MATAN GIDA Complete Hausa Novel

Tana zuwa tasamesa saikai kawo yake yana ganinta yashiga dakinsa tasamesa acan yace daga ina kike part din Rumaisa wakika tambaya lokacin bakanan to zuwa gunta dolane maiyasa kike kokarin kaini bango haba Farouq gaskiya nibazan’iya wannan rayuwarba kuma bazan iyakyale Rumaisa ba domin batayimin komaiba komai yafaru atsakanin June dan haka nibaishafanba kaima dazaka iya dauka yakata da yafi haka kika fada eh amma idan abin dana fada yabata ranka to Allah yahuci zuciyarka tafita tanufi dakinta yasameta anan yashiga fada da ita ta’inda yake shiga batanan yake fitaba tayi shiru batace dashi komaiba bayan yakarasa yafita
Toh masu karatu zamutsaya anan sai kuma gobe idan Allah yakaimu dafatan munsha ruwa lafiya
By. Fauziya Usman Kogo
[1/2, 19:52] Maman Adyan: ????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
MATAN GIDA
????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
2⃣0⃣
Na
Fauziya Usman Kogo
Da dare tasamesa adakinsa zaune take sai faman dannar waya yake ta’isa inda yake taxaune kanta nasunkuye take masa magana cikin tausasa murya tace Farouq bazangajiya ba gurin fadama gaskiya ba domin ina bukatar alkhairi atare dakai Farouq garka manta yau girkin Rumaisa ne amma sam baga kana kokarin tashi domin zuwa part din taba wanda kuma hakan laifine maigirman gaske Farouq kayi hakuri dani da kuma halina domin nasan zuciyarka tana cike da ni akan yawan zancan Rumaisa danake yima Farouq dan Allah katashi katafi kasamu Rumaisa domin kufuskanci juna kai da ita domin tahakanne zaka sami jutuwa atsakaninku yaja numfashi Fatima tabbas abinda kika fada gaskiya ne saidai kumani kagagara manta abinda Rumaisa ta’aikatamin wannan yasa sam bana bukatar kasan cewa atare da ita a’a Farouq sam garka fadi haka kuma garka manta rayuwa maikyau ita take manta baya domin tagyara gaba badan komaiba saidan rayiwarmu tatsabtata Farouq katina daba’a yafiya ko ba’amanta baya da Rumaisa bazata taba kasan cewa akarkashin kulawarkaba da Rumaisa bata yarda tazamo matarkaba amma duk girman laifinda ka’aikawa Rumaisa tayarda tayafema kuma tadawo gareka Farouq Rumaisa tayima halaccin daba kowane mutun zai’iyamashiba kuma kaikanka kasan da haka da wannan nake naiman alfarmar kabar komai yawuce domin dukanmu murayu cikin farin ciki yasauke ajiyar zuciya yana maicewa gaskiya Fatima ke mutunniyar kirki ce hakama kina da halaiya nagari kowa ne namiji zaiso yasameki amatsayin mata wallahi ina alfahari da kasancewarki mata agareni Allah yabarni dake har mutuwa Amin mijina kaima mutunne nagari ina farin ciki da samunka amatsayin miji Allah yabani ikonyin biyaiya agareka Amin
Farouq yanzu abinda nakeso dakai shine katashi katafi gurin Rumaisa tinkafin barci yayi awan gaba da ita kaga dare yayi sosai karfe 11:30pm kuma dan Allah idan katafi karkayi abinda zaibata ranta kaji kallonta kawai yayi batare dayace da ita komaiba Farouq katashi mana yagirgiza kai yace Fatima kenan waike dan Allah kodan kishinnan bakyayi ni wallahi bansan wace irin mace baceke sam bakya kishina tayi murmushi sosai Farouq kenan kaima kasan inakishinka kawaidai Rumaisa sace bazan’iya kishi da ita ba domin sam banayimata kallon kishiya balantana na’iyayin kishi da ita har kullum har koyaushe kallon kanwa nakeyiwa Rumaisa domin tayimin halaccin da har yanzu banyimata Shiba Farouq wallahi kasani daba Rumaisa bace takasance amatsayin matarkaba da wallahi kasha mamakina da kuma kafahimci cewar ashe ina da kishi tasauke ajiyar zuciya tace kaga Farouq lokaci nakara tafiya karfe 12:00am ake magana katashi katafi to shikenan tinda kinyimin izini dana tafi zantafi yatashi sunyi sallama yatafi
Rumaisa kuwa ganin lokaci yatafi batayi tinanin zaishigoba amma wannan baisaya tarufe kofartaba tana kwance rungume da Amrat taji shigowarsa tashinfide Amrat tafito saidai batagansaba wannan yasa tanufi dakinsa saidai kuma tayi rashin sa’a domin yarufe dakinsa da sakata jinyarufe kofar yasa tajuya takoma dakinta batare data buga masa kofaba tayi zaune tare da buga wani uban tagumi abin duniya ya’isheta tarasa maiyake mata dadi wannan yasata fashewa da wani irin kuka maitsanani lokaci daya tausayin kanta yakamata takai kallonta ga photon iyayenta tatashi ta’isa gurin tayi tsaye tana maicewa Dady maiyasa kazabamin miji irin yaya Farouq dominshi yakasance mutunne maitsananin fishi da xuciya idan yayi fishi yanajimawa kafin yasauka sam bayajin tausayina arayu kona mutu duk dayane agurinsa Dady wallahi badan da kariga kabada Aurena ga yaya Farouq ba ba wallahi bazantaba kasan cewa matarsaba koda kuwa daga baya yabukaci hakan batayi barciba awannan daran da asuba tanajin lokacin dayafita zuwa masallaci bayan ta’dar da salla tadawo falo tanajiran dawowarsa saidai baidawoba part din Fatima yanufa yashiga dakinsa yakwanta ganin badawoba zaiyiba yasata tashi tanufi dakinta takwanta bayan wani lokaci barci yadauke kasancewar da dare batasamuyin barciba tana cikin barcinta su Adeel suka tasheta takallesu Adyan kuntashi to mutafi mashirya maku tadaukesu tashiga toilet dasu tayi masu wanka tafito tashiryasu itama tayi nata wanka tafito tashirya sunfito falo tahada masu shayi sunsha Adeel yace Ammie mutafi gurinsu yaya Farhan Ammie ina Dady yana part din Aunty Fatima ganin sunsakata agaba da zancan Dady dasu Farhan yasa tadauki Amrat tarika hannunsu Adyan suntafi part din Fatima sunshiga su Adeel kaitsaye dakinsu Farhan suka nufa Rumaisa kuma tayi zaune kankujera bayan wadansu mintuna saiga Fatima tafito tace tofa maraba da Rumaisa yaushe kika shigo banwani jima sosaiba ina kwana Aunty Fatima lafiya qlau yakarfin jini to Alhamdulillah to Allah yakara lafiya Amin suna cikin firarsu saiga Farouq yafito Fatima takallesa cike da mamaki tace Farouq yanaga kana fitowa daga dakina Rumaisa tare kukashigone kafin yace wani abu Farouq yace kinga Fatima banasan sa’ido da yawan binkice baruwanki dan haka kika bakinki kiyi shiru haba Farouq taya zanga kana fotowa daga dakina kuma kace nayi shiru to aisaikiyi tadawo da kallonta ga Rumaisa tace Rumaisa kifadamin gaskiya tare kika shigo dashi ko anan kikasamesa tayi dangajeran murmushi Aunty Fatima dai kawai kiyi yanda yace kabarzancan yawuce toshikenan tinda kingoyi bayansa yace tonizanfita to Allah yakiyaye adawo lafiya Allah yasa sun’amsa da Amin yafita abinsa
Rumaisa tabisa da kallo yayinda idanuwanta suka cicciko da hawaye tayi saurin kauda kanta saboda batasan Fatima tafahimci halinda take saidai abinda batasaniba shine duk yanayinda take ciki Fatima nakallace da ita tafahimci tana tare da damuwa matuka wannan yatabbatar mata da Farouq baihakuraba tagirgiza kai tare da kiran sunanta Rumaisa ta’amsa asanyaye kiyi hakuri da duk irin abinda Farouq zaiyimaki domin wallahi Farouq sam bayajin shawara kuma idan yayi niyar aikata wani abu to bawanda ya’isa yahanasa face ya’aikata hakama babuwani abu da yake tabbata acikin duniyarnan dan haka kikara hakuri da zarar yasauko shikenan zakiga komai yawuce bakomai Aunty Fatima
Da dare yadawo part din Rumaisa yasameta zaune afalo yayi kamar baigantaba yanufi dakinsa tabishi da kallo yakai kofar dakinsa saidai yasami kofar arufe bayan yashigo tamayar da kofar tarufe da mukulli yajuya zaifita nanma yasami kofar arufe yatafi inda take yace Rumaisa wannan wane irin wulakancine maizaisa kirufemin kofa kayi hakuri domin nasan idan har bahaka nayiba tobazaka taba sauraranaba shiyasa nama haka yaya Farouq inasan zaniyi magana dakai dan Allah kayi hakuri kasaurareni ganin saimagiya takemasa tare da hadashi da Allah yasa yazauna domin saurarar abinda zata fada masa cikin kasa-kasa da murya irin ta ladabi tace yaya Farouq nasancewa kana fishi dani fishi sosai domin zuciyarka tana zargina da abinda bani na’aikataba