HAUSA NOVELMATAN GIDA Complete Hausa Novel

MATAN GIDA Complete Hausa Novel

Kwance yake tazo kusa dashi tazauna sai kallonsa take tare dajin mamakinsa takira sunansa Farouq gaskiya abinda kake bakakyautawa duk irin laifin da Rumaisa yayima baikamata kahukuntata da rashinkaba domin wannan sam ba adalci bane kuma kasan tana bukatar adalcinka hakama tana da haki da kai baikamata kayimata hakaba kaibakaje kadubataba kaibaka kirata awayaba duk da cewa batada waya hannunta amma aizaka iya iiran layin Hajiya domin kaji yajikinta Farouq karfa kamanta Rumaisa fa Amanace ce agurinka karkayi kokarin illatar da ita tahanyar haddasa mata da damuwa tare da bacin rai Farouq kaikanka shaidane akan Rumaisa yarinyar kirkice batada wata matsala ko damuwa hakama ni wallahi sam bana tinanin Rumaisa zata’iya zubarma da ciki saidai kawai idan hawu ce tahauwa tare da tsautsayi jintasakasa agaba sai duba takeyimasa tamkar ankunna fanfo yasashi dakatar da ita Fatima dan Allah ya’isa haka bana bukatar jinkomai gurinki hakama bakida abinda zaki nawa Rumaisa kariya domin ko itakanta bazata iyabawa kanta kariya ba domin tasan abinda ta’aikatamin a’a Farouq yace ya’isa Fatima ya’isa haka yafada cikin tsawa tare da daga murya yaja taki dan Allah fita kibarmin dakina Farouq nikake kora dakinka eh fita ok zanfita tatashi tafita abinta

Toh masu karatu sai kuma gobe idan Allah yakaimu taku har kullum har koyaushe Fauziya Usman Kogo

By. Fauziya Usman Kogo
[1/2, 19:52] Maman Adyan: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀
MATAN GIDA
????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

1⃣8⃣
Na

Fauziya Usman Kogo

Washe gari bayan tagyara gidanta tashirya yara tashiga kicin tahadama Rumaisa abincin break fast bayan takarasa tatafi tashirya tsab ganin lokaci yatafi yasata shiga dakin Farouq tasamesa gincire jikin gado yana chart ko shiryawa baiyiba ta’isa inda yake yazauna tare da kallonsa taja numfashi tare da kiransa Farouq yace ya’akaine tasauke ajiyar zuciya tana maicewa Farouq yanaga baka shiryaba harwannan lokacin Fatima kenan to dokane saina shirya awannan lokacin zanshirya aduk lokacin danaga dama badole sai yanzuba Farouq yau bazaka tafi office bane eh bazakiba maiyasa badole saikin saniba Farouq amma aizamu tafi muduba jikin Rumaisa ko kaga idan batafi sai Hajiya tafawo gida tasamu tahuta gajiya nadan wani lokaci ko dan Allah katashi kashirya domin kainake jira akaimata abin break fast yayi shiru kamar baijitaba sai aikin dannar waya kawai yake tace Farouq kanafa jini kinga Fatima dan Allah garki bataminrai dasanyin safiya kitashi kitafi kabawasu Farhan suba Iro yakaimata amma Farouq maiyasa kai bazaka kaimataba yayi shiru Farouq idan Kai bazakaba toni dan Allah kabarni natafi tare dasu Fara kaga Amrat dasu Adyan ko yaushe cikin kuka suke suna kiran sunan Ammie Fatima nafada maki gaskiya eh to wallahi bazaki ba Farouq bazaniba sai kuma kiyi kanki akeji takaicinsa yamata yawa tatashi tafita ranta bace taba Fara abincin tace takaiwa Iro yakaiwa Rumaisa takarba takaimasa yatafi

Zaune suke saidai ba mai magana acikinsu suna haka Amir yaturo kofa yashigo tare da sallama yasami guri yazauna tare da gaisawa da Hajiya bayan sungaisa yatashi yatafi inda Rumaisa yazauna agefenta yakai kallonsa gareta tare da kiran sunanta Rumaisa ta’amsa tare da kallonsa yajikinki jiki yayi sauki Alhamdulillah to madallah Allah yakara lafiya Amin Rukaiya nagaisheki da takwararki ina amsawa Hajiya tace Amir zaka jima anan eh to bara nakira Ahmed yakaini gida nasamu nadan watsa ruwa saina dawo to Hajiya am kiramin Ahmad to yatashi yafita yanufi office din Ahmed yasamesa acan yafada masa Hajiya tana naimansa ya’amsa da to sunfito tare sunnufi dakin da Rumaisa take Ahmad yace Hajiya gani am Ahmad gida nakeso kasaukeni to Hajiya Rumaisa yajikin yayi sauki to Allah yakara afuwa Amin Hajiya takalleta Rumaisa bara natafi nadawo ko to Hajiya adawo lafiya sunfita suntafi bayan fitarsu Amir yadauko kayan abincin da yazo dashi yace to bismillah kici abinci nagoshi kingoshi eh maikikaci tayi shiru kinga Rumaisa dan Allah garkimin haka kici abincinnan kisha magani kinji dan Allah yashiga rarrashinta tare da yimata magida dole tayarda yazuba mata yace aiya Rukaiya bata sako cokali ba kuma hannunki nadama da kalula gashi kuma nazuba abincin zakiyarda nabaki da hannuna takallesa tare da girgiza masa kai yace maiyasa kinga Rumaisa dan Allah kiyi hakuri kibari nabaki kici kisha magani yasa hannu ya’iba yana kokarin sakamata abaki takauda kanta yace Rumaisa waimiye haka dan Allah karbi kici wallahi idan bakiciba to bazankara zuwa dubakiba karbi kici cimana bazakiciba ok to bara natashi natafi yatashi kamar zaitafi har yakai kofa zaifita tayo kuransa Amir zomana zanzo amma da sharadin idan nabaki abinci zakici nayarda yauwa Rumaisa yafada yana murmushi yadawo yafara bata abinci tadanci kadan tace takoshi yashiga toilet yawanke hannunsa yafito yazauna takallesa tare da kiran sunansa Amir ya’amsa na’am am dan Allah idan da hali zanso katafi kadauki Rukaiya kutafi gida tadaukomin kayan da zansa inasan nayi wanka ko zanji dadin jikina gaskiya bazantafi nabarki kedaya ba saidai nayiwa direban su Umma waya yatafi yadauketa yakaita ok ba matsala haka kuwa akai yakira direbansu Umma yafada masa yatafi yadauki Rukaiya yakuma kira Rukaiya yafada mata sakon Rumaisa ya’amsa da to

Bayan mintuna biyu saiga Iro yashigo yakawo abincin da Fatima ta’aikosa yagaishesu tare da yiwa Rumaisa yajiki ta’amsa da Alhamdulillah to Allah yabida lafiya Amin yamike tonizantafi nagode Iro yafi yayi tafiyarsa bayan wani lokaci saiga Rukaiya tashigo rai bace kamar zatayi kuka sai huci take Amir sai kallonta yake Rumaisa tace Rukaiya lafiya hum taja numfashi tare da jan tsaki cikin bacin rai tace Aunty Rumaisa waimai kikaiwa yaya Farouq ne tace maiyafaru ne natafi gida domin dauko maki kaya kamar yanda kika bukata shine yarufemin kofa yace bazandaukar maki komaiba kuma yahanani zuwa da Amrat gata nasameta sai kuka take tana kiran Ammie amma dan rashin tausayi yace bazanzo da itaba saidai nakoma gida nadauko maki nawa kayan Rumaisa tayi shiru sai wani bacin rai takeji lokaci daya tafara zubar da kwalla tace garki damu da wannan Rukaiya nima bansan mainaiwa yaya Farouq ba tinda nazo asibitin nan yaya Farouq baizo yadubaniba kuma baibar Aunty Fatima tazo tadubaniba bansan mainai masaba him taja numfashi tare da mikewa tsaye tanufi toilet sunbita da kallo yayinda tausayinta yayi yawa atare dasu tana shiga Amir yatashi yafita bayan tafito tashirya Rukaiya takalleta amma Aunty Rumaisa su Abba sinsanda haka kuwa Rukaiya kenan to kosunsani yazasu dashi taja numfashi Allah dai yakyauta Amin

Amir yana fita yanufi gidansu Hajiya yana isa kaitsare part din Fatima yanufa yasami su Fara afalo bayan singaishesa yadauki Amrat yace zaki tafi gurin Ammie tadaga masa kai alamar eh da sauri su Adeel sukace uncle nima zani to kutashi mutafi yadauki Amrat yarika hannunsu Adyan sunfito basukai ga fitaba Farouq yafito yakallesa cike da mamaki yace Amir inazaka dasu haka gurin Rumaisa zankaisu da sauri yace meye kaga Amir inaganin mutuncinka ajemin yara tinkafin raina yabaci yajuyo sunfuskanci juna yace haba yaya Farouq wannan wane irin finkarfine maiyasa kake kokarin cutar da Uwa da ‘ya’yanta wanne daliline da kai da zaka hanasu Amrat zuwa gurin Rumaisa kaibaka tafiba kumasu kahanasu yaya Farouq abinfa yana naima yazama zalunci yadakatar dashi cikin bacin rai yace ya’isa haka Amir ashe bakada kirki rashin kunga zakayimin maiyadameka da abinda yake tsakanina da iyalina inaruwanka ita Rumaisa ce taturoka domin kafadamin duk abinda yayima dadi komiye waima tukun maiyakaika gurin Rumaisa ne yar uwarkace tobari kaji wallahi karka yarda kakara tinanin komawa gurin Rumaisa domin bakada wani dalili wanda zaisaka zuwa inda take ka’ajiyemin yara katafi dama zantafi amma kasani duk wanda yazalunci wani to Allah ma bazaibarshiba ya’ajiye Amrat tare da Sakina hannunsu Adeel yajuya yatafi zuciyarsa kamar zata fashe dan zafi Farouq yaja tsaki aikin banza yaciro wayarsa yakira garin office dinsa yafada masa idan Amir tazo shiga inda Rumaisa yahanasa idan kuma yana ciki to yafito daahi saura kuma karkayi yanda nace kayi yanda Rumaisa take so da kuwa kahadu da fishina matuka batare dayaji abinda zaifadaba yakashe wayarsa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button