HAUSA NOVELMATAN GIDA Complete Hausa Novel

MATAN GIDA Complete Hausa Novel

Safwan yadawo gida Safna tataresa tare da yimasa sannu da zuwa yauwa barka da kokari yana kokarin zaunawa yaji Angara kiran salla kaitsaye sunnufi gurincin abinci sunacikin buda bakine Safwan yake fada mata abinda yafaru da Salim tace subhanalillah to Allah yatsare gaba Amin ya Allah bayan sunkarasa Safwan yanufi masallaci gurin salla Safna bayan ta’idar da salla are dayin azkar takira layin Salim ta jaje

Tomasu karatu sai kuma gobe idan Allah yakara hadani daku dominjin cigaban littafin da wannan nake cewa musha ruwa lafita

By. Fauziya Usman Kogo
[1/2, 19:50] Maman Adyan: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀
MATAN GIDA
????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

 

0⃣8⃣
Na

Fauziya Usman Kogo

Kwance take banda juyi ba’abinda take saboda batajin dadin jikinta kasan cewar juna biyune atare da ita tana haka taji anturo kofa anshigi tare da sallama ta’amsa batare da tatashi zauneba takaraso tare da zaunawa takalleta Aunty kwance kike kardai jikin hum taja numfashi wallahi Rumaisa jikin ne duk yamacemin sam banasan motsasa domin gaba daya jikin ciwo yake subhanalillah to Allah yakawo sauki Amin Aunty yau mai’za’adafa lokaci yatafi yamma tasomayi har yanzu bamu dora komaiba nikaina wallahi jikina duk amace yake barci kawai nake bukata shiyasama kikaga najima banfitoba Rumaisa kice tare zamu sauke kamarya zamu sauke banfahimtaba Rumaisa kenan kemadai kinsan cewa akwai juna biyu atare dake da sauri tace juna biyu Aunty dan Allah rufamin asiri Rumaisa Allah da gaske nake da akwai juna biyu atare dake kinaso kifadamin cewar bakisan dashiba shiwa cikin dayake jikinki dan Allah Aunty kidena fadamin haka idan baso kike kibata rainaba juna biyu yanzu anazaune qlau saikace nafi kowace mace haihuwa gaba daya shekarar Amrat nawa dahar zansake daukar wani cikin bayan nasan wahalar danasha yayin haihuwarta har saida akayimin c.s aiduk saurin haihuwata zanyihakurin Amrat tashekara biyar tukun Fatima sai kallonta take tace Allah sarki kinga Rumaisa ni kuma naso nakasance kamar ke saidai kowa da irin tsarin da Allah yamasa kinga ni bantaba planing ba amma duk yarana shekara shidane atsakaninsu am Aunty niduk bawannanba sunake kifadamin zancan gaskiya maikika fahimta game dani Rumaisa saidaifa kiyi hakuri kawai amma kisani akwai juna biyu atare dake innalillahi wa’inna’ilaihiraji”in tirkashi aikuwa zaisha kasa maikike nufi kardai zubardashi zakiyi sosaima kuwa domin shiyafi komai sauki agurina sabida ayanzu ba haihuwa atsarina amma Rumaisa kinsan hatsarin dayake cikin zubar da ciki kuwa Aunty aibasai natafi asibitiba domin inada tabbacin cikinnan bazaiwuce watanni biyu a domin suna dauka banyi alluraba kinga kuwa magani kawai idan nasha yawadatar to naji amma yazakiyi da Farouq idan haryasami labarin kinzubar masa da ciki aisai idan yaji sannan ransa zaibaci haryayi fadako to idan kuma baijiba fa kinga kenan ba’abinda zaifaru Fatima tayi murmushi Rumaisa kenan kinga dubacan kiga takai kallonta ga inda tayimata nuni dashi cike da mamaki takira sunansa yaya Farouq yaushe kashigo taya zakisan shigowarsa tinda hankalinki baya jikinki amma yajima anan kuma yaji komai

Farouq sai wani irin kallo yake yimata batare dayace da ita komaiba yace Rumaisa wallahi kisani ko tsautsayi kika bari yazubar da cikin da yake jikinki to tabbas zakisha mamakina idanke bakya bukatar abinda yake tare dake toni ina bukata dan haka saiki kiyaye idan kuma kinso kya’iyayin abinda kikaga dama yajuya zaitafi talirasa yaya Farouq yadakar da ita batare dayajuyoba tahanyar daga mata hannu yacigaba da tafiyarsa tasauke ajiyar zuciya tare da cewa nashiga uku ni Rumaisa Aunty kitaimakeni dan Allah garwani abu yafaru dani Aunty kinfasan yanda nawahala ga haihuwar Amrat hakama kina daga cikin wadanda suka karbi haihuwata yanda nawahala haihuwar Amrat ko haihuwarsu Adeel banwahala hakaba ke kanki kinfadamin cewar inabukar hutu kafin nakara daukar wani cikin kuma saikawai yanzu ace inada juna biyu ni wallahi inajin tsoron karwani abu yafaru dani a’a Rumaisa kidenajin tsoro insha Allah ba’abinda zaifaru dake Amrat fa shekararta uku harda wata biyar kinga kuwa bawani abinda zaifaru dake kisaka wannan aranki kinji bata’iyacewa da ita komaiba saidai ta’iya daga mata kai yayinda idanta suke zubar da kwalla haba Rumaisa miye haka kike dan Allah kidena kinji to yauwa kokefa haka suka tashi suka shiga kicin domin gabatar da abincin buda baki bayan sunkammala Rumaisa tanufi part dinta yayinda take mamakin kanta tayanda zatasami juna biyu batare da sanintaba to maihakan yake nufi yakai kallonta ga photon iyayenta tace Dad Mum kunji wai inadauke da juna biyu kuma yaya Farouq bazaibarni zubar da shiba inatinani watakil nima nakusa zuwa duniyar da kuke domin narayu atare daku inasanka Dad inasanki Mum tafada tana maixubar da kwalla tanufi toilet tayi wanka tare da doro alwala tafito tashirya takoma kangado tayi kwance tanaji ina kiran salla tatashi taci dabino sannan tayi salla bayan ta’idar takoma tayi kwanciyarta tanajin Fara nabuga mata kofa tare da fadamata Farouq yace tafito suyi buda baki amma tayi shiru kamar batajinta wannan yasa tajuya tayi tafiyarta takoma tafada masa cewar tabuga mata kofa amma batayi magana ba valantana kuma ta’iya budewa ok Fatima tace mebi kuma barci take yace komadai miye ruwanta bismillah muyi buda baki sunyi buda baki bayan sunkarasa yatashi yanufi masallaci Fatima tace kai Rumaisa kinasan kiwahalar da kanki duk kinsan Farouq bazaitaba yarda da bukatarkiba to bata rai name itama tatashi tatafi gurin salla

Farouq nadawowa daga masallaci kaitsaye part din Rumaisa yanufa baisameta afaloba wannan yasashi shiga uwar daki yasameta akwance ba kika takeba amma abin mamaki idanta suna zubar da kwalla yamata kallon tsab sannan ya’anbaci sunanta Rumaisa waimaiyasa kikesan wahalar da kankine hausawa fa nacewa fadin dayafi karfinka to kamaidashi wasa sai azauna lafiya maiyasa ke duk lokacin da kika sami juna biyu saikin bata ranki kinbata nawa bayan kinsan wannan badai-dai bane kinkumasan bazantaba yarda da bukatarkiba tinda kikaga banyarda kinzubar da cikin Amrat ba shida kikasamu alokacin su Adyan suna da watanni shida to kinsan bazanyarda kizubar da wannan cikinba dan haka shawara daya zan’iya baki kicere damuwa da tinaniko bacin rai atate dake domin hakan zaisa kirayu cikin farin ciki keda abinda yake atare dake yanzu abinda nakeso dake kitashi mutafi kiyi buda baki domin nasan bakici komaiba kuma garki yarda kice dani bazakiciba ko kinkoshi tashi mutafi bagardama tatashi sunnufi part din Fatima shida kansa yazuba mata abinci taci badantasoba tana gamawa tatashi tanufi part din Hajiya kofa suka isa sunsameta acan Farouq yakalleta yagirgiza kai yana maitin murmushi Rumaisa kenan

To masu karatu sai kuma gobe idan munsake haduwa daku da wannan nake cewa musha ruwa lafiya

By. Fauziya Usman Kogo
[1/2, 19:50] Maman Adyan: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀
MATAN GIDA
????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button