MATAR UBA 27

Hashim cike da mamaki yace “Kina nufin Mahaifiya ta kawar kice?”
Cikin rashin fahimta tace “Mahaifiyar ka Kuma?”
“Eh suna na Hashim Ahmad shettima”
“Ah ikon Allah,lallai Hashim ka girma rabona da Kai tun kan ka tafi kasar waje karatu”
“Hakane nayi mamakin yanda akayi ban gane ki ba,duk da ina Miki kallon sani”
Yar karamar dariya tayi irin tasu ta manya tace “Ai dole an kwana biyu ai”
“Hakane ina Yesmin?”
Kan ta bashi amsa suka jiyo muryar ta Tace “Gani Nan,mummy Baki mukayi?”
Zama tayi akan kujera Mai d’aukan mutum d’aya.
“Eh yayan ki ne Hashim”
“Oh Allah sarki kullum ina jin labarin ka Amma ban Sanka ba”
Murmushi yayi Yace “Gashi yau ki. Ganni”
“Hakane shekaran jiya ma a gidan Mummy Amina na wuni,har…..”
“Yesmin Dan Allah surutun ya Isa haka”
Ya Maida kallon ga Nana yace “Amma Nana kin tafka babban kuskure,kiyi ta istigfari”
“Ina Kai Abban Yesmin,ba dare ba Rana” ta karasa maganar tana share hawayen da suka zubo mata.
“Yanzu kuka ba naki bane idan na zakiyi kiyi shi akan Sallaya” ya Maida kallon sa ga Hashim “Masha Allah abun duk na gida ne,to yanzu mafita d’aya ya rage Mana mu kama Baraka red handed shine kad’ai inda zamu samu a kamata”
Asiyah Tace “But she is so clever Taya za a yi mu samu evidence?”
Murmushin gefen baki Nana tayi tace “simple Amma fa akwai risk,dole zan koma na bata hakuri mu cigaba da kawance,ke Kuma Asiyah zaki koma gidan ku”
Khamal,Diyya, Hashim,da Asiyah a tare suka ce ” whaaaat?” har Saida Yesmin ta d’an tsorata sabida duk ta Maida hankalin ta Akan wayarta tana chatting.
Hashim murya na rawa yace “No baziyu ba gaskiya Asiyah baza ta koma gidan Nan ba,kin manta yanda take Mal treating d’in ta ne? Itace fa sanadiyar makancewar ta Allah ya kawo Mana da sauki da ita da gani har abada, gaskiya a canza wani shawara”
Khamal yace “Babu wani mafita Hashim, don tun Kan ku dawo muke ta shiri da ita this is the only way,in dai muna so mu kamata da laifin shine kad’ai abunda zamuyi,zamuyi amfani da Asiyah ne wurin tona Mata asiri human rights zasu shiga zancen, sannan Nana zata koma Mata ne sabida tasa ta fad’in ita ta kashe su da bakin ta Ni kaina bana so Nana ta rab’e ta sabida annoba ce, zamuyi hakan ne sabida mu kwato wa asiyah hakkin ta”
Hashim Kam jinsu kawaii yake yi don shi Sam hankalin sa bai kwanta hakan ba.
Tashi Diyya tayi daga inda take zaune ce to matso kusa da shi, cikin murya Mai sanyi ta ambaci sunan sa “King”
‘dago kansa yayi ya kalle ta “please ka kwantar da hankalin ka insha Allah babu abinda zai sameta”
Girgiza Kai yayi yace “Take a look at her” yana nuna mata inda Asiyah ke zaune ya ‘daura da fad’in “hankalin ta a tashe yake Kuma kice ta koma,gaskiya bazaiyu ba, Asiya Nan Jin su Murmushi tayi ta taso itama ta zauna a gefen sa sai suka sa shi a tsakiya Tace “Ya Hashim Please Kar ka damu komai zai yi dai dai kaji”
“Look bazan ba fahimce ku ba kawai Ni baza kije ba”
“please…..”
Riko hannun ta yayi yace ” I don’t wanna loose you queen, Baki San halin da na shiga ba a rashin ki har na kusa zaucewa,idan wani abu ya same ki bazan iya jurewa ba ya kamata ki fahimce Ni”
“Wanann wani irinn Soyayya Hashim yake yi wa asiya? Nasan baya min irin wannan Soyayyar,ko dai tausayin ta yake Jine? Amma da me ta fini?” Diyya ke jero wa kanta wa’annan tambayoyin Wanda duk ba mai Bata amsoshin su.
Maganar su ce ta dawo da ita daga tunanin da ta shiga “Ya Hashim I will be careful I promise you,and insha Allah babu abinda zai sameni tunda a baya ban mutu ba yanzun ma hakane”
“Amma ai taso kashe ki,ta kashe Dad da mom sannan ta kashe Anisah ke kad’ai ce kika rage tana samun dama zata hallakaki tunda ta iya sa Miki barkono a Ido ba gargada zata iya sa Miki poison a abinci,so ni ban yarda ba”
Yana Kai Nan ya tashi ya fita,bin bayanshi tayi tana Kiran sunan shi Amma Bai kulata ba,cikin mitary say ya shiga har yasa key tayi saurin kwace wa.
“Haba king” kallon ta yayi don baiyi tunanin zata kirashi da wannan sunan ba ta d’aura da fad’in “Nasan baka so a cutar dani ina alfahari da hakan but me kake ganin zamuyi in ba wannan ba ko kana da wani shawarane?”
Girgiza Mata Kai yayi alamun a’a.
“Good to kayi hakuri muyi hakan kaji yanzu kan tashi mu koma ciki kaji king?”
Murmushi yayi Yace “Shikenan na amince Amma da sharad’i”
“Uhmnn ina jin ka mene ne sharad’in?”
Fuskar sa ya nuna Yana Murmushi har saida dimple ‘din fuskar sa ya nuna zaro Ido tayi Tace “me hakan yake nufi?”
“Me kuwa peg Zaki bani”
Zaro Ido tayi Tace “Peg Dan Allah ka rufa min asiri”
“Asirin ki a rufe maza ina jira” ya rufe idanun sa, sai Karan Bud’e kofar yaji yayi saurin riko Hannunta “Ina Kuma zakije?”
“Ka manta Ana jiran mune?”
“Ban manta ba ki bani peg ‘dina kawaii”
“Na maka alkwarin ka bini bashi”
“bashi zuwa yaushe Kenan?”
Cike da kunya Tace “Our first night.”
Har cikin ransa ya ji dad’in maganar sai Kuma ya ‘bata fuska yace “Ni ban yarda ba wayo Zaki min”
“Allah da gaske nake”
“Tunda kince Allah na amince”
“To tashi Muje”
Sakin hannun ta yayi suka fita,suna zuwa parlor shirun kamar ba kowa,kowa da abinda yake ayyanawa a ransa.
Hakuri ya Basu sannan yace ya amince,anan ne ya ke fad’a musu abinda ke tsakinin su da Safiyya, Asiyah Tace “Allah sarki Kanwata bata chanchanci hakan ba, hakan zai karya mata zuciya”
Nana tayi saurin fad’in “Babu abinda zai sameta, sabida ba a cikin hayyacin ta take ba, ita ma asiri aka Mata,sannan Safiyya bata son Hashim ko kad’an tun Lokacin da ta San labarin Hashim babu yanda bata yi ba Akan ta shige Masa ba Amma taki,Amma Ni a Lokacin ban San Kai bane don Taki fad’a min a fad’in ta sai komai ya kankama zata Sanar dani”
Diyya cike da mamaki Tace “Asiri Kuma Baraka ce ta mata,Inna lillahi wa Inna ilaihirraji’un wannan wace irin uwace haka?”
“Baraka Kennan tafi sonka kanta fiye da kowa in dai zata samu biyan bukata bata da matsala”
“Toh Allah ya kyauta”
Duk suka amasa da ” ameen”
Nana Tace “Tunda kin amince da plan d’in ya kamata ki koma gidan cikin gaggawa sannan akwai wani tulu a karkashin gadon ki, sannan akwai a d’akin Safiyya idan, sannan akwai a d’akin Baraka,sanin Kanki ne baraka bata Bari kowa ga shiga mata d’aki, daga Ni sai Safiyya, idan kika samu damar fasa na d’akin Safiyya,abun zai Zo Mana da sauki, Don malam yace ko da ganin tulun Safiyya tayi sihirin zai lalace, da fatan kin fahimta?”
“eh na fahimta”
Khalmal yace “Yanzu yaushe Zaki koma?”
“Gobe nake son komawa”
Nana tace “Ki bari sai jibi,don yau d’in Nan zanje gidan ta, in ya kwana biyu sai ki koma”
Ta amsa da “To Shikenan”
Khamal yace “Yauwa na manta ban Sanar daku ba,akwai camera da zan bawa Nana duk sanda zata je gidan sai ta makala zai Mana video na komai,Ni Kuma Ina nan ina recording a laptop d’ina.”
A haka suka Gama shirya yanda zasu Kama Baraka.
Baraka ba ta dawo ba har Saida ta gama sheke ayan ta da wani Alhaji kana ta dawo gida, a Lokacin karfe Bakwai da rabi haryanzu Safiyya bata sa inda take ba baccinnta take , Murmushi tayi Tace “Yar iska Ni zaki rainawa wayo tukanna ma” hannu tasa akan Safiyya ta Fara shawa a hankali tana lashe baki kamar wata sabuwar mayya hannu tasa a sugar ta tana wasa da dukiyar fulanin ta.
(Ni kaina da nake d’auko muku rahota abun yayi matukar bani mamaki,me hakan yake nufi,meyasa take shafata haka? Koma dai menene zakuji muje zuwa)