HAUSA NOVELMATAN GIDA Complete Hausa Novel

MATAN GIDA Complete Hausa Novel

Mum sai murmushi take yayinda take kallon dan nata tatashi da kanta tatafi tazubo mata abinci tabawa Sahla tace takai mata takarba tatafi tasami kofarta arufe tabuga tazo tabude Sahla tagaisheta tare da mikamata abincin da yake hannunta takarba waya aikoki Mum to hala anfada mata cewa banyi girkiba to wayasani idan zakici to idan kuma bazakiciba saikibani nakoma dashi Sahla garkiyimin tashin kunyafa wuce kibani guri tashige tare da rufo kofarta Sahla tajuya tatafi tadawo tafada masu takaimata ok Allah yaimaki albarka Amin Mum tazauna suncigaba da buda bakinsu bayan sunkarasa sunyi salla Dad baidawoba sai bayan sallar esha yadaukesu sunfita suntafi gidan Amir sunjima sosai agidan kafin zutabi bayan wani tsayin lokaci sukayimasu sallama suka tafi sundawo gida sundan taba fira kadan sannun dukkanninsu suka tafi suka kwanta Mum ce yakai Seedar dakinsa bayan yakarasa duk waji shirinsa nakwanciya yakwanta sannan tafito tanufi makwancinta

Toh zanu dakata anan saikuma gobe idan Allah yakaimu fatana anan Allah yasadamu da alkhairin dake cikin wannan wata Allah yasakamu acikin yantattun bayi Amin yarabbi musha ruwa lafiya

By. Fauziya Usman Kogo
[1/2, 19:51] Maman Adyan: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀
MATAN GIDA
????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

1⃣2⃣
Na

Fauziya Usman kogo

Bayan su Suhaila sunkwanta Saif yafito yanufi part din Safiya yasami kofar arufe tashiga buga mata kofa tanajinsa tayi banza dashi yakirata awaya amma bata dagaba saibayan wani lokaci sannan tazo bakin kofa tace wai waye cikin bacin rai yace Saif ne kibudemin kofa nashigo au ashe kasan anan kake shine kashantake acan bakaga damar dawowaba sai yanzu to bazan budeba kakomacan inda kafito kakwana acan taja tsaki tare da tafiyarta yana kiranta tare da buga kofa amma tayibanza dashi tayi tafitarta Safiya kibudemin kofa kinafajina aisai kayi iyayinka idan kagaji saika tafi domin bazantaba budema kofaba aikin bazan tashige abinta taja numfashin yana maifadin innalillahi wa’inna’ilaihinraji’un yajuya yakoma part din Suhaila yakirata awaya bayan tadaga yace tazo tabude masa kofa bagardama tazo tabude masa yashigo yayi zaune tare dayin tagumi Suhaila takallesa tafahimci yana cikin damuwa tare da bacin rai cikin tausasa murya take tambayarsa Saif lafiya maiyafaru dakaine Safiya ce tarufemin kofa to kodai tayi barcine kakirata awaya mana hum yaja numfashi ba barci takeba domin da bakinta tafadamin cewar bazata budemin kofa ba to amma maiyasa Safiya zata rufema kofa yasauke ajiyar zuciya garki damu da wannan tashi mutafi mukwanta dare yayi kinsan akwai tashi sahur amma Saif yadakatar da ita tahanyar cewa a’a Suhaila garkice dani a’a tashi mutafi yasauke ajiyar zuciya ok tatashi sunshiga yashiga toilet yayo wanka yafito yayishirinsa na kwanciya yazo yakwanta

Karfe 03:30am Suhaila tatashi tashiga kicin domin dora abincin sahur tana cikin aikinta Saif yashigo yasameta ya’isa inda take yarungumota ta baya yakawo bakinsa dai-dai kunnanta cikin kasa-kasa da murya yarada mata cewa kinkyauta domin banyi tinanin haka daga garekiba Suhaila maiyasa kikayimin haka kawai saboda Safiya saiki hanani kanki yajuyota sunfuskanci juna Suhaila maiyasa saboda Safiya ne ko to bari kiji koyanzu bazaki gujewa zargintaba dama fitinarta cikin wata irin murya take magana kayi hakuri mijina saboda bazaiyuwu nayi anfani da kwananta ba saboda nima bazanso wata rana tayi anfani danawa kwananba kuma hakan sam baidace ba yakamata muyimata adalci duk da cewa laifinta ne amma duk da haka ina naiman afuwarka mijina yayi murmushi vakomai Suhaila Allah yaimaki albarka Amin inagodiya to bara natayaki ko naga lokaci yana naima yashige to godiya nake haka kuwa akai yata yata sunkammala sunjera akan tebur yatafi yatashi Seedar ita kuma tanufi dakin Sahla domin tashinta Saif yatura kofa yashiga yasami Seedar yanata sharar barci ya’isa inada yake yazauna gefensa yana kallonsa yaja numfashi yana maicewa ya’Allah kanunamin lokacin da Seedar zandinga yiwa kainai hidima lokacin da zaifara tafiya da kafafunsa Amin yarabbi yasinbacesa aka idansa arufe yace Mum atinaninsa Mum dinsa ce tazo tashinsa Seedar tashi karmu makara jinmuryar Dad dinsa yasashi saurin buda idansa yace Dad kaine eh Seedar kana mamakine gaskiya da mamaki domin nasan yau apart din Aunty kake hakane amma sam garka damu da wannan taso mutafi kayi brush tare da alwala to Dad yarikashi yasashi akekensa yaturashi yakaishi yayi brush tare da alwala yafito suntafi gurin teburin abinci sunsami su Sahla agurin sunzauna kafin sufara sahur Seedar yace Dad Aunty fa tana apart dinta tare da abin sahur dinta ok to mufara domin lokaci natafiya ok sunfara sahur dinsu cikin natsuwa da kwanciyar hankali harsuka kammala Dad yanufi masallaci sukuma sinyi tasu agida bayan yadawo sungaisa yatashi yanufi part din Safiya Mum takai Seedar dakinsa saida taga yakwanta sannan tafito Sahla tanufi nata dakin haka Mum

Saif ya’isa part din Safiya yasami kofar abude kaitsaye dakinta yanufa saidai yayi rashin sa’a domin kuwa kofar dakinta arufe take yashiga buga mata kofa saidai tayi kamar batajisaba tabawa banza ajiyarsa yaja tsaki zaki fito kuma zaki hadu dani, dani kike zancan sainasa kinraina kanki yajuya yanufi dakinsa hum taja tsaki kanka akeji domin ni banda lokacinka ya’isa dakinsa yakwanta tare da takaicin Safiya aransa yasa hannunsa aljihu yadauko watarsa yakira layin Suhaila ringing buyu tadaga yace bakiyi barciba eh yanzu nake shirinyinsa ok Seedar fa yakwanta yayi barci kenan to bazance komaiba domin banida masaniya akan hakan ok to Sahla fa itama takwanta ok kuna cikin farin ciki ko maiyasa katambaya saboda nafahimci hakan daga gareki Uwar ‘ya’yana tayi dariya Saif kenan aifarin cikinmu yana tare danaka domin Kaine ginshikin farin cikinmu wannan yasa Mike alfahari dake akowane lokaci fatanmu akullum Allah yakara daukaka ka yabaka nasara yayima tsari da tsarewarsa yahaskaka al-amurranka da kasa agaba Amin Suhaila gaskiya ke mutunniyar kirki ce ina alfahari da kasancewarki matata Uwar ‘ya’yana Allah yabarmu atare Amin mijina to bara nabarki kiyi barci inagodiya kaima kakwanta kayi varci kaji to shikenan zanyi kokarin ganin nayi barci insha Allah to Allah yabaka iko Amin sunyi sallama ya’ajiye wayar yana murmushi tare da girgiza kai ya’anbaci sunanta cikin wani irin yanayi Suhaila ‘yar Aljanna yarufe idansa yana saffantata acikin idanuwansa nantake tanemi damuwarsa yamanta bayan wani dan lokaci barci yadaukesa

Karfe 10:30am yatashi daga barci yanatashi yafada toilet yayi wanka yafito yashirya tsaf cikin wani farin material yafito tana kwance kan kujera yayi tamkar baigantaba yanufi hanyar fita ganin yayi ko oho da ita yasata tayi saurin tashi tatafi tayi tsaye jikin kofa yadaka mata harara batare daya kira sunantaba yace kikwauce kibani hanya nafita ina zaka bansaniba aikena kikai dazaki tsareni da tambaya to bara kaji idan har baka fadamin inda zakaba to bazantaba barin kafita gidannanba yakirata cikin tsawa Safiya kibani hanya nafita bazanbayarba tarike kugu yana wani girgiza kai bata ankaraba taji saukar mari afuskarta tas tare dasa hannu yajanyeta gefe yafita yayi tafiyarsa tace kan uban nikamara wallahi zakasani domin zaka dawo kasameni agidannan sai nasa karena kanka taja tsaki tayi ciki

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button