MATAN GIDA Complete Hausa Novel

To masu karatu sai kuma gobe idan maikowa yakaimu taku har kullum maiyimaku fatan alkhairi take cewa musha ruwa lafiya
By. Fauziya Usman Kogo
[1/2, 19:49] Maman Adyan: ????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
MATAN GIDA
????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
0⃣7⃣
Na
Fauziya Usman Kogo
Safna nifa al-amuran Salim sunfara bani tsoro domin akullum zakiga Salim to yana tare da damuwa gayawan tinani idan natambayesa kuma sai yace dani bakomai narasa maiyake damunsa haka Nafisa itama sam bata fadar komai nikuma wallahi abin yana matukar damuna sosai hum taja numfashi hakane Dear nikaina da wannan damuwar atare dani haka Mum da Dad domin sukansu sungagara sanin damuwarsa balantana a’iyasama masa mafita subhanalillah to Allah yakawo mana sauki Amin toni zantafi gidan Umma yanzu zaki tafi gidan Zainab duba Ahmad a’a sai munsha ruwa tukunna ok to Allah yakaimu lokacin lafiya Amin yarabbi yamike tsaye domin fita tayi masa rakiya yatafi tadawo ciki tare da tinanin yayanta azuciyarta to taya zasusan damuwarsa domin su’iya taimaka masa tahanyar naima masa mafita takasance da wannan tinanin harnawani tsayin lokaci daga bisani tatashi tayi salla sannan tashiga kicin domin girki
Tsaye suke jikin mota bayan suntashi daga tafsir Kabir yace am Safwan dama ko inasan zaniyi wata magana dakai to bismillah inajinka Safwan nace wai kakosan yanayinda Salim yake aciki ko nace kasan halinda yake ciki da sauri Safwan yace kamaryafa banfahimceka ba maikake nufi Safwan ahalinda ake ciki ayanzu Salim yana cikin wata irin jarabawa tarashi wadda tasamesa tahanyar hada hannun jari Safwan ahalin yanzu abinci maidadi yana wahalarci agidan Salim rayuwa gaba daya tasauya masa ganin kayi ko oho ne yasa nace bara nama magana naji lokaci daya wani bacin rai da damuwa suka shiga Safwan cike da rudani yace Kabir wai wane Salim kake magana akansa Salim dai nawa ko kuwa wani Salim kake bani labari akansa domin kabarci acikin duhu inabukatar haske daga gareka Safwan kenan Salim dai naka nake magana akansa Salim yayan Safna dasauri Safwan yashiga fadin innalillahi wa’inna’ilaihiraji’un Kabir yaushe wannan musibar ta’afka akan Salim to gaskiya nima bansaniba wannan zancanma ba’abakinsa najiba dominshi sam bayasan kowa yasan halinda yake aciki subhanalillah nagode Kabir bara natafi ok sunyi sallama yatafi kaitsaye gurin siyayya yanufa yayi masu siyayya maiyawan gaske sannan yanufi gidansu ya’isa bayan angama shiga da kayan yashiga Nafisa nayimasa godiya yadakatar da ita tahanyar cewa a’a bana bukata ina Salim yana gidansu Mum ok yajuya yafita tabishi da kallo tafahimci cewar cikin bacin rai yake hakama akai damuwa atare dashi to maiyake damuwa da Safwan ne haka
Ya’isa gidansu Dad yashigo tare da sallama bayan sungaisa yakai kallonsa ga Salim tare da fadar sunansa Salim waikuwa da gaske ni dan Uwankane anya kanayin kallon kani kuwa shin kamanta girman zumuncin dayake atsakaninmu ne Salim koda bamukasance yan Uwan junaba kuma ban’Auri Safna ba garka manta nidakai abokan juna muke amma duk da girman zumuntarmu sai kayi kokarin nunamin matsayina tahanyar nunawa al-ummar gari cewa niba kowa bane agareka wallahi banji dadin hakanba kuma sam bakayimin adalciba amatsayina nakininka abokinka kuma mijin kanwarka Dad sai kallonsa suke Mum tace Safwan waimaiyake damuwane cikin kasa-kasa damurya yake fadamasu abinda Kabir yasanar dashi lokaci dayasu Dad suka saka salati tare da fadar innalillahi wa’inna’ilallahinraji’un Salim yaushe hakan tafaru dakai wata biyu kenan Dad haba Salim haba Salim tomiye nayin shiru kakifada kabar kanka da iyalinka acikin damuwa da bacin rai wannan sam ba dai-dai bane to miye anfanin dukiyata idan har yarona zairayu acikin kunci da rashi miye anfanin dukiyar Abbanka wanda nasan ashirye yake daya sadaukar da komaisa akanka domin. Nishaidane akan haka miye anfanin dukiyar Safwan idan har bazai’iya maimakama ba Salim maikake tinanin zaifaru dani idan har wani abu yasamesa adalilin haka dan Allah Salim garka kara aikatamin irin wannan zunubin kajiko kuma kayanku zasu fito dayardar Allah nanda kwana biyu komai zaidai-daita kaji yarona yayi murmushi tare da ansawa eh Dad sannan kuma yabasu hakuri dukansu bakomai Salim Allah yama albarka Amin Dad ayanar Dad yatura masa kudi maiyawan gaske acikin account dinsa yace yayi anfani dashi nakwana biyu yayi masa godiya sosai Safwan yafada masa karyasiyi kayan abinci domin yagama da wannan babin ya’amsa da to tare dayimasa godiya bakomai Salim ganin lokacin buda baki yakaraso yasa Salim da Safwan sukayiwasu Mum sallama kowannansu yanufi gidansa
Salim yasami gidanss tas sai kamshi ketashi abin mamaki Nafisa tataresa da murmushi tare da yimasa sannu da zuwa sai wani kallo yakeyimata maicike da mamaki tayi musmushi sosai yakake yimin irin wannan kallon Kaga nasan agajiye kake abinda za’ayi mutafi kawatsa ruwa kaga zuwan wannan lokacin yakarasa saimuyi buda baki ko shidai kallonta kawai yake hakama yagagara cewa da ita komai ganin bayada niyar tafiya yasata janyo hannunsa suka shiga ciki takaishi har toilet sannan tafito tare da dauko masa kayanda zaisa bajimawa yafita takallesa tana murmushi sannu da fitowa tatsane masa ruwan jikinsa tare da shafesa da mai tagyara masa gashin kansa harzuwa fuskarsa tashiryasa baga daya yayikyau yasa kayansa sunfito suna fitowa anakiran salla kaitsaye sunnufi teburin Cin’abinci taja masa kujera yazauna tazuba masu abinci sannan tazauna har zuwa wannan lokacin zuciyar Salim cike take da mamakin Nafisa takallesa lokaci daya sukayi ido biyu tayi masa yar dariya am zakaci da kankane kokana bukatar nabaka abaki shidai kallonta kawai yake jinyayi shiru baiyi maganaba yasa tafara bashi abaki yana ciki hakasukayi buda bakinsu harsuka gama yatashi yanufi masallaci bayan yadawo yasameta ta’idar da salla tana azkar yayi zaune sai kallonta kawai yake bayan ta’idar takallesa tafahimci har zuwa wannan lokacin coke yake da mamakinta cikin kasa-kasa da murya irinta ladabi take magana yaya Salim tabbas nayima laifi maigirman gaske hakama nisam bakasance mace tagariba nakumasan balallai ka’iya afeminba domin ayanzu bazaka kara yards daniba balantana kuma abinda zanfada domin kuwa zahirina yanunama komai a game dani yaya Salim wallahi idan nace bana sanka kona dena sanka to tabbas nayi Karya kuma wannan itace babbar karyar dazanyi acikin wannan duniyar tabbas ina kaunarka amma ayanzu balallai ka’iya yatda daniba amma duk da haka inamaineman afuwarka abisa zunubin dana aikatama magana take yayinda kwalla take fita daga fuskarta yayi shiru saikallonta yake tadago fuskarta wadda takasance asunkuye sunfuskanci juna tace yaya Salim dan Allah kayimin magana ganin baixe da ita komaiba sai akn kallonta dayake yasata tashi tashiga ciki tafada kangado yayinda take wani irin kuka lokaci daya taji tatsani kanta maiyasa ta’aikatawa Salim haka tana haka taji yarikota tare da tada’ita zaune yakalleta tare da girgiza kai yana maishare mata kwalla a’a Nafisa kidena kuka banaso yaya Salim nasani zuwa yanzu kana fishi dani fishi sosai to taya bazanyi kukaba a’a Nafisa nisam bana fishi dake domin tinda jimawa nasan waceceke wannan yasa sam banajin kinyimin laifi dan haka kidena kuma dama damun kanki kinji bakomai kisa aranki ba’abinda yafaru kimanta da komai kinji nagode mijina Allah yabani Ikon yin biyayta agareka yanda yakamata ya’amsa da Amin yana maiyin murmushi