Uncategorized

MATAR UBA 16

 ????????????????????????????????             *MATAR UBA* 

????????????????????????????????

       _(A True Life Story_ )

            *Short story* 

 “`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“` 

Follow me on Wattpad @milhaat

Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* ????????️

 _(‘Kungiya d’aya tamkar da dubu)_ _____________________________

*MATAR UBA*  Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.

Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK*  much Love.

 *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

“`CHAPTER 16

NOT EDITED“`

????????????????????????????????

Likatan ce ta fito ta nufi Inda baba Mai gadi yake Tace “Kaine ka kawo yarinyar Nan ko?”

Cikin Rawar murya ya ” eh eh nine”

” Okay Amma ya akayi Naga ruwan barkono a idon nata? ”

Zaro Ido yayi yace ruwan barkono?”

“Yes ruwan barkono”

????????????????????????????????

“Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un, Amma ya akayi Asiya tasa ruwan barkono a idonta?” Yana wannan maganarne a zuciyar sa, maganar da likata tayine ya dawo dashi daga tunanin da ya Lula cikin Rawar murya yace “Na’am likita me kikace?”

A karo na biyu ta Kuma maimaita maganar da tayi ” Ana bukayar million biyar Wanda za a wanke Mata Ido cikin gaggawa daso samune ka ayi aikin a yau don idan ta Kwana a haka idanunta zasu it’s lalacewa gaba ki d’aya ma’ana baza ta sake gani ba”

Baba Mai gadi Banda kalmar Innalillahi wa ilaihirraji’un babu abinda yake furtawa a nitse ta ce Masa “Baba lafiya kuwa”

Cikin rawa murya yace “Lafiya lafiya kalau”

“Okay to ayi maza a Nemo kud’in Nan” 

“To likita” tana kai Nan ta yi tafiyar ta.

Baba maigadi kansa ne ya kulle ya rasa abinda zaiyi ya tabbata Baraka baza ta had’a kud’in ba sannan Yana da tabbacin itace ta watsa Mata ruwa, d’akin da Asiya take ya Shiga, Banda shesshekar kuka babu abinda yake ji a d’akin cikin muryar tausayawa yace “Sannu Asiyah, Amma ya akayi Kika sa ruwan barkono a idon ki? ”

” Baba Mummy Ce ta sa ruwan zafi sannan suka sa barkono aciki ta bud’e idanuna ta watsa min” ta karasa maganar cikin kuka.

” Asssha me Baraka take nema a duniyar nan, Ni ban tab’a ganin Mara imani irin ta ba, me laifin yarinyar Nan don tazo a matsayin Yar mijin ki? Yanzu gashi tana kokarin lalata Miki Ido Asiyah, million biyar ake bukata Don wanke Miki Ido, Asiya Ina zan samo makudan kud’in nan?” Ya karasa maganar Yana kuka Mai cin Rai, murmushin takaici tayi Tace “Baba ka daina kuka, me zai Hana kaje gun dangin mahaifiyata, Ina ga su kad’ai ne zasu taimaka min?”

‘dago kansa yayi a hankali ya kalle ta kana yace “dama kina da wasu dangi a garin nan? Amma Kika zauna a gun maras imanin Nan tana gallaza Miki azaba? ”

” Baba Suma sun gujeni sanadiyar Abubuwan da mummy ta ke musu tun suna hakuri har suka daina zuwa inda nake”

Huci yayi kana yace “Allah shi kyauta ya Shiga tsakanin mugu da na gari”

Ta amsa da ” Ameen ba”

” A wace unguwa suke? sai naje na same su, don Tace min Kar mu d’auki lokaci cikin gaggawa ake bukatar ayi aikin”

“Bayan rasuwar mahaifiyata Aunty Rukayyace kad’ai da kakata suke zuwa inda muke, bayan mutuwar mahaifiyar mu da shekara d’aya kakar mu ta rasu, Aunty Rukayyace kad’ai ta rage min sai Kuma Uncle Suleiman Amma shi ba a kasar Nan yake ba”

Tayi Masa kwatancen unguwar da Aunty Rukayya take sannan ta Masa kwatancen gida, tashi yayi ya fita.

Yana Isa unguwar ya Shiga neman gida ya d’auki tsawon awanni biyu bai gane gidan ba duk da ya sha tambayar mutane daban daban daga bisani ya samu gidan, kwankwasa gate d’in yayi aka bud’e Masa bayan sun gaisa sai ta shaida Masa Rukayya yake nema ma’ana matar gidan, mutumin da ya bud’e gate d’in yace “Ayya ai sunfi watanni  biyar Basu kasar Mai gidan ya samu chanjin wurin aiki sun koma chan da Zama”

Durkusawa baba Mai gadi yayi ya d’aura hannu a Kai yace “Allah Sarki Asiyah ke Kuma Taki kaddarar Kenan ya Allah gamu gare ka, Kai ka San yanda zakayi da wannan baiwa taka”

Da sauri Mai gadin ya fito Yana Kare wa baba Mai gadi kallo yace “Kamar sunan Asiya naji ka ambata ko?”

“Eh hakane” Yana maganar yana kokarin share hawayen dake idon sa, Murmushi yayi yace ” Ai kuwa an bani sako na bata, Hajiya Tace tasan Dole watan watarana zata nema ta shiyasa ta bani wata takarda ina ka kamar wasika ce, bari na d’auko maka?”

Sai ya shige Bai d’au lokaci ba ya fito hannun sa rike yake da wata farar takarda ya mikawa baba Mai gadi had’e da fad’in “Dan Allah ka bata don Hajiya ta tabbatar min da cewar Yana da muhimmanci”

” Kar ka damu insha Allah yanzun Nan zan Kai Mata” sukayi ban Kwana ya Kama hanyar shi ta komawa asibiti Bai ji d’adin Jin Rukayya Bata gari ba Amma ya ji hankalin sa ya kwanta na ganin bata manta da Asiyah ba.

Tafiya yake yazo zai tsalle titi Bai lura ba wata mota ta sako Kai da gudu, ta kad’e shi Nan take yafi sumamme.

Nan da Nan mutane sukayi chaaa akansa, mutumin da ya buge shi ya fito a firgice jikin sa sanye yake da uniform na soldier da alama soldier ne, ya nemi taimakon mutanen dake gun a ka Sa Shi a mota Kai tsaye asibiti suka nufa, emergency room aka Kai shi sabida ya buge kansa ya zub da jini sosai.

Safa da marwa yake har likita ya fito yace “Kaine ka kawo mutumin da yake zub da jini?”

Ya amsa da “Eh nine”

Yace ” Okay ya fita a danger mun samu mun tsayar da jinin yanzu Haka Yana bacci, Amma zamu rike shi anan sabida ya d’an bugu akan sa”

Iska Mai zafi ya hura yace ” Kana nufin zai samu sauki ki babu abinda ya same shi?”

“Eh insha Allah”

“Ga wannan a aljihun sa aka samu, kamar wasika ce kuma da sunan wata akai”

Karb’a yayi ya duba ya ga an sa sunan ” ASIYAH” da manyan harufa,

“Okay na gode sosai”

Wayar sa ce ta Fara ringing ya amsa da

 “Hello abokina ya?”

“Kalau ka isa gidan ne?”

“A’a a hanya ta ta tafiya na buge wani yanzu Haka ina asibiti”

“Subhannallahi kaga shiyasa nace maka ka kwnatar da hankali Kar ka Bari sabida Nana ka cutar da kanka”

” Ya zanyi ne Ameenu? Ya zanyi? Yanzu fisabillilhi Nana abinda zata min Kennan, yanzu ko don yarmu Yesmin baza ta daina abinda take ba? Taya za a yi ina ji ina gani matata ta Zama public toilet kace min na kwantar da hankali na?”

” I know,I know it’s not easy,but ya kamata kabi komai a Sannu ka fahimce Ni? Yanzu ina mara lafiyan yake hope dai da sauki?”

” Eh da sauki, bari na Shiga na duba shi”

” Okay Shikenan duk yanda ake Ciki let me know please”

“Alright ba matsala” a tare suka katse wayar.

Bayan ya Shiga ya duba shi ya fito ya nufi hanyar gida, a hankali yake driving don gaba ki d’aya ji yake kamar baida lafiya,Yana Isa layin gidan say ya hangi motar Maman Yesmin ta fito da alama fita zatayi, packing yayi don ganin inda zata je ganin ta yi gaba,yasa ya Fara bin bayanta ga mamakin sa har fita sukayi a cikin gari Bata tsaya ba Saida taje wani jeji kana ta fito ta shiga,tana tafiya tana waige waige,Shima parking yayi Dan nesa sa ita, ya dad’e a gun Yana jiran fitowar ta Amma shiru kake ji, bin bayanta yayi ga mamakin sa wata Yar karamar bukka ya gani,tun daga nesa yake jiyo muryarta tana wasu irin surutai Wanda yake fatan ba abinda yake tunani bane jiki a Sanyaye ya Shiga cikin bukkar, a tsawace yace “Nana” ba ita ba kad’ai ba harda boka ya tsorata don sunyi nisa cikin shashancin su Basu sanda mutum a gun ba,a razane boka ya tashi Yana kokarin duba inda wandon sa yake, ita Kuma ta neman inda kayan ta suke, cikin muryar kuka yake magana “Nana Ni? Ni zakiyi wa haka yau ke na Kaka red handed da wuni turmi da tarb’arya kin cuceni Nana, Allah ya Isa tsakani na dake” Banda kuka babu abinda da take yi, ganin bokan na kokarin guduwa ya cukumo shi ya fara na d’a Masa na jaki ran Soja ya b’aci sanda ya had’a Masa jini da majina ya kyale a tsawace yace “Ke kuka wuce mu tafi” jiki na rawa ta fice daga bukkar da gudu ta Shiga motar ta ta nufi gida Shima ya bi bayanta.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button