Uncategorized

MATAR UBA 15

Ad

_____

 💦💦💦💦💦💦💦💦             *MATAR UBA* 

💦💦💦💦💦💦💦💦

       _(A True Life Story_ )

            *Short story* 

 “`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“` 

Follow me on Wattpad @milhaat

Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* 📚🖊️ _(‘Kungiya d’aya tamkar da dubu)_ _____________________________

*MATAR UBA*  Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.

Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK*  much Love.

Ad

 *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

 “`NOT EDITED“`

 “`CHAPTER“` “`15“`

Murmushin takaici yayi yace ” Ko kad’an ban ga laifin Nana ba Kaine ka cutar da matar ka lalata Mata Rayuwa”

” Kamarya Kenan ban fahimce ka ba?”

Gyara Zama yayi Kan yace ” Ka saurareni da kunnen basira”

Yace “Kai nake sauraro.”

💦💦💦💦💦💦💦💦

……….”da farko dai zan sa so ka sawa zuciyar Kan ruwan sanyi, sannan ka tuna da alkawarin mu da Kai”

“ina sauraron ka”

“matar ka tana cin amanar ka kamar yanda kake zargi,nayi screenshot d’in chats d’in gashi ka gani da idon ka”

Ya Mika Masa wayan, Abban Yesmin ya karb’i wayan hannun sa na rawa, kirjinsa na dukan uku uku, ya fara karanta chat d’in tun Kan yayi nisa idon sa ya cika fal da hawayen bakin Ciki, kasa karanta sauran chat d’in yayi ya Mika Masa wayarsa.

Murmushin gefen baki Abokin nasa yayi yace “Kaji ba dad’i ko? To Kar ka ji haushin kowa sai Kan ka sabida kaine ummul aba’isin abubuwan da take yi”

Rai a ‘bace yace “kamarya zaka ce laifina ne? Bayan kaga Abubuwan da take yi”

“Kaine mana, yanzun Nan kace min ka Kai 6 months baka je gida ba, how do you expect her to do Kai ka na Nan kana bin matan banza hankalin ka a kwance ita Kuma ka kyaleta a chan ko oho, kaga Ni I know nayi nisa da matata, Amma hakan baya hanani zuwa ko Kuma ita tazo, sabida ba iya abinci bane hakkin ta akanka kamar yanda kake da hakki a kanta haka itama take da hakki a Kan ka”

Shiru yayi kana yace “Amma kasan idan na Miji yayi iskanci ado ne a gunsa ko?”

“Lallai ma bawan Allan Nan a wani aya ko hadisi akace haka?”

Shiru yayi kawai Yana kallon sa, alamun bayi da amsa, kad’a Kai yayi yace ” You see baka da hujja iskanci wani riba ka samu a Ciki? Banda tarin zunubai? Kamar yanda kake Zina da Yar wasu Kai ka za’ayi wa naka, haka da matar ka sabida itama ‘yace so ni Banga laifinta ba dama ai ramuwar gayya tafi ta gayya”

“Hakika nayi babban kuskure da na Maida Zina abin yi, Ni gani nake abinda nake yi waye wa ce, Amma yanzu ka tada Ni daga baccin da nake, yanzu tell me, me zanyi don Wallahi kaina ya kulle”

“Abu Mai sauki kawai ka dawo da ita Nan ko Kuma ka nemi posting a Maida ka gida, but a shawarace ka dawo da ita Nan zaifi”

” Toh Shikenan nagode sosai Abokina, na godewa Allah da ya bani Kai a matsayin Abokina”

Murmushi kawaii yayi, ya cigaba da Danna wayarsa.

“Asiyah!! Asiyah!!! Safiya ce ke Kiran sunan ta tana bubbuga Mata kofa, a hankali ta bud’e kofar idon ta a kumbure da alama Tasha kuka ne Kan tayi bacci, tsaki taja tace “Malalaciya kawaii, tun dazu ake kiranki kina Jin mutane” wurga Mata Abu tayi Tace “Gashi inji mummy ki sayo Mata kosai” tana kai Nan ta tafi, Asiya jiki ba Karfi ta durkusa ta d’auki kud’in taga naira biyar ce, tab’e Baki tayi ta shige toilet ta wanko fuskar ta ta fice daga gidan, bayan ta sayo kosan a hanyar ta ta dawo wa suka had’u da Hashim Yana exercise, Yana hango ta ya Fara Murmushi bayan sun gaisa ta Sanar dashi zata wuce gida, baice komai ba ya Bata hanya ta wuce, kallonta ya tsaya yi har sai da ya ga ya daina ganinta kana ya cigaba da gudun sa, Asiyah na komawa gida ta tarar da Mummy da safiya a tsakar gida, durkusawa tayi har kasa Tace “Mummy ina kwana?”

“A gidan ubanki na kwana” a tsawace 

Asiyah ko kad’an hankalin ta bai tashi ba don Inda sabo ta saba, “har zakice min ina kwana? Wato Asiya Rayuwar da Kika zab’awa Kanki Kennan ko, iskanci Zaki Fara yimin a gidana? Wallahi tir da halin Baki Isa tun daga yanzu kina fita kina kwana waje ba”

Asiya dafe kirjin ta tayi a tsorace ta mike ta tsaya Tace “Kwana a waje Kuma mummy wallahi Ni ban kwana a waje ba yanzun Nan na fita Kuma safiya ce tace kin aiken na sayo kosai gama ledan” tana nuna mata ledar dake hannun ta.

Murmushi gefen baki tayi Tace “Saifiya a Ina kika ganta?”

“Mummy yanzun Nan na fita don na Sha iska na hango su a wani lungu Yana rungume da ita sai kiss yake Mata”

” Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un, haba safiya kiji tsoron Allah sharri Zaki min?”

Wata mahaukaciyar mari ta mata Tace “Don uwar ki safiya ce zata Miki? Safiya je ki d’auko min ruwan nan”

Wani shu’umin dariya tayi ta shige Ciki Bata d’au lokaci ba ta fito da wata karamar roba a hannun ta Baraka duka ta Fara kaiwa Asiyah ta ko ina, sai da ta Mata dukan tsiya Wanda ko Motsi ba ta iya yi da kyau, cikin sauri ta karb’i roban da ke hannun safiya ta watsa Mata a Ido, ihu Asiya take yi tana kuka a kawo Mata agaji, tana ihun “Idona Idona Mummy Idona Dan Allah ku taimake Ni” a daddafe ta rike kafar Baraka ba tausayi ta hankad’e ta dafa, ta riko hannun Safiya suka barta a gun, baba mao gadi da yanzu shigowar sa ya karasa inda take da gudu Yana Kiran sunan Asiya “Asiya me ya same ki?” A tsorace yake maganar don ganin yanda take ihu tana tsalle,tausayin ta ya Kama shi sosai

Ad

_____

1 2Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button