MATAR UBA 27

Door bell taji wani irin tsaki tayi cikin zafin nama ta nufi kofar tana Bud’e wa ta Fara masifa “Kai Bala bance maka Kar ka kuskura ka dame Ni ba me ya…..” Ganin wacce take tsaye ta tsaya baki a Bud’e Tace “Kece?”
Murmushi Nana tayi Tace Eh nice”
Hashim tunda suka bar gidan Abban Yesmin, ya zarce dasu inda ake sayar da wayo yi, yace su zab’i son ransu ganin sun tsaya Rawar Ido ya d’auka musu iPhone 13, sannnan ya mikawa Asiyah karmar waya Shima sabuwa a kwali,ta kalli Tace “Wannan fa?”
“Dole ki rike karamar waya kin San bazaiyu ki rike babbar waya a Wannan gidan naku ba” ya karasa maganar rai a d’an ‘bace dariya kawai tayi suka Masa godiya.
Diyya Kam tun da suka baro gidan ta kasa sakin jikinta, hashin ya kura da ita ya gano kishine ke cinta “To meyasa baza tayi koyi da Asiyah ba ita Sam bata damu ba Kuma yasan Asiyah na son shi” a ransa yake ayyana hakan ,cikin wannan tunanin suka Isa gidan su Diyya.
????????????????????????????????
Please vote and Comment
Milhart ce
Yar terawa
[ad_2]