaya Farouq yazaci ninazubar da cikin nan tahanyar anfani da wani abu ko kuma shan wani abu tabbas hasashena zaizama gaskiya wannan dalilinne yasa yaya Farouq baizo gurinaba innalillahi wa’inna’ilaihiraji’un nashiga uku tabbas ina cikin tsaka maiwuya domin kuwa bansan tayanda zanfahimtar da yaya Farouq ba duk abinda zanfada bazaitaba yarda daniba tabbas ina cikin matsala maigirman gaske innalillah wa’inna’ilaihiraji’un subhanallahi yau bakina yacini yahaifarmin da matsala maigirman gaske mezanyi domin goge laifina awannan daran bata’iya barciba sai tinani take iri daban-daban tare da neman mafita