Uncategorized

MATAR UBA 27

Ad

_____

 💦💦💦💦💦💦💦💦     *MATAR UBA*

💦💦💦💦💦💦💦💦

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

                 *(MILHAAT)*

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

Ad

Not Edited

CHAPTER 27

Safiyya na Jin karar motar ta gane ta fita ne tsaki ta jaaa, ta fito fridge ta nufa ta d’auki wannan yoghurt din da Baraka tasa Abu a ciki, tana Bud’ewa ta kafa Kai ta shanye tass ko bismillah batayi ba,wani irin bacci ne taji ya kamata,har ta Fara haurawa Kan stairs taji baza ta iya ba ta dawo kan sofa ta kwanta.

💦💦💦💦💦💦💦💦

…….Kiran Hashim sukayi bayan sun gama Shirin,Bai d’auki lokaci Mai tsawo ba ya karaso  Kiran Diyya yayi a waya, tsuman tsaye yayi ya sanya kallon su ganin yanda suka had’u suka had’e shikam yayi dace sai yanzu ya Kare musu kyau duk kyawun Badiyya, Asiyah ta ninkata ninkin banin ki. 

Iska Diyya ta d’an hura Masa a idon sa yayi saurin Maida kallon sa gareta shi Sam Bai ma San sun karaso inda yake ba, Murmushi yayi Yace “Hello!!”

Murmushin ita ta Maida Masa Tace “Hy”

” Ya Hashim irin wannan kallo haka?”

Asiyah ce ke Masa wannan tambayar.

“Hmm ai ku din me duk Kun tafi da imani na,kunyi matukar kyau sai dai fa gaskiya baza ku fita a Haka ba”

A tare sukace “Meyasa”

Dariya yayi Yace “Kar ku cinye Ni,ni was nake mu tafi ko?” 

Ya Bud’e mota zai shiga sai kuma ya tsaya ganin duk zasu shiga baya, kallon su yake yi har Asiyah ta kafar ta d’aya a cikin motar yace “Kuna nufin duk ki biyun a baya zaku zauna Kenan?”

Diyya Tace “Eh Mana”

“iyee sannun ku gani driver d’inku ko?”

“Eh man Kai kace kaji ka Kuma ka gani,dama Kuma ance nan Miji bawan matane”

‘daga gira yayi yace “Harda Ni?”

” Eh man harda Kai”

“Hahaha Aunty,ya Hashim ba bawan matane ba”

“kyaji ki Asiya to mene shi in ba bawan Mata ba?”

“Masoyin Mata dai”

Kama Baki yayi yace “La’ilaaaa”

Diyya Banda dariya babu abinda takeyi, Asiya Kuma said yanzu ta fahimci maganar da tayi don Bata ma San sanda ta furta ba.

Yace “Queen ai gara ki ce min bawan Mata da Masoyin matan nan”

Kunyane ya sa ta shigewa motar ta leko ta window tace “Aunty ki shiga gaba man mu tafi”

Zagayowa tayi ta shige gaba duk da hakan bata daina dariya ba, girgiza Kai kawai yayi Shima ya shige motar ya tsaya kallon ta “To ke Wai dariyar bata ishe ki haka ba?”

“Dasaura”

Hannayen sa ya hard’e wuri guda yace “To idan kin gama sai mu tafi”

“Am sorry am sorry” sai ta Kuma fashewa da dariya.

Waigowa ya kalli Asiyah banda Murmushi babu abinda ta ke yi yace “Kinga abinda Kika jawo min ko?”

Sunkuyar da kanta ta shiga dariya.

” Au kema dariyar kike? Shikenan sun  Maida Ni mahaukaci” ganin dariyar tasu Taki karewa ya sa wa mota key suka Bari gidan.

Gidan Abban Yesmin suka nufa,zuwar su yayi dai dai fitowar sa ,Yana ganin su ya yi Murmushi hannu ya mikawa Hashim suka gaisa, yace “Kaga mutanen India yaushe a gari?”

“Jiya just Nan”

“Masha Allah da fatan anyi nasara ko?”

“eh gashi Nan kuwa kana ganinta” ya nuna Masa Asiyah dake gefe.

“Aa’aa Masha y gaskiya naji dad’i,yanzu Asiya kina gani na?”

Yar karamar dariya tayi Tace “Eh”

Yatsun sa guda uku ya d’aga yace nawa ne Nan?”

Cikin dariya Tace “Biyar”

Zaro yayi ya kalli hannun sa yace “Asiya biyar Kuma ko dai idon akuya suka sa Mike ne? Amma Kuma ganan idanun ki yanda suke” Yana Mai Kara kallon idanuwanta harda gyara tsayuwar sa. 

Maida kallon sa yayi ga Hashim dake ta dariya yace “Hashim gaskiya aikin Nan baiyi ba ace tana ganin uku Tace min biyar,ya kamata mu shirya zuwa wata kasar wannan karon Chaina Zamuje”

Duk su ukun suke dariya shi kuwa magana yake dagaske ya Kuma cewa “look ba maganar wasa nake ba Dole mu kaiki chan”

Hashim yace “Queen ya kamata ki fad’a masa gaskiya ki cire shi daga rud’un da ya shiga ko Kuma mu kaiki Chaina d’in Kinga daga Nan Sai cire Miki kwala kwalan idanun ki su sa Miki irin nasu”

“A a me yayi zafi am sorry Daddy zolayar ka nake Ina gani yanzu”

“umm ummm Asiyah ban yarda ba ina tantama”

“okay tunda baka yarda ba, shaddace a jikin ka lemon green, wanchan motar baka ce,sannan motar da muka Zo da ita Blue ce,Aunty Diyya kuma bakar doguwar Riga Ce a jikin ta, Ya Hashim Kuma bakar Riga da farin jeans da facing cap Fari”

“Ko da naji yanzu Kam na yarda”

Bud’o kofar da akayi ne yasa dukkanin su kallon gun, Nana tana ganin su Tace “Kace Baki mukayi in kitchen sai Jin surutai nake,shine ka bar su a waje, bismillah ki shigo mana”

Diyya dake tun d’azu ta gaji da tsayuwa ta Zama ‘yar kallo a cikin su, tayi saurin bin bayan ta, tana mamakin Hashim sau d’aya fa suka had’u da shi Amma zaka d’auka sun San juna na tsawon shekaru.

Zama sukayi suka sake gaisawa Nana da khamal sunyi matukar farin cikin ganin Asiyah ta samu sauki dama shine first mission ‘dinsu, gyara Zama khamal yayi had’e da gyaran murya.

“Hakika bazan iya misalta Muku irin tsananin farin cikin da nake cikiba, tunda naga Asiya ta samu lafiya, Asiyah tamkar ‘ya take a guna Mahaifin ta babban Abokina be,sanadiyar aikin tsaro da na shiga ne yasa mukayi nesa da juna babu yanda baiyi dani ba Akan na cigaba da Business ‘dina Amma naki,sabida ina matukar son aikin ya hakura ya goya min baya,sabida Zanyi duk abinda naga zan iya yi don inga an d’aure Baraka har sai inda karfina ya Kare”

Ad

_____

1 2 3 4Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button