MATAR UBA 13

???????????????????????????????? *MATAR UBA*
????????????????????????????????
_(A True Life Story_ )
*Short story*
“`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“`
Follow me on Wattpad @milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0
???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* ????????️
_(‘Kungiya d’aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* much Love.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
NOT EDITED
CHAPTER 13
Ta fice daga motar ita Kuma ta tada motar ta tafi, Baraka kuwa tana Shiga ban d’aki ta fad’a ruwa Mai zafin gaske ta Hana ta sa dittol a Ciki ta Shiga da nayar Zama a Ciki wani Kara ta sake Kan ta sake Kara ruwan sanyi a Kai, ta zauna zafi take ji sosai Amma tasan in ba hakan tayi ba baza ta daina Jin rad’ad’in da take ji ba.
????????????????????????????????
………. “Asiyah in tambaye ki Mana?”
“Ina sauraron ki”
” Ranar da Kika kwana a gidan mu bata tambaye ki a ina Kika Kauna ba? ”
Murmushin tayi kana Tace “ke ma kin San jazaman ne wannan, har Saida ta kusa dukana ma”
“Ya salam, Dan Allah Asiyah ki dawo gidan mu, ki rabu da mutanen Nan, so suke su kashe ki misali ranar da ta Koro ki yanzu da sun cutar dake Kuma fa, daba don taimakon Allah da taimakon mutumin Nan ba da yanzu Labari ya Sha ban ban”
” Laa kin tuna min ma mun sake had’u wa dashi”
Gyara Zama shamsiyya tayi Tace ” Haba Dan Allah da gaske kike?”
“Eh wallahi da gaske nake mun gaisa na mishi godiya, har ya fad’a min sunan sa”
“Mene ne sunan nashi?”
” Hashim”
” Wow hashimu”
” Shamsiyya nifa Hashim nace Miki”
” Toh Hajiya ai ainahin sunan Kenan”
” Toh iyani naji, Kinga na daukoy uniform na islamiya yau ba sai na koma gida ba”
” Yauwa yafi ai, sai biya ta gidan mu Kan Muje islmiyar ko? ”
” Tih Shikenan ba matsala.”
Nan suka cigaba da hirar su har Mai driver din shamsiyya yazo,Kai tsaye gidan su shamsiyya suka nufa, bayan sunci abinci sunyi sallar la’asar ya Kai su Islamiyya.
Baraka tunda ta samu tayi wanka taji saukin azabar da take ji, tana fita ta kwanta Bata d’au lokaci Mai tsawo ba baccin wahala yayi awon gaba da ita.
Yesmin tunda ta dawo daga school ta Shiga d’akin taga mummyn ta na bacci ta jaa Tsaki had’i da fad’in “Mata Bata da aikin yi sai bacci” tana Kai Nan ta Maida kofar ta rufe, kitchen ta nufa ta girki Abinda zata sa cikin ta, bayan ta gama ne ta ta Shiga ta watsa ruwa kana ta yi Sallah ta fito garden ta zauna a Kan kujera tana chat tana sipping five alive, horn da taji a gate ne yasa ta Maida kallon ta a gun, Mai gadi da sauri ya leka ta karamar gate don ganin wane ne.
A nitse yake tafiya cikin nitsuwa ya gaida shi “Ina wuni baba”
Ya amsa da “lafiya Lau ‘dan Nan”
“Baba Dan Allah tambaya nake”
“Toh Allah yasa na sani”
“Asiyah nake nema”
Baba Mai gadi mamaki ne ya Kama shi, a zuciyar sa yace “Asiyah ake nema a Karo na farko ban tab’a ganin an Zo neman ta ba Allah yasa dai lafiya”
A fili Kuma yace “Lafiya kake neman ta?”
” Dama…… ”
Muryar shamsiyya ne ya katse shi tana fad’in “Mai gadi Wai wane ne haka?”
Tana maganar ta karasa ta fito waje, tsuman tsaye tayi don ganin kyawun sa, Hashim ganin kallon yayi yawa ce “Sannun ki” ta amsa da “yauwa San sannu, how may I help you?”
“Dan Allah Asiyah nake nema”
Wani Abu Taji ya tokare ta a kirji da kyar ta samu ta sai saita kanta Tace “Asiyah da fatan dai Lafiya?”
“Eh lafiya Lau,jiya ne ta manta tray d’inta a bakin hanya shine na kawo Mata.”
Wani irin kallo ta Masa ta ce “Dama Kuna had’uwa ne?”
“Eh to, ban San yanda zance Miki ba dai, kawatace”
” Kawa?”
” Eh please don’t think otherwise, na lura Bata gida ko?”
” Eh Bata Nan”
” Islamiya taje ne?”
” Ni dai ban sani ba”
” Ba Yar uwar ki bace”
” Yar Uwa Tace”
” Kuma kice Baki San inda taje ba” tab’e baki yayi had’e a d’aga kafad’a Wanda hakan ya zame Masa jiki, sai ya d’aura da fad’in “Any ways ganan tray d’in da ta manta” Yana Mika Mata ya juya da niyar tafiya, da sauri Tace “To in ta dawo wa za’a ce Mata?”
Murmushi yayi Wanda ya nuna kyawun fuskar sa ya nuna dimple d’insa, d’an juyawa yayi yace “kice Mata Hashim Ahmad Shettima.”
Zaro Ido tayi tace “Hashim Ahmad Shettima?”
Bai tanka manta ba ya shige motar sa ya bar gun, ganin tsayuwar da take bazai amfane ta da komai ba, ta shige Ciki, Zama tayi a garden d’in Taji zaman ba dad’i ta jaa tsaki ta shige d’akin ta.
Kwanciya tayi akan gado tayi ruff da Ciki, a bayyane Tace “Hashim Ahmad Shettima, tabbas ina Jin Labarin guy d’in Amma ban tab’a tunanin kyawunsa ya Kai haka ba”
*WANE NE HASHIM AHMAD SHETTIMA?*
Hashim Ahmad Shettima d’ane ga Alhaji Ahmad Shettima, Ahmad Shettima shahararren d’an kasuwa ne Wanda yayi suna idan baizo a na farko ba, zai zo a na biyu, hakan yasa Bai fiye Zama ba yawanci a kasar waje yake business d’in sa, matar sa d’aya Hajiya Amina da ‘ya ‘ya biyu Hashim da Fadeelah,a sanadiyar neman na halal d’insa jirgin su ya fad’i ya Kone kurmus, iyalan sa sun Shiga tashin hankali sosai Amma babu yanda suka iya kullu nafsin za’ikatul maut.
Bayan rasuwar Alhaji Ahmad, Suraj Wanda ya kasance PA d’in Alhaji Ahmad ya Auri Fadeelah suna zaune cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali Babu abinda ta rasa har ta Haifa masa Yara biyu Adnan da islam, Hashim Kuma bayan rasuwar mahaifin nasu ya Koma kasar waje karatu ya karanci business, bayan ya gama ya dawo gida ya Fara kula da harkokin Mahaifin nasa.
Wannan shine cikekken tarihin Hashim.
“Hashim ‘din Soyayya yake da Asiyah? Kai it can’t be” tashi tayi tana kaiwa tana kawo wa ” Dole na San abin da zanyi akai, sabida na kamu da son sa bugu da Kari Yana da kud’i Dole na rarrashi Mummy ta nema min mafita.”
A Haka bacci ya d’auke, Hashim na tuki mamaki yake a zuciyar sa yace “Wannan wani irin gidane haka, tabbas yarinyar da na gani Yar uwartace don suna mugun Kama, Amma daga shigar ta kasan Yar hutu ce , Amma Asiyah kayan jikin ta duk a kod’e? Hatta uniform d’in da na Fara ganinta dashi a yage suke, Kai Dole na fad’ad’a bin cike akan ta, I need to help her.”
Zaro wayar sa yayi a aljihun rigar sa ya yi dialing number faisal, Faisal daga d’ayan ‘bangaren ya amsa da “Yane mutumina?”
“Kalau fa kana ina?”
“Ina gidan su zee”
” Mtswws Kai kullum sai ka jene, baka gajiya? ”
” Gajiya haba malam ai gaya maka idan kaga na daina zuwa to nayi wuff da ita ne”
” Hmm to Allah ya kyauta yanzu ya za’a yi? Ina son ganin ka, ko na zone?”
” A’a malam idan na gama zan Zo har gida na same ka Kar ka rage min hanzari”
“mtsww zakaji dashi ai, sai kazo”
Sai ya katse wayar, ya Koma gida Yana zaman jiran zuwan sa.
Maman Yesmin tunda ta Koma gida ihu da nishin Boko da Baraka ne ya tsaya Mata a rai duk hankalin ta ya tashi wani irin feelings take ji, da zaran ta tuna sai ta taune baki Nan take marar ta ya Fara ciwo, sai saki take ta jaa a fili tace “Kai wallahi auran soja ma matsala ne yanzu ina bukatar mijina ba hali”
Wayarta ta d’auko ta bud’e Facebook account da sunan Maman Yesmin, Nan da Nan akayi ta turo Mata friend request, Kun San maza da zaran sun ga sabon account anyi ta rushing ana turawa request, tun da Fara accepting request a kwance take a gun har akayi sallar Maghriba da Isha bata tashi a gun ba, dake Yesmin ta tafi hutu, ita kad’ai ce a gidan.