MATAN GIDA Complete Hausa Novel

Amir yadawo asibiti rai bace idanuwansa sunyi jajir kallo daya zakayimasa kafahimci yana cikin matukar damuwa maigirman gaske d lokaci daya suka shiga tambayarsa lafiya bai’iya magana ba saidai yagirgiza masu kai alamar bakomai suna haka saika yaron Farouq wanda kuma shiyake kula da dakin da Rumaisa take yashigo cikin asanyaye yacewa Amir yafito yanasan zaiyi magana dashi bagardama Amir yabiyosa sunfito nanyake fada masa yanda sukai da Farouq yakallesa tare da suke ajiyar zuciya yace ok bara nashiga nayi sallama da ita to yashigo yacewa Rukaiya idan kintashi zuwa gida saikiyimin waya yadawo da kallonsa ga Rumaisa yace Rumaisa nizantafi kuma balallai na’iya dawowaba saboda Farouq yace gar’abarni nakara zuwa dubaki shine salon da yaronsa yafadamin yanzu Rumaisa tace Amir kahadu da yaya Farouq ne eh nanyafada mata yana sukai dashi yajuya zaitafi tadakatar dashi tahanyar kiransa Amir ya’amsa tare da juyowa tamika tsaye jirani mutafi domin nima bazan iya cigaba da zama ananba Rukaiya hadamana kaya mutafi bagardama tahada kayan sunfito suntafi suna isowa kaitsaye part din Hajiya suka nufa
Sunsami Hajiya tana shirin tafiya asibiti tace tofa anyi sallama kenan a’a Hajiya kawaidai naji bazan’iya jure zama acanba shiyasa nadawo gida kuma naga nasamu lafiya amma Rumaisa aidakinyi hakuri komai aizuwa yake yawuce hakane Hajiya saidai wallahi sam banajin zan’iya kara hakurin kwana asibiti to Allah yabaki lafiya Amin tace Hajiya inasu Amrat Hajiya tayi murmushi to kice yaranki suka dawo dake yanzunnan Fara tadauketa suka tafi part din Fatima ta’isheni da da fitina takai kallonta ga Rukaiya tace Rikaiya dan Allah daukomin ita to tatashi tatafi bajimawa sundawo da ita har dasu Adyan suna ganinta sunzo da gudunsu sinfada jikinta Ammie sai wani murna suke lokaci daya taji wani farin ciki yana shigarta
Toh masu karatu zamu tsaya anan sai kuma gobe idan Allah yakaimu da wannan nake cewa musha ruwa lafiya
By. Fauziya Usman Kogo
[1/2, 19:52] Maman Adyan: ????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
MATAN GIDA
????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
1⃣9⃣
Na
Fauziya Usman Kogo
Bayan mintuna biyu saigasu Farhan sunshigo sungaisa da Rumaisa tare da yimata yajiki ta’amsa da Alhamdulillah to Allah yakara lafiya Amin Fara ina Aunty tana part dinta ok to idan kunkoma kufada mata ina gaisheta zanfada mata da yamma Amir yadauki Rukaiya suka tafi bayan tafiyarsu saigasu Ahmed tare yake da Anisa bayan sungaisa Ahmad yace Rumaisa yahaka koda natafi asibiti sai nasamu bakyanan tayi dan gajeran murmushi kayi hakuri yaya Ahmad wallahi nagaji da zama acanne shiyasa kawai nadawo gida kuma naga nasami sauki dama jini nake bukata kuma tinda akasamin jini sainaji nawarware shiyasa kawai nadawo gida to Allah yakara lafiya Amin Aunty Anisa ina Aimana tana gidan Hajiya inagaisheta zataji ganin yamma tayi sosai yasa sukayi masu sallama suka tafi su Fara sundawo part din Fatima sunfada mata cewa Rumaisa nagaisheta tayi shiru kadan sannan tasauke ajiyar zuciya tare da girgiza kai suna zaune suna buda baki tace Farouq Rumaisa fa tadawo amma har zuwa wannan lokaci bakatafi guntaba nikuma baka barni natafiba Farouq yakamata kabar komai yawuce sai azauna lafiya amma hakan da kake sam ba dai-dai bane Farouq kanafa jina kayimin shiru baice da ita komaiba saima tashi da yayi yatafiyarsa tabishi da kallo tafada azuciyarta kai zuciya irin ta Farouq Allah yakare mutun da ita tatashi yashiga daga ciki
Da dare suna zaune afalo sunafira yayinda Amrat tare zaune jikinta su Adyan kuma suna jikin Hajiya kasan cewar bata koma part din taba wayar Hajiya tadau ruri tadaga tare da sallama bayan sungaisa yamata barka dashan ruwa yafada Mata cewar bazai sami damar shigowaba saboda bayajin dadin jikinsa tace subhanalillah to Allah yakawo sauki Amin dan Allah inayiwa Abba barka dashan ruwa zaiji to nagode sunyi sallama tafadama Abba sakon Farouq yace to Allah yabashi lafiya sun’amsa da Amin Abba yace Rumaisa nikuwa inasan natambayeki wani abu to Abba nace waikuwa bawata matsala atsakaninki da Farouq domin acikin kwana biyunnan nafahimci kamar babu jituwa atsakaninku kwananki biyu asibiti amma bantaba zuwa nasamesa agurinkiba yau kindawo gida amma tinda kika dawo baishigo ba nayi tinanin sai dare zaishigo saikuma gashi yanzu yayiwa Hajiya waya yana fadamata cewar bazaisami damar shigowaba wai bayada lafiya wanda kuma wannan ba gaskiya bane yafadi hakanne sabida baya bukatar yashigo yayi tozali dake Rumaisa kifadamin gaskiyar abinda yake faruwa atsakaninki da Farouq tayi shiru tare da girgiza kai Abba nima bansan komaiba bansan abinda na’aikata masaba bakiymasa komaiba tadaga masa kai alamar eh yaja numfashi tare da sauke ajiyar zuciya yajinjina kai yana maicewa lallai Farouq baya da kirki amma zanhadu dashi domin bazandaukar masa cinmutuncinki ba balantana kuma yayi kokarin wulakantaki yazama dole nanuna masa kuskuransa domin yayi kokarin gyarawa tafirgiza kai tana maicewa a’a Abba kabarshi nizanyi iyakokarina dan ganin nagyara tsakanina dashi banasan kai ko Hajiya kuce zakushiga wannan zaisa yaga kunfifitani akansa wanda hakan zaisa yakarajin yatsanan ko wani abu nakamancin haka dan haka ina mainaiman alfarmar garkayi masa zancan komai akaina dan Allah Abba amma Rumaisa idan har nabar Farouq yace gaba da zaluntarki Allah bazaibarni ba domin zaitambayeni Amanarki da akabani garka ddamu Abba komai zauwuce insha Allah to Allah yakyaura Amin Abba bayan mintuna kadan tatashi tashiga daga ciki tashinfide yaranta sannan takwanta tare dajin mamakin Farouq tare da tinanin mafita taya zata fuskanci Farouq da wannan tinanin tayi barci
Washe gari da safe tatashi tatafi part dinta tagyarashi tsab takuma part dinta domin tafahimci adalilinta ne Farouq yasa baishiga part din Hajiya ba bayan fitar Farouq Fatima tatashi tanufi part din Hajiya gurin Rumaisa saidai bata sameta acanba Hajiya tafada mata cewar takoma part dinta tafito tanufi part din Rumaisa taturo kofa tashigo tasameta zaune tayi shiru tare da buga wani irin uban tagumi ga’alama tinani take ga kuma kwalla tanabin fuskarta take lokaci daya Fatima taji tausayinta yakamata ciki mutuwar jiki takaraso inda take tazauna cikin sanyin murya ta’anbaci sunanta Rumaisa saidai bata amsaba tafahimci tayi zurfi acikin tinaninta tadafata cikin kasa-kasa da murya takira sunanta Rumaisa tajuyo takalleta batare data amsaba Fatima taci gaba dacewa Rumaisa dan Allah kiyafeni kikuma gafarceni nasan cewa kina cike da mamakina akan rashin zuwa dubaki amma kisani wallahi ba laifina bane Farouq ne yahanani amma wallahi Allah shine shaidana dake nake kwana araina kuma dake nake tashi Rumaisa tagirgiza mata kai bakomai bakomai Aunty Fatima kuma wallahi bantaba ganin laifinkiba domin kasan bakida laifi dan haka kidena bani hakuri domin bakiyiMin komaiba
Fatima takalleta tare da cewa Rumaisa nikuwa inasan natambayeki wani abu inajinki Rumaisa maiyasa kika zubar da ciki tasauke ajiyar zuciya tare da jan numfashi tagirgiza kai wallahi Aunty Fatima bani nazubar da cikin nanba Allah shine shaidana domin shiyafi sanin komai akanmu wallahi hawuce tahauni tare da tsautsayi tabbas nayita kokarin ganin nazubar da cikinnan amma yaya Farouq baiyarda ba tabbas nahakura da zancan zubar da ciki daga bisani kuma Allah ya’aikomin da wannan al’amarin tahanyar ciwan mata wanda har yayi sanadin zubarmin da ciki amma wallahi banyi anfani da komaiba amma nasan yaya Farouq bazaitaba yarda daniba kasan cewar yasan yana natsani haihuwa ayanzu wannan dalilinne yasa haba daya yadena bani kulawa suna haka saiga Farhan yashigo yace Mamie waikizo inji Dady haryadawo eh tinda jimawa kace masa inazuwa ok yajuya yafita tadawo da kallonta ga Rumaisa tace Rumaisa zantafi saina kima dawowa to Aunty Fatima nagode tatashi Tafita